SCTv Africa HS @sunusicryptotv Channel on Telegram

SCTv Africa HS

@sunusicryptotv


Number one channel for verified news and updates on blockchain and cryptocurrencies.
Contact: [email protected]
Youtube: youtube.com/@SunusiCryptoTV
X (twitter): x.com/SCTvAfrica
Facebook: https://www.facebook.com/sunusi.d.ali

SCTv Africa (English)

Are you looking for reliable news and updates on blockchain and cryptocurrencies? Look no further than SCTv Africa! This Telegram channel is your number one source for verified information in the world of digital currencies. Whether you're a seasoned investor or just starting out in the crypto world, SCTv Africa has got you covered with the latest trends, market analysis, and expert opinions.

Run by the dedicated team at @sunusicryptotv, SCTv Africa is committed to delivering high-quality content that will keep you informed and up to date on all things blockchain. From breaking news to in-depth analysis, this channel is your go-to resource for everything crypto-related.

Want to connect with the SCTv Africa team? You can reach out to them via email at [email protected]. You can also check out their YouTube channel at youtube.com/@SunusiCryptoTV for video content and tutorials. Follow them on Twitter at x.com/SCTvAfrica and on Facebook at https://www.facebook.com/sunusi.d.ali to stay connected with the latest updates and announcements.

Don't miss out on the opportunity to stay ahead of the curve in the fast-paced world of blockchain and cryptocurrencies. Join SCTv Africa today and become a part of a thriving community of like-minded individuals who share a passion for digital currencies and decentralized technologies. Stay informed, stay updated, and stay connected with SCTv Africa!

SCTv Africa HS

03 Dec, 11:22


Mey kuke tunani dan gane da hoton na?
😅🔥

SCTv Africa HS

02 Dec, 18:14


Akwai full time yan crypto, sune wayanda duk yanayin da kasuwar crypto ta juya ba’a daina jin duriyarsu. Ma’ana dai sune wayanda ko achikin bear market ba’a daina jin duriyarsu, haka zalika idan ana bull market anajin duriyarsu.

Akwai kuma seasonal yan crypto, sune wayanda ba’a jinsu sai kasuwar crypto ta shiga bull run. Ma’ana dai ana shiga bear market zaka nemesu ka rasa. Kuma hakan yana faruwa kasancewar seasonal yan crypto iya trading da/ko holding kawai suka iya, su kuwa wayannan abubuwan basa yiwuwa a lokachin da kasuwar take extremely bear market.

Kamar yanda kuka sani cewa kasuwar crypto tanada yanayi biyu. Bull market da bear market, kasancewar kuma circle din kasuwar crypto shekaru hudune, bear market yana daukar shekaru biyu da rabi, yayin da bull market yake daukar shekara daya da rabi (wannan iya abin daya faru abayane, ba’asan menene zaizo a gaba ba).

Idan ana bear season, yan crypto sukan mayarda hankalinsu wajen yin aikace-aikace (crypto jobs) ga crypto projects, sannan kuma sukan koyi ilimin dazai amfanesu idan bull season yazo. Ma’ana dai alokachin bear season, yan crypto sukan tsame dukkan kudadensu dağa kasuwa, sakamakon kasuwar tana yin kasa ne sosai alokachin. A bear market, mafi yawan crypto projects sukan mayarda hankalinsu wajen building din project dinsu, don haka suna bukatar ma’aikata kadan.

Idan ana bull season, yan crypto suka mayarda hankalinsu ne kan yin trading da holding. Kuma a wannan lokachin ne ake kokarin koyar skills da zasu taimaka maka wajen samun crypto jobs idan bear market yazo.

Yanzu da ake chikin bull season, kamata yayi muyi kokarin koyar skills da zasu taimaka mana wajen zama full time yan crypto. Misali, zamu iya koyan community management ko moderation, ko kuma mu koyi crypto content creation, da sauransu. Ire-iren wayannan skills din idan mutum ya koyesu a yanzu, chikin sauki zai samu aiki idan bear season, wanda akalla za’a dinga biyansa mafi karanchi $200 zuwa $500 a kowanne wata (wasu project din har $1000 suna boya).

Misali, idan mutum yana son koyon community managing ko moderation dole ya iya sarrafa telegram bots kamar Mrs Rose da sauransu, dole ya iya kirkirar telegram bots, da sauran abubuwan daya kamata ya koya. Haka zalika idan mutum yana son koyon crypto content creation, saiya koyi salon iya rubutu na jan hankali, da sanin yanda ake amfani da emojis, da sauransu.

A yanzu, idan mutum yana koyon wayannan skills din, sai kuma yayi aiki a kyauta (volunteer), ko kuma a kudi kadan kamar $100 a wata tunda bashida kwarewar da za’a biyashi kudi sosai. Idan community managing ko moderation ne, dole ya mayarda hankalinsa a telegram da twitter. A telegram, ya shiga group na projects da yawa, ya fahimchi projects din sosai. Dazarar wani yayi tambaya ko neman karin bayanı a group din sai yayi sauri ya amsa masa. Da hakane har zai samu wasu projects din suyi noticing dinsa, suyi masa magana ta DM, su bashi aiki. Haka kuma ya kasance yana yawan halartar twitter space na projects din, sannan yana yin magana ta karin bayani ko nuna yanda project din yake burgeshi m. Hakama yana sawa ayi noticing din mutum a bashi aiki.

Kai rubutun yayi yawa, amma bayani shima da yawansa 😀. In Sha Allah community managing/moderation, content creation da sauransu suna chikin abubuwan da zamu koyar a SCTv HUB idan mun budeshi. Kafin nan, zaku iya amfani da wannan bayanin domin koyon wasu abubuwan a YouTube. Kuyi kokarin zama full time yan crypto, ba seasonal yan crypto ba.

Sunusi Danjuma Ali
YouTuber II Founder, SCTv Africa.

SCTv Africa HS

02 Dec, 06:26


SCTv Africa squad code na wave wallet wheel ayau shine 👇🏽

0ohvfr

SCTv Africa HS

01 Dec, 12:24


Holding a Crypto

Na zabi nayi wannan rubutunne domin kuskuren fahimta da naga mutanenmu suna yiwa holding a crypto. A yanzu da aka fara shiga bull run, akwai bukatar mutane su san ya ake holding da kuma kalar token daya kamata su saya domin holding. Dogaro da fahimtata, na raba holding zuwa kashi biyu (2).

Kashi na farko shine gajeren holding. Ma’ana, holding din da mutum zai na gajeren lokachi, kamar yan watanni kawai. Akwai token din da baka bukatar ka rikeshi na dogon zango kamar shekara daya zuwa sama, saboda trend tokens ne. Ma’ana, token din yayi kawai yabi. Misali ace ga wani sabon narrative (misali, AI tokens) da ake yayi a bullrun, saika nemi token da aka kirkirar

Token da ake saya domin gajeren holding sune wayanda akesa ran za’achi kasuwarsu a watse achikin wannan bull run din. Babu lissafin rikesu har bayan bull run. Shine yasa nace trend kawai suke bi. Tokens da ake musu gajeren holding ba’a cewa za’a rikesu zuwa wani kayyadadden lokachi, a’a ana cewa za’a rikesu ne zuwa wani farashi da akesa ran zasu kai. Atakaice dai, ana basu target price ne wanda dazarar sunkai ake watsar dasu ayi taking profit anemi wasu. Hakan na nufin ko yau mutum ya sayesu, gobe suka kai target price nashi zai sayar dasu ya nemi wasu.

Misali, ka sayi token mai suna $SDA yana farashin $1 da niyar yi masa gajeren holding. To zaka bashi target price ne wanda dazarar yakai wannan farashin zaka sayar dashi, koda kuwa achikin satın saka siyeshine. Zaka iya sayen token kace kana target 100X ne, don haka ko bayan awa daya da siyanshi yayi maka 100X zaka siyar ka nemi wani kuma.

Abubuwan da ake dubawa yayin yin fundamental na ire-iren wayannan tokens din sun hada tokenomics design (fair launch is very important), use case (trends is very important), nasarori da team na project sukayi abaya, da sauransu. Gajeren holding ana iya shigarsa da kudi masu yawa lokachi guda.

Rukuni na biyu sune tokens da akeyin holding na dogon zango. Wayannan tokens din ana sayensu da niyar holding na wasu shekaru masu zuwa. Kamar sayen token da tunanin holding dinsa na shekaru masu yawa. Ba’a duba trends a token da za’ayi masa dogon holding, domin trends a kasuwar crypto suna chanjawa lokachin bayan lokachi.

Token na dogon holding ana duba karfin use case dinsu (technology) da suke dashi ne. Don haka koda hankali bai kawo kan wannan technology din ba a yanzu, nan gaba hankali zai koma kansa. Don haka sai mutum yayi dabara yana sayen token din a hankali-ahankali.

Ire-iren tokens da akeyi musu dogon holding zakuga su kansu team na project din basu damu da hayaniyar bull run da ake chiki ba. Sunfi mayarda hankalinsu kan building na project dinsu kawai, saboda suma tunaninsu bana kusa bane. Irin wayannan tokens din ba’a fiya damuwa da duba tokenomics design dinsu ba sosai, abu mafi muhimmanchi shine ace maximum supply dinsu yayi daidai da total supply. Koda kuma ace 20% ne kawai circulation supply dinsu ba’a fiya damuwa ba.

Tokens da za’ayi musu dogon holding ba’a saka musu kudi masu nauyi lokachi guda, saboda ana sayensu ne ahankali-ahankali. Misali, mutum zai iya cewa zan dinga sayen wannan token din na $5 kowanne wata, ko kuma idan ma’aikachin albashine yasawa kansa ka’idar sayen token din na N5000 duk lokachin da akayi albashi yanda bazai takura ba.

Mafi yawan masu yiwa tokens dogon holding sunada wani plan ne da suke son chimma a rayuwarsu. Misali, wani yanada wani quduri da yake son chimma nanda shekaru biyar masu zuwa, saiya duba tokens da yake tunanin cewa sai a next bull run ne zasuyi yayi sosai. Saiya fara sayensu tun yanzu. Kamar yanda nace anfi duba tokens da suke da tech mai karfi akansu amatsayin use case. Allah yasa mu dace da dukkanin rahamarsa.

Sunusi Danjuma Ali
YouTuber II Founder, SCTv Africa.

SCTv Africa HS

01 Dec, 07:53


Yanda ake samun tickets da yanda ake amfani dasu a sabon tsarin wave wallet na meme wheel.

SCTv Africa squad code na yau shine 👇🏽

0kj1kg

SCTv Africa HS

30 Nov, 17:53


🐋 Wave Wallet Sun Kawo Tsarin Meme Wheel.

🐋 Tsarina na samun ticket da mutum zaiyi amfani dashi ya shiga wheel domin samun wave points ko kyautar meme token kamar WEWE da sauransu.

🐋 Yanda ake samun ticket din shine ta hanya uku.

🐬 Hanya ta farko shine ta squad code. Kullum suna saka code a squad, sai squad leader ya bawa members na squad dinsa. Idan suka sakayi amfani dashi zasu samu ticket daya. Squad code dinmu na yau shine 0viyj2, kuma In Sha Allah kullum zan dinga ajiye squad code dinmu anan Facebook da telegram channel dinmu.

🐬 Hanya ta biyu itace ta hanyar yin trading akan Wave wallet bangaren meme token. Duk trading na $1 mutum zai samu ticket 1, kuma ba’a yarda mutum ya samu samada ticket 10 ba a rana ta hanyar trading. Ma’ana daga tickets 10 an rufe a wannan ranar, sai kuma washegari.

🐬 Sannan ana samun tickets ta hanyar yin wasu tasks.

In Sha Allah gobe zanyi mana gajeren bidiyo domin nuna mana yanda ake samun ticket din, da yanda ake amfani dashi.

Wayanda basa chikin Wave Wallet squad dinmu, zan ajiye link dinsa a comment, idan basuda squad zasu iya shiga namu.

Link na SCTv Africa squad a Wave wallet 👇🏽

https://t.me/waveonsuibot/walletapp?startapp=3YMKAZ3j87RVdggaC7f9JttaJYpLZQUxGNRce25NgM5W3Za

Code na squad dinmu a yau shine 👇🏽

0viyj2

SCTv Africa HS

30 Nov, 14:47


Fair Launch Tokenomics

Fair launch tsarin tokenomics da ake sakin dukkan token da aka kirkira gaba daya a kasuwa. Ma’ana, a tsarin fair launch ba’a rage wani adadi na token da aka kirkira da niyar ajiyewa domin nan gaba adinga sakinsa a kasuwa ahankali-ahankali ko da kadan-kadan. A tsarin fair launch, adadin token da yake yawo a kasuwa, daidai yake da adadin token da aka kirkira gaba daya, kuma daidai yake da adadin token da za’a iya kirkira daga baya. Ma’ana, daga adadin da yake yawo a kasuwa, baza’a kara kirkira wani adadi ba na wannan token din koda guda dayane. A yaren crypto hakan na nufin 👇🏽

Circulation supply = Total supply = Maximum supply. Haka kuma 👇🏽

Market Cap (MC) = Fully Diluted Value (FDV)

Manyan investors na crypto sunfi son token din da yakeda tsarin fair launch. Domin basu da fargabar nan gaba za’a dinga kara yawan token din a kasuwa, wanda hakan zai hana farashinsa yin abin kirki. Hakane ma yasa manyan investors sukafi saka manyan kudadensu akan meme token, saboda meme token akafi sani da yin tsarin fair launch, ba’a fiya ganin hakan a wajen standard tokens ba. A mafi yawan lokachin, rashin tokenomics mai kyau shine yake hana wasu manyan tokens motsin kirki. Misali, mu dauki Worldcoin, Ton, da sauransu, ya kamata ace farashinsu ya wuce yanda yake a yanzu, amma saboda rashin tokenomics mai kyau sun kasa kaiwa farashin daya dace dasu.

A mafi yawan lokachi, token da akayi masa fair launch yana samun dumping ne na iya yan kwanaki, saboda kusan duk wayanda suke da niyar sayarwa zasu sayarne achikin yan kwanaki dayin launching, mafi yawansu ma suna yin dumping ne achikin 24 hours dayın launching. Hakane yake sawa manyan investors basa saka kudinsu akan token daya samu fair launch da wuri, sukan jira na yan kwanaki domin su tabbatar an kammala dukkan dumping da za’ayi. Daga nan saisu shiga.

Idan kanayin on-chain analysis na token da akayiwa fair launch, duk wallet din daka gani a wajen holders, zata iya sakin token din dake chikinta akasuwa aduk lokachin da mai ita yaga dama.

Saidai idan kana holding na token da yake da tsarin fair launch lallai ya kasance duk lokachin da farashin ya tashi sosai, to tabbas manyan investors sukan zare kudadensu daga kansa, kuma saboda girman kudaden süne yasa farashinsa yake yin dumping bayan ya tashi sosai. Wannan shine inda ake yin applying na sell high buy low strategy, dukda yake cewa zaiyi wahala ya koma kan farashin daka siyeshi. Kamar dai yanda ya faru akan Vista baya-bayan nan da farahinsa ya tashi daga $19 zuwa $65, sai kuma yayi dumping zuwa $37.

SCTv Africa HS

29 Nov, 15:00


Shekarar data gabata SCTv Africa YouTube channel tanada 13,000 subscribers. Yanzu kuma tanada 39,795 subscribers. Chikin ikon Allah mutane 26,795 ne sukayi subscribing na SCTv Africa YouTube channel achikin shekara daya.

Achikin kwanaki 28 da suka gabata mutane 14,884 ne sukayi subscribing SCTv Africa. Watakila hakan yanada alaqa da sabbin bidiyon Dex dana fara. Kuma hakan ya nuna yanda mutanenmu suke kokarin neman ilimin cryptocurrency. In Sha Allah SCTv Africa zata chigaba da kawo muku bidiyo masu ilimantarwa akan kasuwanchin cryptocurrency.

Shin zamu iya kai SCTv Africa YouTube channel 100,000 subscribers kafin karshen shekarar 2024? Eh zamu iya! Kowa ya bada gudummawarsa domin ganin mun chimma wannan gachi na 100,000 subscribers.

Gudummawar da zamu bayar shine wanda baiyi subscribing ba yayi, sannan muyi sharing wannan rubutun, kuma musa yan uwa da abokan arzuka suyi subscribing. Haka zalika muyi rubutu a pages dinmu domin jawo hankalin abokanmu na Facebook suma suyi.

Wannan shine solidarity da zaku yiwa tasharku ta SCTv Africa YouTube channel domin ganin ta hada 100,000 subscribers. Ga link na YouTube channel din 👇🏽

https://youtube.com/@sunusicryptotv

SCTv Africa HS

29 Nov, 08:51


Farashin Coin

Ba abin so ko birgewa bane token ya fara da babban farashi. Duk wani token da muke gani a yanzu ya girmama da karamin farashi ya fara. Shi token anfi so ya fara da karamin farashi, sai utility dinsa ya jagoranchi girmansa. Token din daya fara da babban farashi, karshen shine token da project din su ruguje, wato su mutu. Project da token dinsu tamkar ginine daga kasa ake faroshi, a hankali har agina sama. Shin ana fara gini ta sama?

Matsalar farko da token zai fuskanta idan ya fara da babban farashi shine dumping. Duk Wanda aka bawa token din saiya sayar dashi, tun daga kan team na project, VCs, community da sauransu duk sai sun sayarda tokens dinsu idan ya fara da babban farashi. Misali, token mai 100M supply saiya fara da farashin $15, kenan duk wanda aka bawa guda 100 zai samu $1500 kenan. Hakan zaisa yaji ya wadata da kudin ya sayar dashi, don haka zaiyi dumping yayı gaba.

Matsala ta biyu shine manyan traders da holders (investors) zasuji tsoron sayen token din saboda dalilai biyu. Na farko zasuji tsoron dumping, domin ko guda 100 trader ya saya akan $1500 da niyar trading, koya kasuwa tayi kasa sai yaga ba karamar asara zaiyi ba.

Na biyu kuma shine holders (investors) da suke harin token din da zaiyi musu Xs, zasuga wannan token din yayi musu girma saboda girman MC da FDV dinsa. Su holders sunfi son token mai karamin MC da potential, yanda zasu sayeshi saisu jirashi ya girma. Idan token mai 100M supply ya fara da farashin $15, zai kasance yanada $1.5B MC da FDV kenan. Hakan na nufin sai sabon kudi sun hau kansa FDV da MC dinsa sun koma $3B sannan token din yayi musu 1X, kuma samun wannan kudin akan token daya ba karamin aiki bane.

Sunusi Danjuma Ali
YouTuber II Founder, SCTv Africa

SCTv Africa HS

28 Nov, 08:30


Sell High , Buy Low Strategy

Wannan wani strategy ne da hodlers suke amfani dashi wani lokachin (bako yaushe ba). Yanda strategy din yake aiki shine idan mutum yana hodling wani coin ko token, aduk lokachin da farashin token din yayi pumping sosai, saiya sayar dashi, idan farashinsa ya sakko kasa kuma saiya kara saya. Kasancewar ka’idane a crypto (dama sauran harkokinmu na rayuwa) cewa duk abinda yayi sama dole ya sakko kasa, kamar yanda Bahaushe yake cewa “Duk nisan jifa, kasa zai dawo”.

Amfanin Sell High, Buy Low Strategy

⚡️Strategy din zai bawa mutum damar kara tara tokens din da yake hodling. Misali, mutum ya sayi token na $100 da niyar hodling akan farashin $1 duk guda daya, kenan dai ya sayi token din guda 100, sai farashin wannan token din yayi pumping zuwa $2, kenan kudin wannan token din guda 100 ya koma $200. Don haka saya sayarda token din domin yasan farashin token din sai yayi kasa, kamar $1.5. Idan farashin token din ya dawo $1.5 saiya mayarda kudinsa ($200) ya kara sayanshi. Hakan zai bashi damar mallakar wannan token din guda 133.3 maimakon guda 100 da yake dashi abaya.

⚡️Strategy din yakan bawa mutum damar chire wani kaso na kudin daya samu domin biyan bukatarsa. Idan mukayi amfani da misali na sama, mutum zai iya kara mayarda token dinsa guda 100 na baya, sai yayi amfani da sauran kudin wajen biyan bukatarsa na rayuwa.

Rashin Amfanin Sell High, Buy Low Strategy

⚡️ Wani lokachin zaka iya sayarda token din da tunanin ya gama tashi, kana jiran ya sakko saiya chigaba da tashi, kuma bazai taba dawowa farashin daya siyar ba. Hakan zaisa kodai ya haqura da hodling wannan token din, ko kuma ya sayi adadi kasa da wanda ya sayar abaya. Maganin wannan matsalar shine idan mutum ya tashi saiya sayarda rabi (50%) na token dinsa, yabar rabi (50%). Hikimar hakan shine, idan farashin token din yayi kasa, saiya mayarda kudin daya sayar ya kara saya. Idan kuma farashin token din yachi gaba da tashi, to dama bai fita ba gaba daya.

Masu yin wannan strategy sukanyi amfani da coingecko price alert wajen saita farashin da idan token din yakai, sai alarm ya buga. Wasu kuma sukanyi watsi da wannan strategy na sell high, buy low. Dalilinsu shine saboda suna ganin cewa wanda yakeyin hakan ba chikakken hodler bane, trader ne kawai.

Sunusi Danjuma Ali
YouTuber II Founder, SCTv Africa.

SCTv Africa HS

26 Nov, 14:31


UPDATE AKAN SIDEFANS

SCTv Africa HS

26 Nov, 14:31


UPDATE AKAN TOMATIR

SCTv Africa HS

26 Nov, 06:30


🏆 DEX TRADING (I) ya kasance gabatarwane akan Dex trading da rabe-rabensa.

🏆 DEX TRADING (II) munyi bayani akan tools (mobile apps) da ake amfani dasu domin yin Dex trading, harma muka daukosu.

🏆 DEX TRADING (III) mukayi bayanin yanda ake amfani da wasu daga chikin tools domin binchiko token mai kyau daya kamata ayi trading dinsa.

🏆 DEX TRADING (IV) mun nuna ya ake sayen tokens akan Dex.

🏆DEX TRADING (V) zamuyi shine akan yanda zamu samu perfect entry. Ma’ana, zamu mayarda hankaline akan yanda za’a gane cewa koya kamata a shiga token da akayi binchike akansa, ko kuma ajira tukunna.

Ma’ana dai, a DEX TRADING (V) zamu mayarda hankaline akan yanda za’ayi technical analysis akan token da akayi binchike akansa.

Technical analysis zai nuna maka cewa shin ya dace ka shiga token alokachin ko kuma ka jira na dan lokachi, ko kuma ka haqura da token din gaba daya, ka nemi wani.

Achikin bidiyon DEX TRADING (V) zamu nuna yanda ake sarrafa indicator na volume da kuma candlesticks (chart) domin samun perfect entry ma trade.

Kuyi following Abubakar Musa, kwararrene akan Dex trading. Yanayin rubuce-rubuce masu matukar muhimmachin akan dabarun Dex trading. Ku bibiyi rubuce-rubucensa na baya, zaku samu alfanu sosai achikinsa.

Akwai YouTube channel ta Abu Arfat Crypto Trader, shima yayi bidiyo masu matukar muhimmanchi akan Dex trading. Ga link na channel dinsa akasa 👇🏽

https://youtube.com/@abuarfat?si=UJZ2fcwO-SWsYU1X

SCTv Africa HS

25 Nov, 09:54


Ina Masu Verified Worldcoin? Wannan post din nakune!

🌎 DNA code shine 9797

🌎 Idan kun fara amsar ORB da ORO achikin Worldcoin app dinku, to lallai kuyi rijista da DNA.

🌎 Ku shiga App Store achikin Worldcoin dinku. Saiku shiga bangaren Finance, anan zakuga DNA. Saiku taba Get.

🌎 Ku budeshi (Open), sannan kuyi SignIn with World ID.

🌎 Wajen referral code kusa 9797.

🌎 Ku karasa verification din.

🌎 Daga nan kuma sai kuyi rijista ta hanyar amfani da World ID dinku.

🌎 Shikenan! Kun kammala, sai kuma ku jira update.

SCTv Africa HS

24 Nov, 20:44


Alhamdulillah. Bidiyon DEX TRADING (IV) ya hau YouTube.

https://youtu.be/zmp4t__Sb50

SCTv Africa HS

22 Nov, 14:38


Tomatir updates 🔥:
Tomatir sun tabbatar da za suyi listing 20 ga watan december

SCTv Africa HS

21 Nov, 07:00


Sidekick update 🔥:
Ana daf da gama sidekick dan haka in ma baka karasa wani abun ba kayi kokarin yin haka

SCTv Africa HS

20 Nov, 22:11


Jerin bidiyon koyarda Dex Trading da mukayi 👇

✨️ DEX TRADING (I)

https://youtu.be/x0mbE2tWT7U

✨️ DEX TRADING (II)

https://youtu.be/UnM-mBIBx3Y

✨️ DEX TRADING (III)

https://youtu.be/dl-X97k9xsM

✨️ DEX TRADING (IV)

In Sha Allah yana hanya...

SCTv Africa HS

20 Nov, 00:04


TADA NEW UPDATE

Token da zasu bamu a yanzu haka an samar dashi akan Ton Blockchain

Suka ƙara da cewa zasuyi Distribution ranar 21 ga November wato Alhamis kenan, Allah yasa mu zama Eligible Amin

WAGMI.

SCTv Africa HS

19 Nov, 21:11


Alhamdulillah. Bidiyon DEX TRADING (III) ya hau YouTube.

https://youtu.be/dl-X97k9xsM

SCTv Africa HS

18 Nov, 10:42


WEWE sunyi snapshot yau da misalin 4am, gobe kuma da misalin 12pm zasu bada damar claiming da trading dinsa.

Atakaice dai launching sai gobe 12pm.

SCTv Africa HS

18 Nov, 08:36


Wave wallet: SCTv Africa squad code na claiming 50 WEWE shine 👉🏼 08lcrn

Yau da misalin karfe 12pm za’ayi launching na WEWE. Muna fata ya fito da daraja In Sha Allah.

SCTv Africa HS

17 Nov, 07:04


Wave Wallet: Code na SCTv Africa squad domin claiming na 50 WEWE shine 👇🏽

0ms55e

SCTv Africa HS

16 Nov, 11:39


Dukda cewa zanyi bayaninsu achikin bidiyon Dex, bari na danyi mana bayanin ma’anar wayannan crypto terminologies din.

Rug Pull: Shine devs na token su rike kaso mai yawa na token din a wallet(s) dinsu, sai mutane da yawa sun saka kudinsu, sai devs din su sayarda dukkan token dake wallet(s) dinsu, wato dai suyi dumping. Hakan kuma sai yasa farashin token din yayi mummunar faduwa lokachi guda. İrin hakane zamuga lokachi guda farashin token yayi -90%. Misali farashin token yayi mummunan karyewa daga $1 zuwa $0.1 ko $0.001, hakan yake sawa mutum ya sayı token na $100 amma lokachi guda yaga ta koma $2 😭.

Honey Pot: Shine devs suyi coding token dinsu akan cewa saidai a saya amma ba damar sayarwa. Nasan maybe kun taba samun hakan, wato kun sayi token amma kuma ba damar sayarwa. Wani lokachin zakuga kudin token din ya tashi sosai amma ba damar siyarwa. Ka sayi token na $100 ta koma $10,000 amma ba damar sayarwa, saidai kallo 😭.

Removing Liquidity: Shine ka sayi token, sannan zaka iya sayarwa amma lokachi guda kawai sai devs su zare masa liquidity. Hakan zaisa daga baya bazaka iya sayar dashi ba duk ribar daya ba, ya zama hoto kawai a wallet dinka. Bari muyi amfani da policy din tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari as case study. Nasan kun tun lokachin da Buhari ya ware tsofaffin kudaden N1000 da N500 akan cewa sun daina aiki, hakan na nufin ya zare musu liquidity 😃. Hakan na nufin abaya sunada daraja amma yanzu ba damar amfana dasu wajen siyayya.

Shakeout: Strategy ne da project/token suke amfani dashi wajen korar paperhands. Paperhands ko kuma muce jeeters sune mutane da basa iya rike token na tsawon lokachi, wato da token yayi kasa kadan saisu sayar, ko kuma dazarar ya tashi saisu sayar. Paperhands suna mayarda project baya sosai, su hanashi motsin kirki. Don haka sai project su koresu ta hanyar yin amfani da shakeout strategy. Shakeout shine project suna dumping din token dinsu dagangan domin su kori paperhands. Misali, paperhands sun sayı token yanada $2M market cap (MC). Sai project su dinga dumping din token dinsu farashinsa yanayin kasa, MC tana yin kasa. Misali, suyi dumping project ahankali-ahankali, kamar daga $2M MC zuwa $1.8M MC, zuwa $1.5M MC, zuwa $1M MC. Kai zasu iyayin dumping har zuwa $500k MC domin su kori paperhands. Hikimar yin hakan shine sawa paperhands tsoro da fargaba a kowacce gaba ana korarsu. Misali, idan token ya koma $1.8M MC wasu daga chikin paperhands zasu sayar, wasu zasu sayar idan ya koma $1.5M MC. Haka dai abin zaichi gaba da kasancewa, token yana yin kasa paperhands suna sayarwa. Idan project suka gama yin kasa da token dinsu kuma saisu hanashi tashi kuma su hanashi sauka na tsawon lokachi, wato dai token din ya fara consolidation. Hakan zaisa sauran paperhands yan dagiya su sayar tunda farashin token ya tsaya waje daya. Sai rana daya kawai project suyi pumping token dinsu ya koma $2M MC dinsa, bayan sun tabbatar saura real holders na token dinsu.

Wannan karatune mai fadi da kuma muhimmanchi, zanyi mana bayaninsa a chikin bidiyon Dex da nakeyi. Musamman yanda mutum zai nemi tokens masu saukin MC da suke consolidation ya shiga domin holding.

SCTv Africa HS

16 Nov, 07:32


Wave Wallet: Code na SCTv Africa squad domin claiming na 50 WEWE shine 👉🏼 0atqxa

Grass: Jiya aka fara epoch 2 na Grass Protocol.

SCTv Africa HS

15 Nov, 10:09


Wave Wallet: SCTv Africa squad code ma claiming WEWE shine 👉🏼 08jg5l.

Yau saura kwana uku ayi launching WEWE. Guda nawa kuka tara?

#RemainFocused

SCTv Africa HS

14 Nov, 20:37


Alhamdulillah. Na dora bidiyon TRADING (II)

https://youtu.be/UnM-mBIBx3Y

SCTv Africa HS

13 Nov, 09:08


Wave wallet, SCTv Africa squad WEWE code 👇🏽

08cfgk

SCTv Africa HS

12 Nov, 19:17


Alhamdulillah. Bidiyon farko na Dex trading ya hau YouTube.

https://youtu.be/x0mbE2tWT7U

SCTv Africa HS

12 Nov, 07:16


🐬 SCTv Africa squad code na Wave wallet na yau shine 0sq3qt

Dana fara sayen ORB na chikin Worldcoin agurin mutane akan $10, lokachin kuma yana nuna $5 duk 1000 ORB. Na sayi guda 43,750 akan $435.5. Yau kuma na sayi 17,330 ORB akan $18.93 kacal 😀. Kenan da waccan $435.5 din zan samu akalla samada 400,000 ORB.

Wani strategy da nake amfani dashi wajen siyan coins na holding shine, ina duba sabbin blockchains masu kyau da karfin team, blockchain din da suka nuna alamar sunada karfin da za’ayi gogayya dasu. Saina dinga sayen tokens dinsu, na rikesu da tunanin dogon zango (holding), da kuma kyakykyawan zaton cewa aduk lokachin da blockchain din ya fara tashe, wayannan tokens din zasu bishi a tafi tare.

Saidai nakanyi takatsantsan wajen sayen tokens din. Ina duba tokens din da suka samu goyon bayan blockchain kai tsaye tun a yanzu, ko kuma ya kasance tokens din na masu blockchain dinne. Misali, Worldchain network na Worldcoin ne, kuma dai munsan karfin team, gogewa, da karfin liquidity na masu Worldcoin. Da kansu suka kirkiri ORB da ORO tokens, don haka a kautata zaton da nakeyi na karfin da worldchain zaiyi anan gaba, dole zai tafi da ORO da ORB tokens. Kamar hakane a yanzu, aduk chikin layer 2 blockchains nake ganin babu wanda ya nuna karfinsa kamar Base blockchain, don haka shima saina fara laluban tokens achikinsa. Haka zalika SUI blockchain shima. Duk wayannan blockchains din akwai kyakykyawan zaton zasuyi tashe anan gaba.

Saidai mafi yawan ire-iren wayannan tokens din na sabbin blockchains ana samunsu ne akan Dex. In Sha Allah duk zan nuna mana yanda ake sayen tokens akansu, dama sauran blockchains da za’a kirkira agaba.

SCTv Africa HS

11 Nov, 10:41


🦋 MARA Wallet sun dawo, amma sun chanja suna zuwa JARA Wallet.

🦋 Shekaru biyu da suka gabata munyi aiki da Mara wallet, kuma Alhamdulillah mutane da dama sun samu alkhairi da Mara wallet. Yanzuma Jara sun kawo wani tsari da mutane zasu samu alkhairi dasu. Bayan shafe tsawon lokachi ba muji duriyarsu ba, yanzu Mara wallet sun dawo, saidai sun chanja suna zuwa Jara wallet.

🦋 Ba kamar yanda suka faro Mara wallet ba, Jara wallet decentralized wallet ce (EVM). Ma’ana, dukda ana amfani da email wajen yin rijista, Jara wallet bata bukatar yin KYC, recovery phrase da private keys kawai suke bayarwa wanda mutum zai adanasu.

Yanda Ake Rijista da Jara Wallet

Ku taba link dake kasa. Idan ya bude muku, kuyi signup ta hanyar shigar da mail dinsu tareda kirkirar password. Zasu tura muku da sako ta Mail dinku, a mafi yawan lokachi sakon nasu yana tsayawane a spam folder. Don haka saiku shiga spam folder dinku, sannan ku taba Looks Safe domin dawo da sakon zuwa primary folder dinku. Daga nan saiku taba CONFIRM SIGNUP.

https://app.getjara.xyz/join?refCode=DL93Z1O4

Ku dauko Jara wallet application a PlayStore ko AppStore, sannan kuyi Signin da bayanan da kukayi rijista.

Daga nan saiku taba Create a new wallet. Zasu baku secret recovery phrase, ku tabbatar kun rubutashi kuma kun adanashi. Sannan zasu baku private keys, suma ku tabbatar kun adasu.

Shikenan! Kun kammala bude Jara wallet.

Yanda Zaku Tara Jara Points

💥 Daga chan kasan wallet dinku, akwai icons guda 4, na karshen mai tambarin Jara shine zaku shiga. A karkashinsa akwai abubuwa da yawa, kamar Games, Launchpad, Rapples da kuma Rewards.

💥 A karkashin na farkon wato Games, akwai LionTap. Idan kuka shiga zakuyi tapping dinsa na yan sakwanni, yana chika sai kuyi claiming na Jara Points dinku. Sai kuma bayan awanni biyu zaku kara dawowa kuyi tapping. Da hakane zaku tara Jara points.

SCTv Africa HS

11 Nov, 06:52


🐋 SCTv Africa squad code na claiming 50 WEWE a Wave wallet shine 0pc4ig

🐋 SUI yana farashin $3.1.

🐋 SUI yana kara samun karbuwa sosai a duniyar blockchain. Haka zalika team dinsu suna kokari sosai wajen ganin sun chimma nasara. Saidai har yanzu manyan kudade basu fara hawa kan tokens da aka kirkira akansa SUI network ba, kamar yanda muke gani suna hawa kan abokin takararsa, wato Solana.

🐋 A yanzu, akwai potential projects da kuma memes tokens masu kyau akan SUI network, saidai rashin fara hawan manyan kudade kan SUI yasa basu fara motsin azo agani ba, kamar yanda muke gani akan tokens da projects nakan Solana.

🐋 Manyan masanan blockchain da crypto Suna ganin nan gaba (watakila achikin bull run din nan), SUI blockchain zai kere (out perform) Solana. Idan hakan ta tabbata, to tabbas suma tokens na kan SUI zasuyi performing sosai. Don haka yanzune ya kamata mu fara exploring tokens nakan SUI blockchain. Domin idan SUI tokens suka fara performing ya kasance ba’a barmu abaya ba In Sha Allah.

🐋 Wannan ba financial advice bane, ra’ayine na kashin kaina. Shi kuwa ra’ayi kowa da nashi, idan ra’ayina baizo daidai da naka ba, yi wurgi da nawa ka dauki naka!

SCTv Africa HS

10 Nov, 07:35


Assalamu Alaykum.

SCTv Africa Squad Code na claiming 50 WEWE a Wave Wallet 👇🏽

0v1xzs

SCTv Africa HS

09 Nov, 10:15


TADA MINI Update 🔥:
Tada sun ware tabbatar da 21 ga watan zasu fara turawa mutanen rewards din su

SCTv Africa HS

09 Nov, 04:56


Assalamu Alaykum.

SCTv Africa Squad Code na claiming 50 WEWE a Wave Wallet 👇🏽

08cvfu

SCTv Africa HS

08 Nov, 06:01


Assalamu Alaykum.

SCTv Africa Squad Code na claiming WEWE a Wave Wallet 👇

0a36eq

Masu tambayar link na SCTv Africa squad a Wave wallet 👇

https://t.me/waveonsuibot/walletapp?startapp=3YMKAZ3j87RVdggaC7f9JttaJYpLZQUxGNRce25NgM5W3Za

SCTv Africa HS

07 Nov, 15:53


🌑 MoonCoin Sun Saki Tokenomics 🌑

🌑 Zamu iya cewa yau aka kammala mining na MoonCoin. Gaba daya wata biyu akayi ana mining dinsa (8 weeks).

🌑 Sunyi snapshot yau da misalin 11am. Sunce gaba daya users dinsu mutane 400k, achikinsu mutane 7,203 ne suka sayi NFT dinsu. Rashin sayen NFT ba yana nufin mutum bazai samu kasonshi ba, a'a saidai wayanda suka saya zasufi samun kaso mai tsoka.

🌑 Gobe da misalin 10am kowa zai duba adadin daya samu, kuma har ya iya claiming. Sun fitar da checker (zan sashi a comment), wanda ta chikinsa ne kowa zaiga abin daya samu, kuma yayi claiming a gobe.

🌑 Ga bayanin tokenomics dinsu

✨️ Sunan Token: MoonCoin

✨️ Token Ticker: MOON

✨️ Blockchain: Eclipse

✨️ Total Supply: 108 Billion

✨️ Adadin da Zasu Rabawa Miners: 86.4 Billion

✨️ Liquidity: 21.6 Billion

✌️ Kenan dai zasu rabawa miners 80% na token din (MOON), sannan sauran 20% din sun barshi domin liquidity.

✌️ Basu fadi lokachin da za'a fara trading dinsa ba, amma sunce chikin awa 24 masu zuwa zasu fitar da Contract Address (CA) dinsa, da kuma Liquidity Pool (LP). Hakan na nufin za'a iya fara swapping/trading dinsa chikin 24 hours.

Ga checker dinsu 👇
https://airdrop.mooncoin.co

SCTv Africa HS

07 Nov, 13:15


🐋 Wave wallet suna rabawa members na squads kyautar WEWE kullum. WEWE meme token ne da Wave wallet zasuyi launching dinsa nan da kwanaki 11. WEWE ya samu goyon bayan Wave wallet da SUI blockchain, kuma dukkansa zasu rabawa masu mining na Wave ne. Don haka zai iya kasancewa meme token mafi girma akan SUI blockchain.

🐋 Domin claiming WEWE kullum, members na squad suna bukatar daily code da za'a saka a squad din. Wanda ya bude squad dinne kadai yaje iya ganin code din, shi kuma saiya bawa members na squad dinsa. Don haka kullum zan dinga saka code na SCTv Africa Squad anan Facebook da kuma telegram channel dinmu.

🐋 Code na yau shine 050xlc. Idan kuka saka zakuyi claiming 50 WEWE.

🐋 Idan kun shiga Wave wallet dinku, saiku shiga wajen Wave Pump. A wajen tasks zakuga wanda zaku shiga kusa code din domin yin claiming.

🐋 Wayanda basa chikin squad din, ga link dinsa

https://t.me/waveonsuibot/walletapp?startapp=3YMKAZ3j87RVdggaC7f9JttaJYpLZQUxGNRce25NgM44521

SCTv Africa HS

06 Nov, 11:49


Donald yayi nasara 🔥

SCTv Africa HS

03 Nov, 09:43


Pavel ya sanar cewa a cikin satin da zamu shiga zasu yi kara features da yawa a tele.gram mini apps, hakan na nufin project yanzu suna da damar dora abubuwa da yawa a kan apps din su na kan tele.gram wannan ba karamin cigaba zai kara wa ecosystem na tele.gram ba.
Ga hotunan abubuwan da za a kara a kasa nan

SCTv Africa HS

02 Nov, 18:50


Jiya SCTv HUB munyi manyan baki da suka kawo mana ziyarar sada zumunchi tun daga garin Abuja, wato Sir Abubakar Tanko da Malam Aliyu Adamu. Mun tattauna abubuwa masu matukar muhimmanchi, sannan munyi Facebook live wanda achikinsa Sir Abubakar Tanko ya bawa mutane hudu da suka halarta kyautar shiga VIP group dinsa (2 maza 2 mata). Malam Aliyu kuma yayi giveaway na $10 zuwa ga mutane 10+ ($100+).

A madadin team na SCTv Africa muna matukar godiya, da fatan kun koma gida chikin koshin. lafiya.

Sadeeq Yusuf Gwagwarwa
Kabiru Hussaini
Sunusi Danjuma Ali

SCTv Africa HS

31 Oct, 17:04


Laifin dadi… 😭
An kammalla komai na Tomatir sun yi snapshot.
Kamar yadda suka sanar a baya yanzu haka sun shiga maintenance dan haka ba abunda zai cigaba da aiki.

Kowa ya jira yaga mai zai samu nan da 2 ga wata mai kamawa.

Allah yasa muji Alkhairi 🤲

SCTv Africa HS

31 Oct, 16:55


Paws Airdrop update 🔥:
An saka sabon mission a Paws koya yaje yayi.

Ga wanda kuma ba suyi ba:

Domin yin register: https://t.me/PAWSOG_bot/PAWS?startapp=zP4FFxnt

Allah ya bamu sa’a 🤲

SCTv Africa HS

31 Oct, 05:31


🧬 Asset Chain Zasu Debi Creator Key Opinion Leader (KOL).

🔗 Asset Chain blockchain zasu debi KOLs wayanda zasuna rubuce-rubuce ko bidiyo akan manufofin blockchain dinsu da tsare-tsarensu, dama sauran abubuwan da suka danganchi blockchain din.

🔗 Su Waye Zasu Iya Nema?
Mutanen da suke da followers a social media, kamar telegram channel ko group, twitter, facebook, discord, instagram, tiktok, da sauransu. Sun rarraba mutanen da zasu iya applying na zama KOL zuwa rukuni-rukuni gwargwadon yawan followers kamar haka:

Nano KOLs: 1k-5k followers.
Micro KOLs: 5k-50k followers.
Mid-Tier KOLs: 50k-100k followers.
Macro KOLs: 100k-500k followers.
Mega KOLs: 500k followers zuwa sama.

Ribar Dake Chikin Zama KOL
💫 Zasu biya KOLs da coin dinsu a lokachin da zasuyi launching. Biyan zai banbanta daga rukuni zuwa rukuni (Nano zuwa Mega).
💫 Damar hada yan kanamun taruka (meetups) da shirya AMA (Ask Me Anything).
💫 Akwai group na KOLs da zai baku damar tattaunawa da team na Asset Chain.
💫 Damar samun riguna da sauran merch na Asset Chain project.
💫 da sauran ribar daka iya biyo baya.

Ku sani cewa wannan ba aikin albashi bane da za’a dinga biyanku duk wata, saidai kasancewar yanzu project din yake ginuwa, zai kasance kenan project din yana girma, kuna kara samun damarmaki achikinsa.

Domin samun chikakken bayanı akan tsarin KOL dama yanda zakuyi applying ku karanta chikakken bayanın 👇🏽

https://assetchain.substack.com/p/apply-to-asset-chain-creator-kol

SCTv Africa HS

30 Oct, 11:45


𝐃𝐮𝐤𝐚 𝐀𝐛𝐮𝐛𝐮𝐰𝐚𝐧 𝐝𝐚 𝐲𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐭𝐚 𝐤𝐚 𝐬𝐚𝐧𝐢 𝐠𝐚𝐦𝐞 𝐝𝐚 𝐭𝐨𝐦𝐚𝐭𝐢𝐫 𝐲𝐚𝐮 🔥:

▪️Na farko tomatir sun tabbatar bawa community kaso 80% cikin dari da duka tumatir wannan nasara ce babba.

▪️Na biyu za a gama komai na tomatir karfe 12 na daren 31 ga wantan ma’ana ana shiga November an gama tomatir, shiyasa duk abunda za kayi kayi kokari ka gama shi a watan nan.

▪️ Na uku Dan su tabbatar kowa ya samu abunda ya dace ana gama zasu tafi maintenance na tsawon awa 24, idan suka tafi ba abunda zai ke aiki in ka hau dan haka kar ka shiga damuwa dan ka hau kaga komai yaki yi.

▪️Na hudu a lura komai da ka san ana yi a da idan aka shiga maintenance din nan ya dena aiki ko kayi a banza, irin su saka ton ko siyan star ko yin combo koma dai menene, to a lokacin va zai yi anfani ba.

▪️Abu na karshe kowa zai ga adadin balance din abunda ya samu ranan 2 ga watan November a lokacin sun gama maintenance kenan.

Sannan sun kara da cewa za a samu alkahiri sosai da noman tomatir, sannan wanda suka kai matakin Gold zuwa sama sannan da wanda suka mallaki medal din su akwai tagomashi da take jiran su.

An gaishe ku manoman tomatir 😅
Mu hadu ranar girbi!

✍️Sadeeq Yusuf Gwagwarwa