ZAURAN DALIBAN ILIMI @zaurandalibanilimi Channel on Telegram

ZAURAN DALIBAN ILIMI

@zaurandalibanilimi


Ibnul Mubarak(RA) ya ce: Babu wata daraja mafi falala da ɗaukaka bayan Annabta kamar yaɗa ilimi mai amfani.
Ku zuba hannayen jarinku ta hanyar yaɗa ilimin Addini barakallahu feekum💌


Domin magana da mu👇
@AtharqablarraheelBot

ZAURAN DALIBAN ILIMI (Hausa)

Zauran Daliban Ilmi, wanda aka fi so a Hausa, shine Channel mai yawa da yawa da ilimin Addini. A kan wannan Channel, za mu samu wasu turo da suka fito daga Annabta da suke da amfani ga duk wanda ke so ya zama Daliban Ilmi. Bayan Annabta, Ibnul Mubarak (RA) ya ce: 'Babu wata daraja mafi falala da ɗaukaka bayan Annabta kamar yaɗa ilimi mai amfani.' Kada ku sami damar sauraran turo da Mu ta hanyar yaɗa ilimin Addini ta domin zaku iya samun kwarewar ilmi da kuma siyasa a yanayin zaman mu. Ku ziyarci wannan Channel don samun karantarwa da kuma karatu masu nasara a kan ilimin Addini. Don magana da mu, tuntube Channel dinmu a @zaurandalibanilimi.

ZAURAN DALIBAN ILIMI

24 Jan, 05:22


SUNNONIN JUMA'A

Shaykh Muhammad bin Salih Al-Uthaymeen, Allah ya yi masa rahama yana cewa:

1-Karanta Suratul Kahfi
2-Yin wanka
3- Yin asuwaki
4- Sanya turare
5- Tafiya da wuri don isa gareshi, sammako da wuri idan rana ta fito.
6-Mutum ya sanya mafi kyawun tufafin da yake da su, sabo ko wankakke
7- Ya lalubi lokacin amsan addu'a, domin ranar Juma'a akwai wata sa'a da babu wani bawa musulmi zai dace da ita ya roqi Allah wani abu yana tsaye yana sallah face ya bashi wannan abun.
8- Yawaita salati ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam.

لقاء الباب المفتوح (105)

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

23 Jan, 18:08


💦

SAU NAWA KA YI SALATI A GARESHI (SAW) YAU??

"Manzon Allah SAW ya ce: Wanda yayi salati daya a gareni, Allah zai yi salati goma a gareshi". Muslim

Ku yawaita salati a gareshi (SAW) za ku samu alkhairai masu yawa.

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

22 Jan, 09:29


KU YAWAITA YIN NAFILOLI DOMIN DA SU ZA A CIKE GIƁIN FARILLANKU

Manzon Allah (SAW) ya ce:
"Lallai farkon abin da za a fara hisabi wa bawa musulmi a ranar Alƙiyama shi ne SALLAH, idan ya cika ta to, Idan kuma ba haka ba sai a ce: Ku duba shin bawana yana da ''Sallolin Nafila''? Idan ya kasance yana da ''Sallolin Nafila'' sai a cika ta Farillar daga Nafilolinsa. Sa'annan sai a aikata kwatankwacin hakan ga sauran ayyuka na ''Farillah''.

Ibnu Majah da Nasaa'iy, Albaniy ya ingantashi.

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

21 Jan, 15:35


🍃🌹🍃

KU KEƁANCE LOKUTA NA MUSAMMAN DOMIN ZAMA DA ZANTAWA DA IYALANKU

Ka keɓance wani lokaci na musamman ga iyalinka, ku yi hira, ku yi raha, ku yi wasa, ka ji damuwoyinsu, ku tattauna al'amuran gida, rayuwanku a nan gaba, cigabanku duniya da lahira, matsalolinku na gida don samun maslaha, tarbiyya da karatun ƴa ƴanku.... dss.

Manzon Allah (SAW) ya kasance ya na ba ma iyalansa kulawa, zama da su, fira da su, jin damuwoyinsu da nusar da su ababen da za su amfane su duniya da lahira. har ya ce: "Wanda ya fi kowa kyautatawa a cikinku shine wanda ya fi kowa kyautata ma iyalinsa, Ni ko na fi ku kyautata ma iyalina".

🍃Hira da su ba ya kawo raini ko wargi bal ma shi ke ƙara shaƙuwa, ƙauna, mutuntawa da girmamawa. Manzon Allah (SAW) ya na hira da iyalansa, su yi wasa su yi raha, kuma hakan bai sa ya rasa girma a idonsu ba!

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

18 Jan, 16:04


•┈┈•⊰✿🌹✿⊱•┈┈•

ZAMANTAKEWA

Manzon Allah (SAW) ya ce:" Kar da wani mumini ya ɗauki karan tsana ya ɗaura ma wata mumina, domin in ya ƙi wani halayyarta toh zai yi maraba da wani (halayyarta)". Muslim

___________

KA'IDA MAI MAHIMMANCI A ZAMANTAKEWA

Babu mutumin da ya tsaraitu daga aibi da tawaya, domin babu wani mutum cikakke da yake dari bisa dari, amma wanda ka samu kyawawan dabi'unsa da halayyarsa sun fi rinjaye to kuma sai ka kawar da kai daga tawayar da ya samu a wani bangaren, idan ba ka son wani hali na uwar gida to ai kuma akwai halayyarta da yawa da suke ababen so da maraba a gareka, don haka sai ka ke dubi da su ka kawar da kai daga wadancan. Kar ka manta kai din ma akwai naka halayyar da hakuri ta ke a kansu.

Haka duk wanda za ka zauna da shi to ka yi hakuri ka kuma kawar da kai daga wasu tawaya nashi domin babu wanda bashi da aibu saidai a banbanta ko na wani ya fi na wani, in ko ba haka ba to za ka zauna kai kadai ba tare da aboki ba.


#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandaliban

ZAURAN DALIBAN ILIMI

17 Jan, 09:08


•┈┈••♡🍃🌼🍃♡••┈┈•


YAUSHE A KE SAMUN JUMA'A?

Wanda ya riski raka'a ɗaya daga sallar Juma'a to haƙiƙa ya riski juma'a, (a na riskan raka'a ne da samun liman cikin ruku'u kafin ya ɗago), sai ya ƙaro wata raka'a guda bayan liman yayi sallama, Saboda faɗin Manzon Allah SAW: "Wanda ya riski raka'a ɗaya daga juma'a to ya sallaci wata raka'a guda gareta kuma sallarsa ta cika". da kuma faɗinsa: " Wanda ya riski raka'a ɗaya na sallah to haƙiƙa ya riski sallah". Amma wanda Tahiyyah kaɗai ya riska to wannan zai sallaci Azahar ne (raka'a hudu zai yi) domin juma'a ta kuɓuce masa".

فتاوى نور على الدرب لابن باز 13/194

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

•┈┈••♡🍃🌼🍃♡••┈┈•

ZAURAN DALIBAN ILIMI

16 Jan, 17:48


INA KUKE MASOYA MANZON ALLAH (ﷺ)?

❁࿐❁❁࿐❁

Manzon Allah (SAW) Ya ce: "Duk inda ku ka kasance kuyi min Salati, domin lallai salatin ku tana isa gareni."

صحيح الجامع (3164)

Mu yawaita Salati a gareShi
Barakallahu feekum🌷

#Zaurandalibanilimi

WHATSAPP
https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

16 Jan, 13:37


🌹 NEMAN GAFARAR UBANGIJI 🌹

Shaykh Ibnul Uthaimin رحمه الله ya ce: "Ina ba ka shawara ya ɗan uwa da ka yawaita Istighfari, ka yawaita ambaton "Ya Allah ka gafarta min, Allah Ka min rahama, ina neman gafararka da tuba a gareka", ko wani abu makamancin haka, me yiwuwa ka dace da lokacin da Allah zai amsa maka, sai ya gafarta maka a lokacin.

شرح رياض الصالحين ٧١٦/٦

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

15 Jan, 11:50


SAKO GA WANDA YA KE CIKIN WATA JARABAWA..

Ibnul Jauziy(RA) ya ce; "Kar da ka rika ganin lokacin bala'i ya yi tsawo har ta kai ka ga gajiya da yawan addu'a, domin an jarabceka da wannan bala'inne kuma a ka bautar da kai da yin hakuri, don haka kar da ka yanke tsammani daga rahamar Allah ko da kuwa jarabawar ta jima."

...صيد الخاطر ص439

Ubangijinka yana sonka shi yasa ya ke ta jarabtanka, Ka kara hakuri kar da ka yi fushi, kar da ka debe tsammani daga rahamar Allah, ka cigaba da kiyaye dokokin Allah ka cigaba da addu'a, Ubangijinka yana sauraronka kuma zai amsa maka...
Allah ya yaye muku dukkan damuwa ya biya muku bukatunku na alkhairi ya albarkaceku da zuri'arku baki daya.

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi‏

ZAURAN DALIBAN ILIMI

13 Jan, 15:32


KA NA SON TARA TARIN LADA?

Manzon Allah SAW yace:

"Wanda ya karanta harafi d'aya daga Littafin Allah to yana da lada d'aya, kuma kowane lada a na ninkashi zuwa goma, ba ina cewa: Alif laam meem harafi daya bane, saidai; Alif harafine, laamun harafine, meemun harafine". Tirmidhiy

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

11 Jan, 13:36



💧࿐❥💧

AMBATON ALLAH

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا●وَسَبِّحُوهُ بُكْرَةً وَأَصِيلًا".
(الأحزاب :42،41)

"Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ambaci Allah, ambato mai yawa● Kuma ku tsarkake shi, a sãfiya da maraice".

Kuma ya ce:

"الَّذِينَ آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكْرِ اللَّهِ ۗ أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ" (الرعد :28)

"Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu suka natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah zukãta suke natsuwa".

Shaykhul Islami Ibnu Taimiyyah ya ce: Ambaton Allah a gurin bawa kamar kifi ne da ruwa, yaya halin kifi zai kasance idan ya rabu da ruwa?

الوابل الصيب من الكلم الطيب 71

Daga cikin fa'idodin ambaton Allah:

💧Samun soyayyar Allah da kusanci gareshi
💧Samun rahamar Allah da Aljannarsa
💧Yayewar damuwa da bakin ciki da kunci
💧Samun kariyar Allah daga sharrin Shedanu
💧Samun gafaran Allah da sakamako mai girma.

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

09 Jan, 17:44


SHIN KA SAN IRIN SOYAYYAR DA YAKE MAKA?


Shine zai zo a ranar Alkiyama, ranar da dan uwa yake gudun dan uwansa, ranar da daa yake gudun iyayensa, ranar da kowa yake ta kansa, bayan mutane sun gigita, sun dimauce, sun firgita sun fita hayyacinsu saboda tsananin tashin hankalin da ke a wannan rana, A na tsaka da wannan hali an rasa yanda za a yi, zai je ga Allah ya yi ceto mafi girma, bayan ya fadi yayi sujada da godiya a gaban Ubangijinmu, za a ce masa: Ya Muhammad dago kanka, ka fada za a saurara, ka roka za a ba ka, ka yi ceto za a ba ka ceton, Sai ya ce: Yaa Ubangiji Al'umata, Al'umata... 


Iyayena da kaina fansa gareKa Yaa Manzon Allah(SAW).


Ku yawaita Salati a gareshi, duk wanda yayi salati daya a gareshi Allah zai yi salati goma a gareshi🌹


#Zaurandalibanilimi


TELEGRAM

https://t.me/Zaurandalibanilimi


INSTAGRAM

https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

08 Jan, 12:36


TAURARUWA CIKIN MATA

Mai ya kai wannan dadi?

Mace ta kasance: Dalibar ilimi, Mai yada alkhairi, Masaniyar sunnah, Mai kiyaye dokokin Allah Madaukaki, Mai tsoron Mahaliccinta, Mai kiyaye harshenta, kuma ta na mai kula da shi(harshen) ta na mai tsoron ya jefata ga halaka.

نصيحة عامة للنساء المسلمين/الشيخ سليمان الرحيلي

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

WHATSAPP https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N

ZAURAN DALIBAN ILIMI

07 Jan, 15:45


An ruwaito daga Umm Habeebah(RA) cewa ta ji Manzon Allah(SAW) yana cewa:

"Babu wani musulmi da zai yi sallah raka'a goma sha biyu a rana, ta nafila ba farillah ba face Allah Ya gina masa gida a Aljannah". Muslim

Shin ba ka son gida a Aljannah? Ka lizimcesu barakallahu feek

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

05 Jan, 15:17


AMSA MAI KIRAN SALLAH

Manzon Allah (SAW) Ya ce: "Idan ku ka ji mai kiran sallah to ku faɗi irin abin da ya ke faɗi, sannan ku yi salati a gareni, domin wanda ya yi salati ɗaya a gareni ALLAH zai yi salati goma a gareshi". Muslim

Za ka maimaita irin abin da mai kiran sallar yake fad'i, sai gurin da zai ce: Hayya alassalah, sai kace: Laa haula walaa quwwata illa billah, sannan in ya ce: Hayya alal falaah, sai kace: Laa haula walaa quwwata illa billah". Muslim

#Zaurandalibanilimi

Instagram:
https://www.instagram.com/p/B_NuiocDqSw/?igshid=3hzyza1v460v

Telegram:
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

02 Jan, 17:51


SHIN KA SAN IRIN SOYAYYAR DA YAKE MAKA?

Shine zai zo a ranar Alkiyama, ranar da dan uwa yake gudun dan uwansa, ranar da daa yake gudun iyayensa, ranar da kowa yake ta kansa, bayan mutane sun gigita, sun dimauce, sun firgita sun fita hayyacinsu saboda tsananin tashin hankalin da ke a wannan rana, A na tsaka da wannan hali an rasa yanda za a yi, zai je ga Allah ya yi ceto mafi girma, bayan ya fadi yayi sujada da godiya a gaban Ubangijinmu, za a ce masa: Ya Muhammad dago kanka, ka fada za a saurara, ka roka za a ba ka, ka yi ceto za a ba ka ceton, Sai ya ce: Yaa Ubangiji Al'umata, Al'umata...

Iyayena da kaina fansa gareKa Yaa Manzon Allah(SAW).

Ku yawaita Salati a gareshi, duk wanda yayi salati daya a gareshi Allah zai yi salati goma a gareshi🌹

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

02 Jan, 13:47


💎LU'U LU'U💎

Babu abin da yake ɗaga darajar ɗiya mace kamar imaninta da taqawarta, haka babu abin da ke ɗaga ƙimarta da matsayinta kamar: Ilimi, ɗabi'unta, kamewa da kunya, idan mace ta haɗa waɗancan abubuwan, to sai ta kasance lu'u lu'un da kowane mutumin kirki ke jira da fatan samu.

Kiyi ɗaukesu ɗaya bayan ɗaya kiyi ado dasu, za su ƙawata ki🌹

#Zaurandalibanilimi

Instagram:
https://www.instagram.com/p/B_NuiocDqSw/?igshid=3hzyza1v460v

Telegram
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

02 Jan, 13:44


*RAHAMAR ALLAH KE KAI MUTUM ALJANNAH*
-
"Rahamar allah itace take kai mutum aljannah, amma ba aiki ba, idan kaga kaje aljannah, to haƙiƙa bawai yawan aikinka bane ya kaika, saidai rahamar Allah, shi aikinka saidai ya zamto shine silar shigarka aljannar, amma ba dalili ba"
-
"An karɓo daga abu-hurairata Allah ya ƙara masa yarda yace: lallai Manzon Allah ﷺ, yace: babu wani ɗaya da aikinsa zai shigar dashi aljannah, sai akace: har dakai ya ma'aikin Allah?, sai yace eh har dani saidai idan ubangijina ya lulluɓeni da rahama (daga gareshi)"
Sahih Muslim (2816)
-
"Duk wanda yake ganin cewa lallai aikinsa shine zai kaishi zuwa ga aljannah, to haƙiƙa zai kafircewa rahamar Allah wacce itace zata zamto dalilin shigar aljannar tasa, ba aikinsa ba"
-
-
Sabon Instagram ɗinmu 👇
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
-
-
Telegram chennel 👇
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes

ZAURAN DALIBAN ILIMI

01 Jan, 19:01


RAKA'OI BIYUN ALFIJR
(Raka'atayy Alfajr)

Manzon Allah SAW yace: "Raka'oi biyu na Alfijr sun fi duniya da abin da yake cikinta alkhairi". [Muslim 725]

●Sunna ce
●Raka'oi ce guda biyu sauk'ak'a
●Ana yinta bayan bullowar Alfijr na gaskiya kafin a sallaci Sallar Asuba
●Ana yinta a halin tafiya ko zaman gida
●Ana karanta: Fatiha da Qulya ayyuhal kafirun a raka'ar farko, Ta biyun: Fatiha da Qul huwallahu Ahad. Ko Fatiha kadai a duka raka'oin
●Wanda ya shiga masallaci yayi ta, to ta wadatar masa yin Tahiyyatul masjid, in kuma yayi niyyansu a tare to hakan yayi kyau(اللجنة الدائمة/271-7)
●Wanda sallar asuba ta kubuce masa: zai fara sallatar Raka'atay fajr sannan yayi sallar asuba(Ibnul Bazz/Majmu'ul fataawa:377/11)
●Wanda ta kubuce masa yana da zabin ya sallaceta bayan sallar asuba ko jinkirta ta zuwa dagowar rana(Ibnul Bazz/Majmu'ul fataawa:373-11)

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

31 Dec, 06:06


Hasanul Basariy Rahimahullah Ya ce: "Idan har ba ka kasance mai haƙuri ba, to ka koyi haƙuri, Idan ba ka kasance malami ba, to ka nemi ilimi, domin duk wanda yake kamanceceniya da wasu mutane za a haɗa shi da su/zai isa garesu"

مجمع الآداب في معجم الألقاب (٣٧٤)

#Zaurandalibanilimi

WHATSAPP CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

29 Dec, 05:32


ZAURAN DALIBAN ILIMI pinned «#ADON_DALIBIN_ILIMI 11/50 FASALI NA BIYU YANDA A KE NEMAN ILIMI DA DAUKAN KARATU CIGABA: 11● Dalibi ya fara daga qananun littafai kafin manya, kananun littafai zuwa manya sun banbanta daga wannan qasa zuwa wani, da kuma Sabanin Mazhabobi (Mazahabar…»

ZAURAN DALIBAN ILIMI

29 Dec, 04:39


💧AZKAR DIN KA💧

Me ya kai dadin bawa ya fara ranarsa da Ambaton Mahaliccinsa, sai ya sami taimako, nasara da kariya daga Mahaliccinsa.

Ki/Ka yi Azkar din ka kuwa???

Latsa nan domin ganin Zikirorin safe/yamma👇

https://t.me/Zaurandalibanilimi/1028?single

#Azkar #Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

28 Dec, 06:04


🔶 KAFFARAR ZUNUBAI🔶

Daga Abdullahi dan Mas'ud  Allah Ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Babu wani musulmi da abin cutarwa, ko rashin lafiya ko wani abu ya same shi, face Allah ya kankare masa zunubansa, kamar yadda bishiya ke zubar da ganyenta".

صحيح البخاري (5667)

#Zaurandalibanilimi

Telegram
https://t.me/Zaurandalibanilimi

Instagram
https://www.instagram.com/p/B_NuiocDqSw/?igshid=3hzyza1v460v

ZAURAN DALIBAN ILIMI

26 Dec, 17:38


YAWAITA SALATI GA MANZON ALLAH ﷺ

Ibnul Jauziy (RA) Ya ce: "Ku sani babu wani bawa musulmi da zai yawaita yin salati ga Annabi Muhammad ﷺ fa ce:
(1)Allah ya haskaka zuciyarsa,
(2)Ya gafarta masa zunubansa,
(3)Ya buda masa kirjinsa,
(4)Ya saukaka masa lamurransa,
Saboda haka ku yawaita salati ga Annabi ﷺ".

ﺑﺴﺘﺎﻥ ﺍﻟﻮﺍﻋﻈﻴﻦ ﺹ ٢٩٧

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

26 Dec, 15:21


"Yin aiki ba tare da Ikhlasi da koyi da Sunnah ba, kamar matafiyi ne ya cika jakarsa ta tafiya da kasa, gashi da nauyi amma kuma ba zai amfaneshi ba".

Ibnul Qayyim RA.

#Zaurandalibanilimi

https://www.facebook.com/Zaurandalibanilimi/

ZAURAN DALIBAN ILIMI

25 Dec, 09:03


KASHEDINKU DA TAYASU MURNAN IDINSU

Taya kafurai murnan Idinsu ta hanyar nuna farin ciki da murna, ba su kyautuka ko taimakonsu a kan shagalin idinsu nau'i ne na nuna soyayya da kauna kuma Allah ya hane mu a kan hakan, Allah Madaukaki ya ce:

"يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْيَهُودَ وَالنَّصَارَىٰ أَوْلِيَاءَ ۘ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ"

(المائدة :51)

"Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi Yahudu da Nasãra majiɓinta. Sãshensu majiɓinci ne ga sãshe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ yanã daga gare su. Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai".

Kuma Ya ce:

"يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا عَدُوِّي وَعَدُوَّكُمْ أَوْلِيَاءَ تُلْقُونَ إِلَيْهِم بِالْمَوَدَّةِ وَقَدْ كَفَرُوا بِمَا جَاءَكُم مِّنَ الْحَقِّ..."

(الممتحنة:1)

"Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi maƙiyĩNa kuma maƙiyinku masõyi, 845. Kuna jẽfa sõyayya zuwa gare su, alhãli kuwa haƙĩƙa sun kãfirta da abin da ya zo muku, na gaskiya..."

IslamQnA
WHATSAPP
https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

25 Dec, 09:03


HARAMUN NE TAYA SU MURNAN KIRSIMETI

Shaykh Ibnu Bazz ya ce:

Ba ya halatta ga musulmi ko musulma su yi tarayya da yahudu da nasara ko wasunsu cikin bukukuwan Idinsu(ta hanyar taya su murna/ce musu happy christmas dss), wajibi ne barin yin hakan domin duk wanda yayi kamanceceniya da wasu mutane to yana cikinsu, Manzon Allah (SAW) kuwa ya gargademu a kan kamanceceniya dasu da dabi'antuwa da dabi'unsu, saboda haka wajibi ne musulmi da musulma su kiyayi wannan kuma ba ya halatta su taimaka da komai a cikin wannan domin Idi ne da ya saba wa Shari'a.

مجموع فتاوى ومقالات متنوعة 6/405

#Zaurandalibanilimi

WHATSAPP
https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

03 Dec, 17:56


Shaykh Muh'd Saleh Al'Uthaimeen (RA) ya ce:

"Galibi karatun Alkur'ani da daddare ya fi tsananin halarto da zuciya, musamman ma idan ya kasance an yi barci an tashi".

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

"Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana".
(المزمل 6)

اللقاءات الرمضانية 37ص

#Zaurandalibanilimi

Telegram: https://t.me/Zaurandalibanilimi

Instagram: https://www.instagram.com/p/B_NuiocDqSw/?igshid=3hzyza1v460v

ZAURAN DALIBAN ILIMI

29 Nov, 20:33


*SALLAR ASUBAH MAFARIN AIKI*💫

Ibnul Qayyim (رحمه الله) ya ce:
"Sallar ASUBAHI Ita ce  tushen aiki kuma mafaransa(da ita ne bawa zai bude ayyukansa na yinin wannan ranar)".


زاد المعاد (٧٨)
#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

29 Nov, 09:04


FALALAR JUMA'A

"Wanda yayi wanka ranar juma'a ya zama sababin wanka ya yi sammako zuwa masallaci, ya kusanci liman kuma ya saurari khuduba, to duk wani taku da yayi yana da ladan shekara; ladan azumtarta da tsayuwan daraden cikinta".
Tirmidhi ya ruwaito, Albaniy ya ingantashi cikin Saheeh Attargeeb

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

28 Nov, 17:32


YAWAITA SALATI A DAREN JUMA'A

◈•┈┈•◄✾ 🌹✾►•┈┈•◈

MU YAWAITA SALATI A GARESHI (SAW) A DAREN JUMAA DA RANAR JUMA'A

Manzon Allah SAW yace:"Ku yawaita Salati a gareni ranar juma'a da kuma daren juma'a: duk wanda yayi salati d'aya a gareni, Allah zai yi salati goma a gareshi".

[Sunan Baihaqiy:5994. Albaniy ya ingantashi cikin Assaheehah:1407]

Instagram:
https://www.instagram.com/p/B_NuiocDqSw/?igshid=3hzyza1v460v

Telegram:
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

27 Nov, 08:00


ZIKIRI

قال الشيخ الشنقيطي رحمه الله : كثرة الذكر له سِرّ عجيب في الفتح، وفي التوفيق وفي التيسير، فإذا أراد الله أن يزيد درجة العبد جعله يذكر الله على كل أحيانه،
[ أقوال السلف الصالح]

Imamu As-Shankidiy(Rh) ya ce: "Yawan yin Zikiri yana da wani sirrin na ban mamaki na samun budi, haka ma kuma samun dacewa da samun saukin al'amuran rayuwa, saboda haka ne ma idan Allah yayi nufin daukaka darajar bawansa, sai ya sanya shi ya zamto mai ambatonsa a koda yaushe".

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

25 Nov, 11:01


ابشر بما يسرك يا أبا البنات💝👛🎀

ZAURAN DALIBAN ILIMI

25 Nov, 11:01


🎀KA YI BUSHARA YA KAI UBAN 'YA 'YA MATA🎀

Manzon Allah ﷺ ya ce:

"Wanda ya raini 'yan mata guda biyu har suka balaga(ya kula da su ya ba su ingantacciyar tarbiyyah), zai zo a ranar Alkiyama Ni da shi kamar haka (Sai ya hada yatsun hannunsa guda biyu ✌🏼)". Muslim ya ruwaito

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

24 Nov, 14:37


SHIN KO KA SAN....

Yawan zunubai na hana ma mutum yin dace a al'amuransa kuma a ki amsa addu'oinsa??

Shaykh Muhd bn Saleh Al'Uthaimeen ya ce:

"Zunubai na iya yin shamaki a tsakanin mutum da dacewarsa, sai ya zama ba a datar dashi Kuma ba a amsa addu'oinsa".

(شرح العقيدة الواسطية:361/1)

🌵Sai ka ji mutum na cewa: Anya kuma ba hannu a ka samun ba? Komai na sa a gaba babu nasara bare dacewa!!

Shin ka taba zama ka yi tunanin ko zunubanka ne suke da hannu a ciki?

To yanzu ya zan yi? menene mafita?

Kwantar da hankalinka ai Ubangiji yana farin ciki da dawowar bawansa gareshi.

Mafita shine yin ingantacciyar tuba da yawan Istigfari🌹yawaita ayyuka na kwarai, lallai kyawawan ayyuka suna goge munana.

Allah ya biya muku bukatunku ya cika rayuwarku da albarka🌷

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

24 Nov, 05:16


💦TUNATARWA: AZKAR DIN KA🌹

Yin sakaci da Azkar din safe da Yamma kamar yin sakaci ne ka bar wata k'ofa da sharri ko cutarwa za su iso gareka!

Hanzarta ka yi zikirorinka barakallahu feek🌷

Latsa nan domin ganin Zikirorin safe da yamma👇👇

https://t.me/Zaurandalibanilimi/1028?single

#Azkar #Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

23 Nov, 12:08


🛑ZUNUBI🛑

Ibnul Qayyim(RA) ya ce: "Kar da ka rudu idan ba ka ga tasirin zunubinka ba a lokacin da ka aikata, za ka iya ganin tasirinsa bayan shekara arba'in.

الداء والدواء 130

Allah Ka gafarta mana zunubanmu Ameen.

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

21 Nov, 17:21


SHIN KA SAN IRIN SOYAYYAR DA YAKE MAKA?

Shine zai zo a ranar Alkiyama, ranar da dan uwa yake gudun dan uwansa, ranar da daa yake gudun iyayensa, ranar da kowa yake ta kansa, bayan mutane sun gigita, sun dimauce, sun firgita sun fita hayyacinsu saboda tsananin tashin hankalin da ke a wannan rana, A na tsaka da wannan hali an rasa yanda za a yi, zai je ga Allah ya yi ceto mafi girma, bayan ya fadi yayi sujada da godiya a gaban Ubangijinmu, za a ce masa: Ya Muhammad dago kanka, ka fada za a saurara, ka roka za a ba ka, ka yi ceto za a ba ka ceton, Sai ya ce: Yaa Ubangiji Al'umata, Al'umata...

Iyayena da kaina fansa gareKa Yaa Manzon Allah(SAW).

Ku yawaita Salati a gareshi, duk wanda yayi salati daya a gareshi Allah zai yi salati goma a gareshi🌹

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

20 Nov, 04:55


حسنات لا تعد💡

An ruwaito daga Abu Hurairah(RA) cewa Manzon Allah(ﷺ) ya ce: "Wanda ya ce: "LA ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LAA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADEER". Sau dari (100) a rana, za a ba shi ladan 'yantar da bayi guda 10, Kuma za a rubuta masa lada guda 100, kuma a kankare masa zunubai guda 100, kuma za ta zame masa kariya daga shaidan a wannan ranar har zuwa yammaci, kuma babu wanda zai zo da abin da ya fishi lada sai mutumin da ya aikata fiye da shi". Bukhariy da Muslim

__

Malamai suka c
e hadisin bai shardanta cewa lallai sai an yi duka darin nan take a lokaci guda ba kafin a samu wannan falalar, abin da a ke so dai ya kasance a yini guda ne a ka yi su sau darin.

Imam Annawawiy Rahimahullah ya ce: Abin da yake zahiri ga wannan hadisin shine a na samar da wannan lada da a ka ambata a wannan hadisin ga wanda ya fadi wannan hailalan sau dari a ranarshi ko da yayi su a tare ko a rarrabe a gurare daban daban, ko wasu daga ciki yayi a farkon yini wasu kuma a karshen yini.

Sai dai abin da ya fi shine: Ya yi su a tare a farkon yini, domin ta kasance masa tsari da kariya a duka yininsa".

شرح النووي على مسلم 17/17

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

WHATSAPP https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N

ZAURAN DALIBAN ILIMI

20 Nov, 04:54


حسنات لا تعد💡

روى البخاري ومسلم من حديث أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : ( مَنْ قَالَ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ ، فِي يَوْمٍ مِائَةَ مَرَّةٍ ؛ كَانَتْ لَهُ عَدْلَ عَشْرِ رِقَابٍ ، وَكُتِبَ لَهُ مِائَةُ حَسَنَةٍ ، وَمُحِيَتْ عَنْهُ مِائَةُ سَيِّئَةٍ ، وَكَانَتْ لَهُ حِرْزًا مِنْ الشَّيْطَانِ يَوْمَهُ ذَلِكَ حَتَّى يُمْسِيَ ، وَلَمْ يَأْتِ أَحَدٌ بِأَفْضَلَ مِمَّا جَاءَ ، إِلَّا رَجُلٌ عَمِلَ أَكْثَرَ مِنْهُ".

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

WHATSAPP https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N

ZAURAN DALIBAN ILIMI

19 Nov, 09:39


✿❁࿐❁✿ 🥗🥗 ‏​✿❁࿐❁✿

ALHADEETH

Manzon Allah (ﷺ) yace:
"Duk wanda yaci abinci saannan ya ce: "Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da ni wannan abincin, kuma ya azurta ni dashi ba tare da wata dabara daga gare ni ba ko wani karfi", an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa..."

[Albani ya hassanashi: Saheeh Attargeeb-2042]

 "الحَمْدُ لِلّهِ الّذِي أَطعَمَنِي هذا وَرَزقَنِيهِ مِنْ غَيْرِ حَوْلٍ مِنِّي ولا قُوَّة".

#Zaurandalibanilimi

Instagram:
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=1voytacck9z4l

Telegram:
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

18 Nov, 13:07


ƘAIƘAYI KOMA KAN MASHEƘIYA

Babban Malami Ash-Sheikh Ibnl Qayyum Al-jauziyya (RA) Yace: Tabbas mutane sun shaida a fili cewa duk wanda ya rayu da Makirci, zai mutu da Talauci.

"ولا يَحيقُ المَكرُ السَّيِّئُ إلَّا بأهلِهِ"

(Igathatul lahfan 1/358)
-
Telegram
https://t.me/Zaurandalibanilimi
-
Instagram
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

17 Nov, 09:55


Shin kana sane cewa kullum ka kwana ka wayi gari rayuwarka kake cinyewa???

Hasan Albasary yace: Ya kai dan Adam, ka sani kai kwanaki ne, duk sanda ranarka ta tafi to wani yanki naka ya tafi...

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

16 Nov, 16:39


KU YAWAITA GUZURIN ZUWA LAHIRA

Aliyu bnul Husain ya kasance idan faqiri ko mabukaci ya zo gurinsa sai yayi bushara kuma ya ce: Maraba da wanda zai daukan mun guzurina zuwa lahira".

صفة الهفوة 2/95

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

14 Nov, 19:44


💦MU YAWAITA SALATI A GARESHI (SAW)

Manzon Allah SAW ya ce: "Ku yawaita salati a gareni a daren Juma'a da ranar Juma'a, wanda yayi salati daya a gareni, Allah zai yi salati goma a gareshi" Baihaqiy, Albaniy ya ingantashi

💦💦💦

اللهمَّ صلِّ على محمَّد وعلى آل محمَّد، كما صليتَ على إبراهيم وعلى آل إبراهيم؛ إنَّك حميدٌ مجيد. اللهمَّ بارِك على محمَّد وعلى آل محمَّد، كما باركتَ على إبراهيم وعلى آل إبراهيم؛ إنَّك حميدٌ مجيد [البخاري ومسلم]

ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMAD, KAMAA SALLAITA ALA IBRAHEEM WA ALA ALI IBRAHEEM, INNAKA HAMEEDUN MAJEED, ALLAHUMMA BAARIK ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMAD, KAMAA BAARAKTA ALA IBARAHEEM WA ALA ALI IBRAHEEM, INNAKA HAMEEDUN MAJEED.

Wanda ya lizimci yawaita salati ga Manzon Allah damuwanshi da bakinciki za su kwaranye🌹

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

13 Nov, 10:55


KANA SON SAMUN HUTU DA NATSUWAR ZUCIYA?

"Babu abin da ya ke natsar da zukata kuma ya hutar da rayuka face komawa ga Allah".
Shaykh Ibnu Bazz(RA)

الفتاوى 2/361

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

12 Nov, 13:48


KAR KA YARDA KA TAFI LAHIRA DA HAKKIN WANI!


Manzon Allah SAW ya ce: "Duk wanda akwai wani zalumci na dan uwanshi a kanshi na daga mutuncinshi (ka zalumceshi ka zubar masa da mutunci) ko kuma wani abun na daban, to ya je ya warwareshi(ya ba shi hakuri su sasanta kansu), tun kafin lokacin da yin hakan ba zai kasance da dinari ko dirhami ba, In yana da kyawawan ayyuka a ciki za a dauki gwargwadon zalumcin da ya yi (a biya), idan kuma babu kyawawan ayyuka za a dauko daga munanan ayyukan abokin nasa (wanda ya zalumta) a daura masa". Bukhary


#Zaurandalibanilimi


TLEGRAM

https://t.me/Zaurandalibanilimi


INSTAGRAM

https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

11 Nov, 04:43


💦TUNATARWA: AZKAR DIN KA🌹

Yin sakaci da Azkar din safe da Yamma kamar yin sakaci ne ka bar wata k'ofa da sharri ko cutarwa za su iso gareka!

Hanzarta ka yi zikirorinka barakallahu feek🌷

Latsa nan domin ganin Zikirorin safe da yamma👇👇

https://t.me/Zaurandalibanilimi/1028?single

#Azkar #Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

11 Nov, 04:06


ALQAWAREER EDUCATIONAL FOUNDATION TANA FARIN CIKIN GAYYATAR YAN UWA MAZA DA MATA DAURA DATA SHIRYA MUSU TA KWANA BIYU MAI TAKEN:

Matakan ingantacciyar tarbiyya

خطوات عملية لتربية إسلامية صحيحة

Steps to a correct islamic parenting





WANDA ZAI GUDANA A SHAFIN MAKARANTA NA MU'ASSASATUL QAWAREER DAKE TELEGRAM

AL'MUDARRIB/TRAINER:
MALAM AL'AMIN AHMAD HAMZA

RANA: LARABA DA ALHAMIS
11&12 JUMADAL ULA, 1446 ( 13&14 NOV, 2024)
LOKACI: KARFE TAKWAS NA DARE 8:00PM TO 10:00PM

LINK DIN AJIN👇🏻

https://t.me/Alqawareeracademy

ZAURAN DALIBAN ILIMI

10 Nov, 16:31


•• 🌸 ••
..💛🌿..

Kar da ka bar wata rana ta wuce ka ba tare da ka karanta wani bangare na Alkur'ani ba ko da ba yawa, idan an yawaita lada ya yawaita, farinciki zai yawaita, alkhairi ya yalwata, albarka ya yawaita shaidanu da sharri suyi karanci🌷

Allah ya muku albarka.

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

09 Nov, 10:49


•┈┈••🍃••┈┈•

KU YI BUSHARA YA KU MA'ABOTA HAƘURI


Allah Maɗaukakin Sarki ya ce:

"إِنَّمَا يُوَفَّى الصَّابِرُونَ أَجْرَهُم بِغَيْرِ حِسَابٍ".
{الزمر :10}

"Mãsu haƙuri kadai a ke cika wa sakamakonsu, bã da wani lissãfi ba".

Wannan kuwa ya ƙunshi dukkan haƙuri:
●Haƙuri a kan ƙaddarorin Allah kar da bawa yayi fushi ko ya ƙi yarda da ƙaddara.
●Haƙuri a kan saɓon Allah, kar da ya aikata.
●Haƙuri a kan ɗa'a ga Allah, yayi biyayya da aiwatar da ita.

Sai Allah ya yi alƙawarin sakamako ga masu haƙuri ba tare da ƙididdigewa ba: Ma'ana ba tare da haddi ko iyakancewa ba, wannan kuma saboda falala da matsayin haƙuri ne a gurin Allah, kuma shine mai taimako a kan dukkan lamurra.

تفسير السعدي

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

07 Nov, 17:38


YAWAITA SALATI GA MANZON ALLAH ﷺ

Ibnul Jauziy (RA) Ya ce: "Ku sani babu wani bawa musulmi da zai yawaita yin salati ga Annabi Muhammad ﷺ fa ce:
(1)Allah ya haskaka zuciyarsa,
(2)Ya gafarta masa zunubansa,
(3)Ya buda masa kirjinsa,
(4)Ya saukaka masa lamurransa,
Saboda haka ku yawaita salati ga Annabi ﷺ".

ﺑﺴﺘﺎﻥ ﺍﻟﻮﺍﻋﻈﻴﻦ ﺹ ٢٩٧

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

28 Oct, 12:30


RERA KARATUN ALKUR'ANI

Shaykh Abdil Azeez Ibn Bazz Allah ya yi masa rahama ya ce:

Rera Alkur'ani shine: Bayyana karatunsa tare da kyautata sauti da natsuwa a cikinsa har zukata su motsa, domin dama manufar shine motsa zukata da wannan Alkur'anin har ta yi tawali'u kuma ta sami natsuwa kuma ta amfana.

Majmu'ul fataawa(349/11)

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

27 Oct, 07:24


KA KASANCE A DUNIYA TAMKAR BAƘO KO MATAFIYI

Manzon Allah SAW yace: “Ka kasance a duniya kamar bako, ko kuma matafiyi da yake kan hanya”. Ibnu Umar (RA) ya kasance yana cewa: Idan ka yi yammaci kar ka jira safiya, idan kuma ka wayi gari to kar da ka jira yammaci, ka ribaci lokacin lafiyarka, saboda lokacin rashin lafiyarka, ka ribaci lokacin rayuwarka kafin mutuwarka". Bukhary

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

26 Oct, 20:41


❁࿐❁❁࿐❁

Ka ribaci daya bisa ukun dare na karshe...

Ta yi wu raka'oi biyu cikin duhun dare su zama sanadiyyar yayewan kunci, damuwa da bakin cikinka...

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

❁࿐❁❁࿐❁

ZAURAN DALIBAN ILIMI

24 Oct, 11:05


💧💕💧

SHI: Ni dai kina burgeni sosai, kuma ina fata ki bani dama don na tabbatar miki da gaskiyar yanda nake ji a kan ki.

ITA: Muna da matsuguni da yake da kofa wanda ake iya kwankwasawa domin neman izini, Ina da Uba mai karamci da karrama bako, halattacciyar soyayya ita mu ke yi wa shimfida da maraba, idan da gaske ka ke to kana da dukkan dama domin nemanta ta hanyar da Allah ya shar'anta.

#Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM:
https://www.instagram.com/p/B_NuiocDqSw/?igshid=3hzyza1v460v

TELEGRAM:
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

23 Oct, 19:55


🍃YA YIN KWANCIYA BARCI

Manzon Allah (SAW) ya ce:

"Idan ka zo kwanciya a shimfidarka, Ka karanta Ayatul Kursiyy "Allahu laa ilaha illa Huwal Hayyul Qayyuum..", domin wani mai tsaro daga Allah ba zai gushe ba a gareka, kuma Shaydan ba zai kusance ka ba har ka wayi gari". Bukhary

________________

*AYATUL KURSIYY ITA CE*:

*"اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ ۚ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ ۚ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِندَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ ۚ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ ۖ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ".*

البقرة (255) Al-Baqara

"Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.

#Azkar #Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

21 Oct, 11:56


SAKO GA WANDA YA KE CIKIN WATA JARABAWA..

Ibnul Jauziy(RA) ya ce; "Kar da ka rika ganin lokacin bala'i ya yi tsawo har ta kai ka ga gajiya da yawan addu'a, domin an jarabceka da wannan bala'inne kuma a ka bautar da kai da yin hakuri, don haka kar da ka yanke tsammani daga rahamar Allah ko da kuwa jarabawar ta jima."

...صيد الخاطر ص439

Ubangijinka yana sonka shi yasa ya ke ta jarabtanka, Ka kara hakuri kar da ka yi fushi, kar da ka debe tsammani daga rahamar Allah, ka cigaba da kiyaye dokokin Allah ka cigaba da addu'a, Ubangijinka yana sauraronka kuma zai amsa maka...
Allah ya yaye muku dukkan damuwa ya biya muku bukatunku na alkhairi ya albarkaceku da zuri'arku baki daya.

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi‏

ZAURAN DALIBAN ILIMI

20 Oct, 16:07


TUNATARWA: AZUMIN GOBE GA WANDA YA SAMU IKO

FALALAR AZUMI SABODA ALLAH

Manzon Allah(SAW) ya ce: Allah Madaukaki ya ce: Dukkan ayyukan dan adam nasa ne face azumi, shi Nawa ne kuma Ni zan saka dashi, Na rantse da wanda ran Annabi Muhammad (SAW) ya ke hannunsa, warin bakin mai Azumi ya fi dadi a wajen Allah fiye da kamshin turaren miski". Al-Bukhary

Shin ba ka son kasancewa cikin masu azumi?

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

20 Oct, 04:40


TUNATARWA: AZKAR DIN SAFE

Da ambaton Allah ne kadai zukata suke samun natsuwa, kwanciyar hankali, arziki, tsari da kariya ma kansu da dukiyoyinsu.

Ka fara rananka da Ambaton Allah

Latsa nan domin ganin Zikirorin safe/yamma👇

https://t.me/Zaurandalibanilimi/1028?single

Kar da ka manta da wuridinka na daga Alkur'ani🌷

#Azkar #Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

19 Oct, 15:25


KA KIYAYE GANINKA

Manzon Allah (SAW) ya ce: Zinar ido shine kallo...

Shaykh Muh'd Saleh Al-Uthaimeen ya ce:

"Mutumin da ya ke sake ganinshi ga mata dole ne ya faɗa bala'i, Idan mutum ya zama duk sanda mace ta gifta ta gurinshi sai ya kama kallonta, to kuwa dole ne ya wahalar da zuciyarsa, kuma imaninsa ya ragu, kuma dole ne ya faɗa cikin wasu al'amuran da ba zai iya tsere musu ba daga baya."

مجموع الفتاوى:237/19

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

18 Oct, 13:59


KU LALUBI LOKACIN KARBAN ADDU'AR RANAR JUMA'A

Manzon Allah SAW yace:"A (Ranar) Juma'a a kwai wani lokaci da babu wani bawa musulmi da zai dace da ita, yana a tsaye yana sallah, sai ya rok'i Allah wani alkhairi face Allah ya bashi". Bukhary da Muslim

Magana mafi rinjaye shine wannan lokaci yana a tsakanin bayan la'asar ne zuwa faduwar rana.

Allah ya datar damu wannan lokaci ya amsa mana addu'oinmu.

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

WHATSAPP https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N

ZAURAN DALIBAN ILIMI

17 Oct, 17:40


SALATI A DAREN JUMA'A
🌀•┈┈•◄✾ 💧✾►•┈┈•🌀

MU YAWAITA SALATI A GARESHI (SAW) A DAREN JUMAA DA RANAR JUMA'A

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ku yawaita Salati a gareni ranar juma'a da kuma daren juma'a: duk wanda yayi salati d'aya a gareni, Allah zai yi salati goma a gareshi".

[Sunan Baihaqiy:5994. Albaniy ya ingantashi cikin Assaheehah:1407]

TELEGRAM:
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM:
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

17 Oct, 12:45


KU QULLA ABOTA DA ALKUR'ANI

Ku qulla abota da Alkur'ani ta hanyar yawaita tilawarsa, da saukeshi(khatma), Aiki dashi da tadabburin ma'anoninsa

Manzon Allah(ﷺ) ya ce: "Ku karanta Alkur'ani, domin zai zo a ranar Alkiyama yana mai ceton ma'abotansa". Abu Dawud

#Ramadan
#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

16 Oct, 12:53


🌱🌼🌱

Imam Ibn Qayyim(RA) yana ce wa "Duk lokacin da Allah Maɗaukakin Sarki ya hana bawansa mumini wani abu daga cikin rayuwansa ta duniya, to haƙika zai chanja masa da abu mafi alkhairi a gareshi. Amma ku sani cewa ba kowa Allah ya ke ba wannan ba sai mumini.
Allah ya bamu duk abin da muke buƙata duniya da lahira.

Al_Fawaa'id

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24

ZAURAN DALIBAN ILIMI

16 Oct, 04:46


TUNATARWA: AZKAR DIN SAFE

Me ya kai dadin bawa ya fara ranarsa da Ambaton Mahaliccinsa, sai ya sami taimako, nasara da kariya daga Mahaliccinsa.

Ki/Ka yi Azkar din ka kuwa???

Latsa nan domin ganin Zikirorin safe/yamma👇

https://t.me/Zaurandalibanilimi/1028?single

#Azkar #AmbatonAllah

ZAURAN DALIBAN ILIMI

14 Oct, 13:06


KAR KA RIKA YI MA IYALANKA ROWAN..

Murmushi, kyawawan magana, jaddada mata kaunarka a gareta, yabawa da gode ma kokarinta, ba ta lokaci, mahimmanci, kulawa, kyautuka musamman irin na ba za ta... dss

Imam Malik RA ya ce: "Yana kamata ga namiji ya rika kyautata ma iyalan gidansa har sai ya zama mafi soyuwan mutane a garesu".المنتقى شرح الموطأ 7/212

Ita ta fi cancanta da wadancan kyautuka, kyautatawa da kyawawan lafuzzan ba waccen HAJIYAR WAJEN BA!

#Auren_sunnah
#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

13 Oct, 17:26


💦TUNATARWA

AZUMIN GOBE LITININ/ALHAMIS GA WANDA YA SAMU IKO

Ina kuke ma'abota kofar Arrayyan? Kun san ko suwaye su?

"Lallai a Aljannah akwai wata kofa da a ke ce mata Arrayyan, a ranar Alkiyama masu azumi za su shiga ta wannan kofar, babu wanda zai Shiga ta cikin ta face su, za a ce ina masu azumi sai su mike, babu wanda zai shiga ta cikin ta face su, idan kuma suka shiga sai a kulle, babu wanda zai sake shiga ta cikin ta". Bukhary da Muslim

Domin kasancewa cikin ma'abota wannan kofa sai mu yawaita azumin nafila, ka tunatar da wasu kana da ladan hakan🌹barakallahu feekum

#Zaurandalibanilimi

WHATSAPP
https://whatsapp.com/channel/0029Va4xUAo2phHEVtrLQ50N

TELEGRAM:
https://t.me/Zaurandalibanilimi

ZAURAN DALIBAN ILIMI

13 Oct, 13:09


LOKACI SHINE RAYUWA

Shaykh Bin Bazz yace:

Duk wanda ya halakar da lokacinsa to ya halakar da rayuwarsa, wanda kuwa ya halakar da rayuwarsa zai yi nadama, kuma nadamar ba za ta amfaneshi ba.

المجموع الفتاوى:16/261

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi