ABINDA NA FAHIMTA DA WANNAN TAX BILL DIN
Wannan Tax reform bill din zaiyi affecting din arewa sosai, amma zaisa states datawa su qara zage damtse gurin niman yadda zasuyi competing wajen niman hanyar samun kudin shiga.
Ga bayanin yadda abin yake a yadda na fahimceshi.
A tsarin kudin shigar kowani state, insuka tattara, suna dauka ne, duk wata sukai Abuja gurin FIRS( Federal Inland Revenue Service), a nan ake daukan wannan revenue din da akai generating na duka states a wannan watan, sai kasafashi wa kowani state.
Ga yadda kasafin yake yanzu(kafin tsarin bill din da shugaban qasa ya kawo) : Misali , kudin da aka tattara na wannan watan daga kowani state, harda Abuja 100B naira ne.
Ga formula na raba kudin:
1. Federal government: 15%
2. State government: 50%
3. Local government: 35%
Federal government: Wannan kudin ake amfani dashi akeyiwa qasa baki daya aiki
State government: Wannan kudin ake bawa gwamnoni suyi amfani dashi wajen gina state dinsu, ga yadda ake kasa 50% din wa duka state din nigeria.
1. Equality : 50%, ma'anar shi equality dinnan shine, kamar yadda mukai misali da 100B naira kudin da aka tattara daga states, 50B naira da aka ware na state government, 25B naira shine na equality, shikuma abinda ake nifi da tsarin equality shine, babba koh qaramin state, ko naira biyar suka kawo a wannan watan, duka kudi daya za'a basu cikin wannan 25B din da kowani state, koda kuwa babban state ta kawo 50B naira ne, kaga wannan yasa states din da suke qananu kuma koda kuwa basa generating din wani kudin kirki, zasu iya dinga biyan ma'aikata. Wannan tsarin yana taimakawa qananun state wanda basa samun kudin shiga sosai, kafin har Allah yasa su fara samun kudin shigansu, sai dai a gani na yasa state governors dayawa sun danyi lalaci, basuyi amfani da wannann daman dakyau ba.
2. Population: 30%, Ma'anar shi kuma population yana nufin, cikin wannan 50B naira na state government, za'a ware 15B naira, a rabawa state according to population din wannan state din, hakan na nufin, idan state dinka sunad mutane 100, wasu state din sunada mutane 1k, toh masu 1k zasufi yawa akan masu 100. Wannan shima tsarine mai kyau domin taimakawa state masu population dayawa, kafin Allah yasa su niman hanyar amfani da wannan population din su fara maidashi hanyar kudin shiga wa state government, har yakaiga federal government. Wannan abune dayake taimakawa arewa sosai, amma wasu governors din basuyi amfani da wannan daman dakyau ba.
3. Derivative: 20%, Shikuma ma'nara derivative shine, har ila yau, cikin wannan 50B naira na state government, za'a ware 10B naira, a rabawa kowani state according to girman abinda ta kawo na kudin shiganta, misali Kano ta kawo 2B naira, lagos ta kawo 5B naira, toh kaga dole lagos tafi kano da 150% , matsalar shine states din arewa dayawa basu generating kudi wa qasa sosai, domin lagos kawai, tana generating kudin da yakai sama da 55% na duka kudin da Nigeria take generating, kano kuwa tafi kowani state a arewa nesa ba kusa ba, amma a haka, dukda lagos tafi generating kudin dayawa, kano ce ta kusan 5 inban mantaba.
A taqaice ma'anar tsarin derivative shine, iya aikinka iya samunka, tunda lagos kawai tana generating kusan 55%, hakan na nufin zata dauki 5.5B cikin 10B naira din kenan, sauran a rabawa state 35, da Abuja 36 kenan. Kaga wasu states din bai wuce su tashi da 100M kenan ba, inma yakai kenan.
Tunda amfahimce yadda kasafin yake tsakanin Derivative, Equality da Population .
Yanzu bari kuga yadda aka tsara bill din wannan karan.
1. Federal government: 10%
2. State government: 55%
3. Local government: 35%
Ga kuma yadda aka kasafa na State government a bill din, kaga wannan karan maimakon 50B naira na state government, yanzu ya koma 55B naira, ancire 5B daga Federal kenan:
1. Population: 20%, inkun karanta dakyau, bangaren population yana daukan 30%(kwatan kwacin 15B naira, a 50B naira kenan), yanzu a bill din, zai tashi da 20%( kwatan kwacin 11B naira kenan, a 55B naira), kaga ansamu ragin 4B naira, wannan karan duk yawanku, an zabge muku sosai, dama farkon masu yawa daga kano na farko,