BINTUS-SUNNAH @bintussunnah Channel on Telegram

BINTUS-SUNNAH

@bintussunnah


Domin Faɗakarwa da Tunatarwa Zuwa Ga Al'ummah Ta Fannoni Daban-Daban.

TELEGRAM:
https://t.me/BINTUSSUNNAH

FACEBOOK:
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube:
https://youtube.com/channe

WHATSAPP:
http://api.whatsapp.com/send?phone=+2349030947171

BINTUS-SUNNAH (Hausa)

BINTUS-SUNNAH ta Bincike da Sunnah a Hausa ita ce wani kamfanin faɗin gaskiya a cikin al'umma. Kanun BINTUS-SUNNAH shine domin faɗakarwa da tunatarwa zuwa ga al'umma ta fannoni daban-daban a cikin Hausa. Kanun an samu a kan Telegram daga shafukan sada zumunta na BINTUSSUNNAH. Komai na Facebook da kuma Bayananmu a YouTube yayin da kowane abu ya zama watsi da wannan kanun. Zuwa ga duk wanda ke so ya samu ɗaukar hankali da kashi na addini, BINTUS-SUNNAH shi ne lokacin da zasu zama lokacin zama. Domin kada ka gamsu da wannan karin watsi, ziyarci shafukanmu a WhatsApp domin sake jefa muku duk abubuwa da suka faru a kanun. Ziyarci hanyoyinmu a Facebook, amma domin samun bayananmu More kai ziyarci YouTube. BINTUS-SUNNAH, yanayin yana da mu a lokacin da kowace irin kaya ya sha biyan bukatarmu a addini da kuma sharri. Ziyarci shafukanmu yayin da kuna da kama da ra'ayoyinmu, domin amfaninmu shine domin gamsu da hankalinka a kan karatunka. Sani da abin da ke cikin wannan kanun, kada ka suka hana da wannan karin zuwa. Sannan ka ɓoye shafukanka ta WhatsApp don sake samun zuwa da duk abin da suke faru a cikin karatunka. BINTUS-SUNNAH, lokacin da zamu mutu a jiki, to ina zamu mutu a lokacin? goyon bayaninmu ne a haka za mu mutu, kuma an sa ka dawo muku. Ziyarci shafukanmu a WhatsApp don samun zuwa da duk abin da suke faru a karatunka. BINTUS-SUNNAH, hango da waɗanda suna ɗaukar hankali da kashi a addini, da kuma wadanda suka tashi da wadannan abubuwa, kwatantawa. BINTUS-SUNNAH, 'ya'yayen sunna'yar wannan kasashe suna damar faɗin gaskiya a cikin al'umma ta fannoni daban-daban. Zuwa ga duk wanda ke so ya kula da wannan karin abu, kullum ya kula ta a kasa. BINTUS-SUNNAH, tsarinmu shi ne a haka za mu cire wadannan hankalai da tunatarwa a karkashin al'umma, domin a cire wadannan hankalai, zamu iya kai ga addinanmu ya zo da ƙarƙashinta. Ziyarci shafukanmu a WhatsApp don kai ga duk abin da zai zo da ƙarƙashinmu a gida. BINTUS-SUNNAH, abin da ke cikinmu ita ce faɗakarwa da tunatarwa zuwa ga al'umma ta yanayin yana. Adireshinmu a WhatsApp, Facebook da YouTube, daga nan zamu iya minin kai ga duk abin da zai zo daga cikin wadanda suka ɗauka hankali da kashi a addini.

BINTUS-SUNNAH

22 Jan, 10:19


HUKUNCE HUKUNCEN RUƘIYYAH A SHARI'AH //07

(Daga fatawoyin manyan Malamai daban-daban)

Wuraren da ake samun Shaiɗanu da Aljanu!

Daga cikin wuraren da ake samun Aljanu da shaiɗanu akwai: wajen kiwon raƙuma, wajen bola da datti, da gidajen dake da hotuna a ciki, hakanan shaiɗan yana zuwa wajen ƙulla ciniki, Ana samun su ramukan dake da duwatsu, shaiɗan yana bacci kan karan hancin ɗan Adam, ana samun su lokacin shigar Maghrib ko kusan lokacin, Ana samun su a maƙabartu, kasuwanni, Teku, gidaje da filayen da babu mutane a wajan, da wajen bahaya da bayan gida, da wajen dake tsakanin rana da inuwa.

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

BINTUS-SUNNAH

21 Jan, 09:57


21/RAJAB/1446H
21/JANUARY/2025

ADDU’AR YAU TALATA:
Ya ALLAH ka sanya albarka cikin rabonmu, kada ka sanya mana hassada a rabon wani.

HADISIN YAU TALATA:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Abinda ya same ka to ba zai kuɓuce maka ba, kuma abinda ya kuɓuce maka to ba zai same ka ba.” [Sahihu jami'us Sageer: 5244]
.
Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube
https://youtube.com/channel/UCG_W7_7gQdibxDgvhQdIEyQ

BINTUS-SUNNAH

20 Jan, 13:08


20/RAJAB/1446H
20/JANUARY/2025

ADDU’AR YAU LITININ:
Ya ALLAH ka tabbatar damu akan daidai kuma kayi mana jagora a dukkan al'amuranmu.

HADISIN YAU LITININ:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Duk wanda yaso duniyarsa (Sosai) To zai cutar da lahirarsa, kuma wanda yaso lahirarsa (Sosai) To zai cutar da duniyarsa.” [Silsilatus sahiha: 3287]
.
Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube
https://youtube.com/channel/UCG_W7_7gQdibxDgvhQdIEyQ

BINTUS-SUNNAH

19 Jan, 09:38


19/RAJAB/1446H
19/JANUARY/2025

ADDU’AR YAU LAHADI:
Ya ALLAH kada ka sanya mu cikin waɗanda za ka sauƙe saboda rahamarKa, ka sanya mu cikin waɗanda za ka ɗaukaka saboda rahamarKa.

HADISIN YAU LAHADI:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Mizani yana Hannun (ALLAH) mai Rahama, Shi yake ɗaga wasu jama'a kuma Yake sauƙe wasu.” [Sahihul Jamii 673]
.
Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube
https://youtube.com/channel/UCG_W7_7gQdibxDgvhQdIEyQ

BINTUS-SUNNAH

18 Jan, 22:29


QUR'AN 🤍

BINTUS-SUNNAH

18 Jan, 17:30


HARAMUN NE YAƊA ƁARNA A BAYAN ƘASA!

Haƙiƙa ana cutar da bayin ALLAH musamman a ƙafafen sada zumunta wanda wasu suke yaɗa ɓarna don ra'ayi da son zuciya da rashin kunya, yayin da wasu kuma suke yaɗa ɓarna don ƙoƙarin wa'azantarwa ko Faɗakarwa ko tunatarwa wanda hakan haramun ne. Babu laifi a wa'azantar a tunatar a Faɗakar amma me yasa baza a bi hanyar usulubin mai kyau ba, menene sai kawo video ko audio ko picture ko link na wannan ɓarnar?

A cikin Alƙur'ani Maigirma ALLAH (ﷻ) Ya ce:

وَلَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بَعۡدَ إِصۡلَٰحِهَا وَٱدۡعُوهُ خَوۡفٗا وَطَمَعًاۚ إِنَّ رَحۡمَتَ ٱللَّهِ قَرِيبٞ مِّنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ٦٥۝

Ma'ana: “Kuma kada ku yi ɓarna a bayan ƙasa bayan gyara ta, kuma ku bauta masa kuna masu tsoro da kwaɗayi. Lalle rahamar ALLAH a kusa take da masu kyautatawa.” [A'araf: 56]

“Kada ku ɓata ƙasa da saɓo bayan an gyarata da yiwa ALLAH biyayya, domin saɓo yana lalata ɗabi'u da ayyyuka da arzkiƙi.” [ Tafseer Assi'idy]

A ƙarƙashin wannan Ayar Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo (Hafizahullah) Ya ce: A wannan ayar ALLAH (ﷻ) Ya yi kashedi game da yaɗa ɓarna a bayan ƙasa bayan gyara ta, su kuma ji tsoron fushinsa da uƙubarsa, tare da kwaɗayin samun yardarsa da sakamakonsa. Rahamar ALLAH kuma tana kusa da masu kyautatawa.

ALLAH (ﷻ) Ya hana yaɗa ɓarna a bayan ƙasa bayan an gyara ta. Babban gyara da ALLAH ya yi wa ƙasa kuwa shi ne aiko da Manzonsa Muhammadu (ﷺ) da addininsa wanda ya ƙunshi Tauhidi, wato bautar ALLAH shi kaɗai ba tare da haɗa shi da komai ba.” [#FayyataccenBayani: 303-305]

Muji tsoron ALLAH domin mai yaɗa ayyukan ɓarna acikin al'ummah shi yafi laifi fiye da wanda ke aikata ɓarnar.

Masu bayyana ayyukan ɓarna sun yi nisa da afuwar ALLAH (ﷻ), Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Dukkan al'ummata za a musu afuwa sai dai masu bayyana laifuka, kuma daga cikin bayyanawan akwai, mutum ya aikata wani aiki (na laifi) da daddare, sannan ya wayi gari alhali ALLAH Ya rufa masa asiri, sai yace: ya wane, jiya na aikata kaza da kaza, alhali ya kwana Ubangijinsa yana rufa masa asiri, sai ya wayi gari yana tona asirin da ALLAH ya rufa masa.” [Bukhari da Muslim]

Muji tsoron ALLAH, idan zamu yi faɗakarwa da wa'anzantarwa mu yi shi ta usulubi mai kyau ba tare da yaɗa ɓarna ba. ALLAH (ﷻ) Ya ce:

ﻭَﺍﺗَّﻘُﻮﺍ ﻓِﺘْﻨَﺔً ﻟَﺎ ﺗُﺼِﻴﺒَﻦَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻇَﻠَﻤُﻮﺍ ﻣِﻨْﻜُﻢْ ﺧَﺎﺻَّﺔً ﻭَﺍﻋْﻠَﻤُﻮﺍ ﺃَﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﺷَﺪِﻳﺪُ ﺍﻟْﻌِﻘَﺎﺏِ٥٢۝

Ma'ana: "Ku kiyayi fitinar da ba za ta shafi masu laifi kawai ba, ku sani lallai ALLAH mai tsananin uquba ne.” [Anfal: 25]

Bilal Bin Sa'ad (Rahimahullah) Ya ce: “Shi aikin saɓo idan aka ɓoye shi to ba zai cutar da kowa ba sai mai shi kawai, amma idan aka bayyana shi, kuma ba a canza shi an yi inkari ba to zai cutar da dukkan al'umma.” [Sha'abul Imaan]

Wajibi ne ga duk Musulmi ya tsawatar ga masu aikata ɓarna domin idan ana aikata ɓarna aka yi shiru aka ƙyale to uƙubar ALLAH idan ta zo za ta shafi kowa da kowa ne, Mai laifi da marar laifi, abin buƙata dai shi ne ayi hanin ta hanyar da ta dace ba tare da an cigaba da yaɗa ɓarnar ba. ALLAH Yasa mu dace (Aameen)

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

BINTUS-SUNNAH

18 Jan, 10:20


18/RAJAB/1446H
18/JANUARY/2025

ADDU’AR YAU ASABAR:
Ya ALLAH muna neman tsarinka daga wasi-wasin Shaiɗan da dukkan sharrin shaiɗan.

HADISIN YAU ASABAR:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Shaiɗan zai zowa ɗayanku sai yace masa: Waye ya halicci kaza ? Kuma waye ya halicci kaza ? Har takai yace: To kuma waye ya halicci ubangijinka ? Idan yakai ga nan wajen, to mutum ya nemi tsarin ALLAH kuma ya katse TUNANIN.” [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi]
.
Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube
https://youtube.com/channel/UCG_W7_7gQdibxDgvhQdIEyQ

BINTUS-SUNNAH

18 Jan, 10:04


HAƘƘOƘIN DA KE KAN MA'AURATA!

TARE DA: Sheikh Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahullah)

BINTUS-SUNNAH

17 Jan, 23:20


Poetry: the petty one قصيدة النز written by Sheikh Sa'ud Al-Shuraim (Hafizahullah)

BINTUS-SUNNAH

17 Jan, 22:40


HUKUNCE HUKUNCEN RUƘIYYAH A SHARI'AH //06

(Daga fatawoyin manyan Malamai daban-daban)

Shin ya halatta Mace mai jinin al'ada (Haila) tayi amfani da ruwa ko mai da aka karanta Alƙur'ani akai?

Sheikh Salih Uthaymeen (Rahimahullah) Ya ce: “Ya halatta Mace Mai Haila tayi amfani da ruwa ko mai da aka karanta Alƙur'ani akai, ko dabino ko gurasa ko wani abu makamancin haka, ya halatta a Karanta Alƙur'ani kan Mai ko abincin maras lafiya, ko abun shansa, domin lallai ALLAH (ﷻ) Ya ce:

﴿وَنُنَزِّلُ مِنَ القُرآنِ ما هُوَ شِفاءٌ وَرَحمَةٌ لِلمُؤمِنينَ﴾

Ma'ana: “Kuma daga Alƙur’ani Muna saukar da abin da yake shi waraka ne da kuma rahama ga muminai;” [Isra'i: 82]

Idan aka yi amfani da Alƙur'ani ta fuskar da take da fa'ida ko maslaha ba a wulaƙanta Alƙur'ani ba, babu laifi.

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

BINTUS-SUNNAH

17 Jan, 21:54


Alhamdulillah mun kammala amsa TAMBAYARMU TA YAU.

Kamar yadda aka bada amsa daidai shine: Annabi Yunus (AS) shi ya ambaci wannan wato LAA ILAHA ILLALLAH ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMEEN.

Zikiri ne mai girma da sirri na ban mamaki da samun yayewa daga bala'o'i daban-daban ga duk wanda ya lizimce shi da ikhlasi da yaƙini zuwa ga ALLAH (ﷻ).

Yazo a cikin Alƙur'ani Maigirma kamar yadda ALLAH (ﷻ) Ya faɗa:

لا إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنتُ مِنْ الظَّالِمِينَ٧٨۝

Ma'ana: "Babu abin bautawa bisa cancanta da gaskiya sai Kai, tsarki ya tabbata a gare Ka, ni na kasance cikin azzalumai.” [Anbiya'i: 87]

Malaman Tafseer sun yi bayanin sababin sauƙar wannan addu'ar da cewa Ayoyin ALLAH (ﷻ) sun ba wa Manzon ALLAH (ﷺ) labarin Annabi Yunusa (AS) lokacin da ya ƙauracewa mutanensa da ALLAH Ya aiko shi wajensu yana cike da fushi, ba tare da samun izini daga Ubangijinsa na ƙaurace musu ba. Ya ƙaurace ne saboda sun doge a kan kafirci da saɓon ALLAH. ALLAH (ﷻ) Ya bayyana cewa, Annabi Yunusa (AS) bai yi zaton cewa ALLAH zai ƙuntata masa don ya bar jama'arsa kafirai ba. To amma sai ALLAH Ya jarrabe shi da faɗawa cikin ƙunci da tsanani yayin da kifi ya haɗiye shi. To a nan ne fa ya shiga addu'a yana cikin duhu a kan duhu; ga duhun dare ga na kogi ga kuma na cikin kifi, inda yake cewa: “Ya ALLAH babu abin bautawa da gaskiya sai kai; tsarki ya tabbata gare ka, lallai ni na kasance daga cikin azzalumai.”

Sai ko ALLAH Ya bayyana cewa ya amsa masa addu'arsa, ya tserar da shi daga tsananin da yake ciki, Ya fito da shi daga cikin cikin kifi. ALLAH kuma ya tabbatar da cewa kamar yadda ya tserar da Annabi Yunusa (AS), kamar haka ne yake tserar da muminai yayin da suka faɗa cikin wani tsanani ko musiba.

An Karɓo daga Sa'ad Bin Abi Waƙƙas (RA) Ya ce: Mun kasance muna zaune a gaban Annabi (ﷺ) sai Ya ce: “Shin ba na ba ku labarin abin da idan wani daga cikinku baƙin ciki ya sauƙar masa ko kuma wani bala'i daga cikin bala'o'in duniya ya sauƙa gare shi idan ya yi addu'a da wannan addu'ar za a yaye masa halin da ya ke ciki ba? Sai suka ce masa gaya mana sai ya ce: Ita ce addu'ar Zin-nuun (Annabi Yunus AS): “LAA'ILAHA ILLALLAH ANTA SUBHAANAKA INNI KUNTU MINAZ-ZAALIMEEN. Babu wani Musulmi da zai roƙi ALLAH da ita game da wata buƙatarsa sai ALLAH Ya amsa masa.”

[HaakimYa ruwaito shi (1864) da Ahmad: (1462) da Tirmidhi: (3504), Albany Ya inganta shi cikin As-saheeha: (1744)]

Jazakumullahu khayran 🥰

BINTUS-SUNNAH

17 Jan, 09:30


ƳAƳA SUNA TASOWA NE A KAN ABIN DA IYAYENSU SUKA TARBIYYANTAR DA SU A KAI

Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria (Hafizahullah)

BINTUS-SUNNAH

17 Jan, 08:48


‏اللَّهُمَّ صَلِّ وَسَلِّم وَبَاركَ عَلَى نَبِيِّنَا ﷴ ﷺ ♥️

BINTUS-SUNNAH

17 Jan, 08:28


17/RAJAB/1446
17/JANUARY/2025

ADDU’AR YAU JUMA'A :
Ya ALLAH ka sanyamu cikin bayinka amintattu, masu riƙo da gaskiya da ƙauracewa cin Amanar juna.

HADISIN YAU JUMA'A:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Abin da zaku fara rasawa daga addininku ita ce Amana.” [Silsilatus sahiha 1739, Jami'ul Ahadith: 9628]
.
Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube
https://youtube.com/channel/UCG_W7_7gQdibxDgvhQdIEyQ

BINTUS-SUNNAH

30 Dec, 09:37


28/JUMADA THANI/1446
30/DECEMBER/2024

ADDU’AR YAU LITININ:
Ya ALLAH Kada Ka zamar da zuciyoyinmu, bayan ka shiryar da mu, Ka bamu rahama daga wajenka, domin kai mai yawan Kyauta ne.

HADISIN YAU LITININ:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Kada ku rinƙa zagin zamani, domin ALLAH Shi ne zamani.” [Muslim Ya ruwaito shi]

TELEGRAM:
https://t.me/BINTUSSUNNAH

FACEBOOK:
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

BINTUS-SUNNAH

27 Dec, 11:15


25/JUMADA-ULA/1444
27/DECEMBER/2024

ADDU’AR YAU JUMA'A:
Ya ALLAH ka taimakemu ka datar damu da abubuwan da zasu amfanemu da addininmu.

HADISIN YAU JUMA'A:
Abu-Hurayrah (RA) Ya ce; Haƙiƙa Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Ka zama mai kwaɗayi akan abin da zai amfaneka, ka nemi taimakon Ubangiji, Kada ka gajiya.” [Muslim Ya ruwaito shi]
.
Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube
https://youtube.com/channel/UCG_W7_7gQdibxDgvhQdIEyQ

BINTUS-SUNNAH

26 Dec, 10:02


SALLAR WALAHA (صلاة الضحى) //09

Sallar walaha wasiyyace daga cikin Manyan wasiyyoyin Manzon ALLAH (ﷺ) ga Manyan Sahabbansa masu girma, wannan ke ƙara tabbatar mana muhimmancin wannan Sallah, wanda wasu daga cikin al'umma suke danganta ta da cewar Sallar tsofi ce, wannan fahimtar kuskure ne hadisai sun tabbatar da Sallah ce ta nafila kuma kowa da kowa zai iyayi domin samun lada, a addinance ma babu wata Sallah da akace ta tsofi ne ko ta matasa.

Daga Abi Hurayrah (RA) Ya ce: “Zaɓaɓɓan Masoyina Annabi (ﷺ) yayi min wasiya akan kada in sake in bar aikata abubuwa guda uku:

1-Sallar wallaha
2-Sallar Wutiri kafin ayi barci
3-Azumi uku a kowane wata. [Bukhari: 1178, Muslim: 721]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

BINTUS-SUNNAH

26 Dec, 10:01


24/JUMADA THANI/1446
26/DECEMBER/2024

ADDU’AR YAU ALHAMIS:
Ya ALLAH ka gafarta mana munanan ayyukanmu, kuma Ka karɓi kyawawan ayyukanmu ka dawwamar damu cikin farin ciki.

HADISIN YAU ALHAMIS:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Idan kyawawan ayyukanka suka sanya ka farin ciki, munanan ayyukanka kuma suka sanya ka baƙin ciki, to kai Mumini ne.” [Silsilatu Ahadith Assahiha 2/91, hadith No.550]
.
Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube
https://youtube.com/channel/UCG_W7_7gQdibxDgvhQdIEyQ

BINTUS-SUNNAH

25 Dec, 04:13


SALLAR WALAHA (صلاة الضحى) //08

Sallar walaha tana da ɗimbin falala ga kuma sauƙi ga wanda ALLAH Ya azurta shi da yinta, akwai daga cikin Falalarta samun gidan Aljannah guda ɗaya ko guda biyu ga wanda yayi sallar wallaha raka'a Takwas, kamar yadda yazo a hadith.

Manzon ALLAH (ﷺ) Yana cewa: “Wanda yayi sallar Walaha raka'a huɗu kuma yayi wasu huɗun kafin wannan na farko, yana da gida a Aljannah.” A wata riwayar Yana cewa: “Yana da gidaje guda biyu a Aljannah.” [Albany Ya kyautata shi cikin Silsilatus Sahīha]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

BINTUS-SUNNAH

25 Dec, 04:12


23/JUMADA THANI/1446
25/DECEMBER/2024

ADDU’AR YAU LARABA:
Ya ALLAH ka taimakemu wajen faɗin alheri da yaɗa shi, ka tsaremu da faɗin sharri da yaɗa shi.

HADISIN YAU LARABA:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Ku faɗi alheri, ku sami lada, ku yi shiru daga fadar sharri, ku kuɓuta.” [Saheehul Jami'i]
.
Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube
https://youtube.com/channel/UCG_W7_7gQdibxDgvhQdIEyQ

BINTUS-SUNNAH

24 Dec, 08:44


SALLAR WALAHA (صلاة الضحى) //07

Sallar Walaha tana sauƙe Ladar sadakar da aka ɗorawa kowace gaɓa a kowane yini da rana take ɓullowa, kuma sallar Wallaha raka'a biyu kaɗai tana daidai yin Sadaƙa sau 360, kasancewar a jikin kowane bawa akwai gaɓɓai 360 Kuma idan gari ya waye dukkanin wannan gaɓɓan suna da haƙƙii na sadaƙa akan wannan bawa.

An Karɓo daga Abi Zarri (RA) daga Annabi (ﷺ) Ya ce: “Kowace gaɓa ta ɗan Adam tana wayar gari a tare da ita akwai aikin sadaƙa da aka ɗora mata, Kowace SUBHANALLAH sadaƙa ce, kowace ALHAMDULILLAHI sadaƙa ce, kowace LA'ILAHA ILLALLAH sadaƙa ce, kowace ALLAHU AKBAR sadaƙa ce, umarni da kyakkyawan aiki sadaƙa ne, hani akan mummunan aiki sadaƙa ne, kuma yana isar maka dukkan waɗannan sadakokin yin sallar wallaha raka'a guda biyu.” [Muslim: 1181]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

BINTUS-SUNNAH

24 Dec, 08:42


22/JUMADA THANI/1446
24/DECEMBER/2024

ADDU’AR YAU TALATA:
Ya ALLAH muna godiya ga abin da Ka raba Ka ba mu, kada Ka sanyamu cikin ma'abota roƙo, kuma Ka tsaremu da talauci.

HADISIN YAU TALATA:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Babu wani mutum da zai buɗewa kansa ƙofar roƙo, yana roƙon Mutane, face ALLAH Ya buɗe masa ƙofar talauci.”  [Saheehul Jami'i]
.
Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube
https://youtube.com/channel/UCG_W7_7gQdibxDgvhQdIEyQ

BINTUS-SUNNAH

23 Dec, 22:36


FAT-HUL MAJEED SHARHU KITABIT-TAUHEED //97

Buƙatuwar Al'ummah kan su koyi Alƙur'ani da Sunnah, da barin abinda basu ba, na ilimin jayayya da ilimul kalam da manɗiƙi da falsafanci, yin hakan akwai alkhayri ga Al'ummah da duniya, domin saƙon Annabi (ﷺ) ya shafi duniya baki ɗaya,

Alƙur'ani ba iya na larabawa bane, na kowa ne, kuma hujja ne ga duk duniya,

Buƙatuwar bawa ga saƙon yafi buƙatuwarsa zuwa ga abinci da abin sha da iska, domin babu rayuwa sai da wannan kamar yadda babu rayuwar jiki idan ba abinci da abin sha da iska.

Tammat bihamdulillah, Rabbil Alamin
-Sheikh Salih AlFauzan (Hafizahullah)

https://t.me/BINTUSSUNNAH

BINTUS-SUNNAH

01 Dec, 18:34


KU YAWAITA MURMUSHI !!!

Ibn Baɗɗal (Rahimahullah) Ya ce: “Haɗuwa da mutane da Murmushi da sakin fuska yana daga cikin halayen Annabawa, yana kore girman kai, yana jawo soyayya.” [Sharhul-bukhari 5/193]

“Mutanen da suke ƙoƙarin sanya farin ciki a zukatan mutane, ba a gane baƙin cikinsu, saboda suna haɗiye nasu baƙin cikin domin kada su sanya mutane cikin damuwa.”

Ya ALLAH ka yaye damuwar dake ɓoye a zukatan bayinka, ka basu ladar murmushin dake ɗauke akan fuskokin su. (Aameen)

BINTUS-SUNNAH

01 Dec, 18:34


“Ka Sani Lallai ALLAH Yana gaggautar da Abubuwa agareka ba saboda wayonka ba, kuma yana jinƙirtar da Abubuwa agareka ba don yayi mantuwa ba, Rayuka da yawa sukan ratayu ga Abubuwa da dama ba don ya manta da su ba, ka kasance a raye domin biye da abunda zai gabato gareka kuma ka kasance mai godewa ALLAH cikin ko wani yanayi .”

#ALHAMDULILLAH.

BINTUS-SUNNAH

28 Nov, 23:56


“Mutane da dama suna da Kirki, amma yadda ake mu'amala dasu yasa suka koma Maras sa Kirki, Mutane da dama suna da ƙarfi, amma yadda ake mu'amala dasu ne yasa suka koma masu Rauni. Haƙiƙa Kyakkyawar mu'amala ko akasinta kan taka rawa wajen canja ɗabi'un ɗan-adam.”

©ℬ𝒾𝓃𝓉𝓊𝓈 𝒮𝓊𝓃𝓃𝒶𝒽

BINTUS-SUNNAH

28 Nov, 23:53


KADA KA YI FUSHI !!!

kada ka taɓa zaton cewa matsanancin hali da kake ciki tozarci ne daga ALLAH, A'a karamci ne daga gare Shi, domin waɗanda suka fi kowa fuskantar tsanani a cikin mutune sune zaɓaɓɓunsa, don haka kada ka yi fushi kuma kada ka butulcewa Ubangijinka.

Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Misalin mumini kamar shuka ce, ba ta gushewa face iska tana kaɗa ta, haka mumini ba ya gushewa face bala'i yana samunsa, Misalin munafiki kuma kamar shukar shinkafa ce, ba ta kaɗawa har lokacin yanke ta.” [Saheeh Muslim: 2809]

Imam Annawawiy (Rahimahullah) Ya ce: Ma'anar wannnan hadisin shi ne: “Mumini Mutum ne mai fuskantar damuwowi masu yawa, a jikinsa, ko iyalansa, ko dukiyarsa, kuma hakan na Samun sa ne don kankarar zunuban sa da ɗaukaka darajarsa.” [Sharh Sahih Muslim: 17/153]

©ℬ𝒾𝓃𝓉𝓊𝓈 𝒮𝓊𝓃𝓃𝒶𝒽

BINTUS-SUNNAH

28 Nov, 23:51


DAGA ƊABI'UN RANAR JUMA'A !!!

● Karanta Suratul Kahfi.
● Yin wanka.
● Yiwa Annabi (ﷺ) salati.
● Sanya tufafi mai tsafta.
● Halartar Sallar Juma'a.
● Sanya turare.

©ℬ𝒾𝓃𝓉𝓊𝓈 𝒮𝓊𝓃𝓃𝒶𝒽

BINTUS-SUNNAH

26 Nov, 21:46


❝ Mafi Wadatar Mutane a duniya, ba shi ne wanda yake da dukiya ba, Amma Wanda ya mallaki lafiya da kwanciyar hankali shi ne Mawadaci.❞

©ℬ𝒾𝓃𝓉𝓊𝓈 𝒮𝓊𝓃𝓃𝒶𝒽

BINTUS-SUNNAH

26 Nov, 21:41


ASALIN MUTUM !!!

Idan Kana son sanin haƙiƙanin mutum kada ka ruɗu da abun da yake faɗa, ka lura da mai yake aikatawa, ka sani mutum ba'a gane shi da abun da yake faɗa, sai dai ana gane shi ne da abunda yake aikatawa.”

©ℬ𝒾𝓃𝓉𝓊𝓈 𝒮𝓊𝓃𝓃𝒶𝒽

BINTUS-SUNNAH

26 Nov, 21:39


KADA KU RUƊU DA DUKIYA DA JINƘAI DA ALLAH YAKE AZURTA WASU GAFALALLU KO KAF*RAI DAGA CIKINKU !!!

Sau da dama son zuciya kan motsawa wasunmu wanda suke tsintar kawunansu cikin wasiwasin shaiɗan wanda yake ƙawata musu ko nuna musu irin dukiya ko daula da ALLAH Yayi ga waɗanda ba su yi imani da ALLAH ba kuma ba su kasance masu bauta agare shi ba kuma sun kasance masu aikata saɓo, amma kuma ya hore musu dukiya da alatun duniya mai gushewa, ya kuma haƙalto musu da wasiwasin cewa gashi su sunyi imani suna bautawa ALLAH dare da rana amma kuma ALLAH Ya jarrabesu da talauci da ƙuncin rayuwa.

Ku yaƙi son zuciyoyinku kuma ku yaƙi shaiɗan domin lalle Ubangijinku ya kasance Mai tausayi ne kuma Mai jinƙai, kuma ku sani cewa ita dukiya fitina ce kuma ALLAH Yana azurta wasu daga cikin bayinsa da ita ne domin ya jarrabe su, ku sani cewa IMANI shi ne mafi Ƙololuwar arzikin da ba kowa ALLAH Yake bawa ba sai ga bayinsa zaɓaɓɓu, saɓanin ita dukiya kuwa yana iya bada ita ga mumini da kaf*ri.

Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Haƙiƙa ALLAH Yana bada dukiya ga wanda yake so har da waɗanda baya so amma baya bada Imani sai ga bayin ALLAH zaɓaɓɓu masoyansa.” [Sahihul targib hadith na 1571]

Hakanan ita duniyar gaba ɗaya bata da wata daraja balle ƙima a wajen ALLAH (ﷻ) domin da tana da ƙima da daraja haƙiƙa da ALLAH bai azurta kaf*rai da gafalallu da ita ba.

Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Da ace duniya ta kai matsayin fiffiken sauro a wajen ALLAH, da ALLAH bai shayar da kafiri acikinta kurɓar ruwa ɗaya ba.” [Tirmizy ya ruwaito shi, Albany ya inganta shi]

Kada ku ruɗu da duniya domin haƙiƙa a wajen ALLAH wulaƙantacciya ce, maras ƙima, banza ce, ba Komai bace a wajen ALLAH, bata kai ƙimar fiffiken ƙuda ba ma, kuma da ace tana da ƙima Ko Yaya a wajenSa da Kaf*rai da gafalallu baza su samu arzikin komai ba a cikinta, Ko da kuwa maƙwarwa na ruwa ɗaya, saboda rashin cancantarsu da hakan domin sun Kafircewa mai ciyar da su, ya shayar da su, Kuma Ya azurta su.

Hakanan yazo cikin suratul zukhruf, ALLAH Ya tabbatar idan ba don tsoron kar bayinsa su kafurce da ruɗuwar duniya ba da ya sanyawa dukkan kaf*rai daula kuma hakan ba zai cutar da ALLAH da komai ba, kamar yadda Ya ce:

وَلَوۡلَاۤ أَن یَكُونَ ٱلنَّاسُ أُمَّةࣰ وَ ٰ⁠حِدَةࣰ لَّجَعَلۡنَا لِمَن یَكۡفُرُ بِٱلرَّحۡمَـٰنِ لِبُیُوتِهِمۡ سُقُفࣰا مِّن فِضَّةࣲ وَمَعَارِجَ عَلَیۡهَا یَظۡهَرُونَ٣٣۝ وَلِبُیُوتِهِمۡ أَبۡوَ ٰ⁠بࣰا وَسُرُرًا عَلَیۡهَا یَتَّكِـُٔونَ ٤٣۝ وَزُخۡرُفࣰاۚ وَإِن كُلُّ ذَ ٰ⁠لِكَ لَمَّا مَتَـٰعُ ٱلۡحَیَوٰةِ ٱلدُّنۡیَاۚ وَٱلۡـَٔاخِرَةُ عِندَ رَبِّكَ لِلۡمُتَّقِینَ٥٣۝ [الزخرف ٣٣-٣٥]

Ma'ana: “Da ba don kada da yawa daga cikin jahilai (wawaye) su yi tsammanin bayar da dukiya shi yake nuna wanda muke so daga cikin bayi, har wannan ya sa su kafirce, lallai da mun sanya wa gidajen waɗanda suka kafirce rufi na azurfa da matattakalai na azurfa, da kuma ƙofofi da gadaje na alfarma da za su rinƙa kishingida akansu, kuma mu ba su kayan ado na zinare. Sai dai duk Waɗannan ba komai ba ne face ɗan jin daɗin duniya mai gushewa, alhali kuwa Aljanna a wurin Ubangijinka ta masu taƙawa ce.” [Suratul Zukhruf: 33-35]

Waɗannan ayoyin sun isa su nuna maka dukiya da arzikin da ALLAH ya bawa kaf*urai da gafalallu ba shi ne ma'aunin gane waɗanda ALLAH yake so ba, ya isa ya tabbatar maka da cewa masu imani da taƙawa sune bayin ALLAH nagartattu kuma zaɓaɓɓu a wajensa.

Don haka kuyi imani da ALLAH kuma ku bauta masa shi kaɗai kuma ku gode masa bisa ni'imar da yayi muku, idan kuka yi haka zaku riski kyakykyawar sakamako da jin daɗi na har'abada. ALLAH Yasa mu dace (Aameen)

©ℬ𝒾𝓃𝓉𝓊𝓈 𝒮𝓊𝓃𝓃𝒶𝒽

BINTUS-SUNNAH

26 Nov, 21:37


SABABIN GUSHEWAR NI'IMA !!!

Ibnul Qayyim (Rahimahullah) Ya ce: “Ba'a ƙwace ni'ima, sai a dalilin daina jin tsoron ALLAH, da kuma cutar da Mutane.” [Ahkaam Ahluz-zimmah: 1/88]

Duk wanda ya ƙauracewa tsoron ALLAH kuma ya zamanto ma'abocin cutarwa ga mutane toh ya sani koda yana acikin ni'imar ALLAH toh ALLAH yana yi masa talala ne, ya kiyayi ranar da ALLAH zai yi masa damƙa, damƙar da babu mai iya ƙwato shi.

© ℬ𝒾𝓃𝓉𝓊𝓈 𝒮𝓊𝓃𝓃𝒶𝒽

BINTUS-SUNNAH

26 Nov, 21:35


Ibnul Mubarak (Rahimahullah) Yace: “(Mutum) ba zai gushe ba yana da ILIMI matuƙar yana neman ilimin, amma idan yayi zaton lallai shi haƙiƙa yana da ilimi, Toh haƙiƙa ya zama Jahili.” [Al-mujalisatu wa Jawaahirul ilmi]

Matuƙar mutum yana neman ilimi toh zai iya kasancewa ma'abocin ilimi, amma daga lokacin da mutum yayi tsammanin yakai ƙololuwa a ilimi yana jin kansa a matsayin wani kogin ilimi yana ƙasƙantar da ilimin wasu a matsayin ba komai bane idan aka haɗa da na shi ilimin, toh ya zama Jahili, saboda shi ilimi ba a gama saninsa, kuma Ma'abota ilimi na haƙiƙa basa alfahari da girman kai da ilimin da ALLAH ya basu domin sun san cewa shi ilimi kogi ne.

© ℬ𝒾𝓃𝓉𝓊𝓈 𝒮𝓊𝓃𝓃𝒶𝒽

BINTUS-SUNNAH

26 Nov, 21:33


“Muna rayuwa a Wani zamani ne Wanda idan aka ji alkhairi daga gare ka sai a ɓoye... Idan Kuma aka ji sharri daga gare ka sai a bayyana shi... Idan Kuma ba'aji komai daga gare ka ba sai a ƙirƙiro wani abu a faɗa akan ka.”

© ℬ𝒾𝓃𝓉𝓊𝓈 𝒮𝓊𝓃𝓃𝒶𝒽

BINTUS-SUNNAH

26 Nov, 21:32


Ƴaƴanka sun fi kwaikwoyon Ayyukan ka, ba maganganun ka ba !!!

BINTUS-SUNNAH

26 Nov, 21:30


Ana ninninka sakamakon ayyuka na ƙwarai saboda gwargodon yawan tunanin zuciya da ambaton ALLAH da kuma mai da hankali akan haka.

© ℬ𝒾𝓃𝓉𝓊𝓈 𝒮𝓊𝓃𝓃𝒶𝒽

BINTUS-SUNNAH

22 Nov, 14:33


KA KASANCE MAI NEMAN MAFAKA GA ALLAH

Sheikh Ibn Uthaymeen (Rahimahullah) Ya ce: “kada ka karkata ga abunda ke zuciyarka na tabbatuwar imani, misali; ka dogara cewa Shaiɗan ba zai janye ka daga kai ba, ba zai sanya maka son zuciya da umarni da mummuna ba, ka kasance mai neman mafaka ga ALLAH (ﷻ) kana mai neman tabbata.” [Tafsir Suratul Yãsin na Ibn Uthaymeen]

Haƙiƙa ya cancanci Mutum yana roƙon ALLAH sabati, ko da ace ya san gaskiya kuma yana aiki da shi yana kuma ƙudurce shi, kada ya amince cewa zuciyarsa ba zata karkace ba ko kuma a fitine shi, sai fitina tazo ta zamar da shi ya ɓata daga hanyar ALLAH, saboda haka ne Manzon ALLAH (ﷺ) Yake yin wannan addu'ar kamar yadda yazo a hadith.

Daga Ummu Salma (RA) ta ce: “Ya kasance daga mafi yawan addu'ar Annabi (ﷺ) yana cewa:

اللهم يا مقلب القلوب ثبت قلبنا على دينك

Ma'ana: “Ya Ubangiji, ALLAH Kai ne mai jujjuyar da zukata Ka tabbatar da zukatan mu akan addininka.” [Silsilatus saheeha: 2091]

Don haka wannan addu'a ce da ya kamata muyi riƙo da ita ta hanyar yawaita yinta.

© 𝔅𝔦𝔫𝔱𝔲𝔰𝔰𝔲𝔫𝔫𝔞𝔥

BINTUS-SUNNAH

27 Oct, 21:45


TUNATARWA !!!

AZUMIN GOBE LITININ GA WANDA YA SAMU IKO !!!

BINTUS-SUNNAH

27 Oct, 12:24


24/RABI'UL THANI/1446
27/OCTOBER/2024

ADDU’AR YAU LAHADI:
Ya ALLAH ka tsaremu da cin dukiyar haram kuma ka tsaremu daga zaluntar bayinka ta kowace hanya.

HADISIN YAU LAHADI:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Haƙiƙa Wasu Mazaje suna cin dukiyar ALLAH ba ta hanyar da ta dace ba, wuta ta tabbata a garesu ranar Alƙiyama.” [Bukhari Ya ruwaito shi]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

BINTUS-SUNNAH

26 Oct, 17:28


KADA MU SHUKA SHARRI GA JUNANMU !!!

TARE DA: Professor Isa Ali Pantami (Hafizahullah)

BINTUS-SUNNAH

26 Oct, 11:33


23/RABI'UL THANI/1446
26/OCTOBER/2024

ADDU’AR YAU ASABAR:
Ya ALLAH ka sanyamu cikin masu tsaida Sallah da zuri'armu, kuma ka karɓi addu'o'inmu.

HADISIN YAU ASABAR:
An Karɓo Daga Ibn Mas'ud (RA) Ya ce: Haƙiƙa an tambayi Manzon ALLAH (ﷺ), Wane aiki ne yafi Falala ? Sai Yace: “Yin Sallah a Lokacinta.” [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

BINTUS-SUNNAH

25 Oct, 13:06


22/RABI'UL THANI/1446
25/OCTOBER/2024

ADDU’AR YAU JUMA'A:
Ya ALLAH dukkan godiya ta tabbata a gareka, godiya mai yawa, kuma kayi rahama agare mu.

HADISIN YAU JUMA'A:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: "Idan bawa ya ce godiya ta mai yawa ta tabbata ga ALLAH, sai ALLAH (ﷻ) Ya ce (ma Mala'iku) ku rubuta rahama Ta maiyawa ga bawa Na.” [Saheehut-targhib: 1578]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

BINTUS-SUNNAH

24 Oct, 10:49


21/RABI'UL THANI/1446
24/OCTOBER/2024

ADDU’AR YAU ALHAMIS:
Ya ALLAH ka sauƙaƙa mana cikin jarrabawar da kake mana, kuma ka bamu ikon cinyewa.

HADISIN YAU ALHAMIS:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Girman Sakamako yana zuwa gwargwadon girman bala'i, Haƙiƙa ALLAH Yana son mutane idan ya jarrabe su, duk wanda ya yarda da ƙaddarar, To yardar ALLAH ta tabbata a gareshi, wanda kuma yayi fushi da ƙaddarar, fushin ALLAH Ya tabbata a gare shi.” [Tirmizy ya ruwaito shi]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

BINTUS-SUNNAH

23 Oct, 11:26


20/RABI'UL THANI/1446
23/OCTOBER/2024

ADDU’AR YAU LARABA:
Ya ALLAH ka taimaki musulunci da musulmai a duk inda suke, ka karya kafurci da azzalumai a duk inda suke.

HADISIN YAU LARABA:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Wata ƙungiya daga cikin al'ummata ba za ta gushe ba tana kan gaskiya, Duk wanda ya wulaƙanta su ba zai cutarda su ba, har zuwa sanda lamarin ALLAH zai zo.” [Muslim ya ruwaito shi]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

BINTUS-SUNNAH

22 Oct, 10:27


19/RABI'UL THANI/1446
22/OCTOBER/2024

ADDU’AR YAU TALATA:
Ya ALLAH ka gafarta mana zunubanmu ka azurtamu da kyakkyawan ƙarshe.

HADISIN YAU TALATA:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Zamanin zai kusanto (zai rinƙa sauri), ayyuka za su ragu (na alkhairi cikin mutane) za'a sanyawa mutane tsananin rowa, kuma 'ALHARAJ' zai yawaita. sahabbai suka ce, menene ALHARAJ ya Manzon ALLAH? sai yace shine Kashe-Kashe (kisa ko ina).” [Bukhari: 6688, Muslim: 4956]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

BINTUS-SUNNAH

21 Oct, 11:18


18/RABI'UL THANI/1446
21/OCTOBER/2024

ADDU’AR YAU LITININ:
Ya ALLAH ka sanya alkhairi a cikin ƙuruciyarmu da tsufanmu kasa mu amfani kanmu da al'ummarmu a tsawon rayuwarmu.

HADISIN YAU LITININ:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Mafi sharrin mutane, shi ne wanda rayuwarsa ta yi tsawo, kuma aikinsa ya yi muni.” [Tirmidhi: 2330]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

BINTUS-SUNNAH

20 Oct, 11:38


17/RABI'UL THANI/1446
20/OCTOBER/2024

ADDU’AR YAU LAHADI:
Ya ALLAH ka kyautata mana harsunan mu ka tsare mu daga gulma da binciken abinda bai shafe mu ba.

HADISIN YAU LAHADI:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Ya Ku taron waɗanda suka yi Imani da harshensu, amma imani bai shiga zuciyarsu ba, Kada ku rinƙa yin gulmar musulmi, Kuma kada ku rinƙa bibiyar al'aurar su, domin duk wanda yabi al'aurar su, shi ma ALLAH zai bi tasa al'aurar, duk kuwa wanda ALLAH ya bi al'aurar sa, ALLAH zai kunyata shi a cikin gidansa.” [Abu-dawud ya ruwaito shi, Albany ya Inganta shi]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

BINTUS-SUNNAH

19 Oct, 22:14


FAT-HUL MAJEED SHARHU KITABIT-TAUHEED //89

CETO DA ZA A YI A LAHIRA IRI SHIDA (6) NE:

1● Babban ceto da Manyan Annabawa zasu ja da baya wajen nema, Annabi (ﷺ) zai ce shi zaiyi, shi kaɗai ke samo ceton nan.

2● Ceto ƴan Aljannah su shige ta.

3.● Ceton masu zunubai da za a sa a wuta kar su shiga.

4● Ceton masu zunubai da suke wuta a fito dasu.

5● Ceto a cikin Aljanna a ƙara ma wasu matsayi da daraja.

6● Ceton Baffan Manzon ALLAH (ﷺ) Abu ƊALIB domin sauƙaƙa masa azaba za a fito dashi saman wuta a samasa takalman wuta.

-Sheikh Salih AlFauzan (Hafizahullah)

https://t.me/BINTUSSUNNAH

BINTUS-SUNNAH

19 Oct, 14:40


ثَمَانِيَةٌ تَجرِي عَلَى النَّاسِ كُلِّهِم
وَلا بُدَّ لِلإِنسَانِ يَلقَى الثَّمَانِيَهْ

سُرُورٌ وَحُزنٌ وَاجتِمَاعٌ وَفُرقَةٌ
وَيُسرٌ وَعُسرٌ ثُمَّ سُقمٌ وَعَافِيَه

BINTUS-SUNNAH

19 Oct, 09:27


16/RABI'UL THANI/1446
19/OCTOBER/2024

ADDU’AR YAU ASABAR:
Ya ALLAH ka bamu rinjaye da imani da aminci da musulunci da nasara akan abin da kake so kuma ka yarda  dashi.

HADISIN YAU ASABAR:
Daga Abdullahi Ɗan Abbas (RA) Ya ce: Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce da shi: “Ya kai yaro: Zan sanar da kai wasu maganganu; Ka kiyaye ALLAH zai kiyaye ka, Ka kiyaye ALLAH za ka tarar da shi gaba gare ka Idan za ka roƙa, ka roƙi ALLAH, Idan za ka nemi taimako ka nemi taimakon ALLAH, Ka sani da a ce Al'umma za ta haɗu a kan ta amfane ka da wani abu, ba za su amfane shi da komai ba, sai abinda ALLAH ya rubuta gare ka, Da kuma za su haɗu a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su iya cutar da kai da komai ba, sai da abinda ALLAH ya rubuta a Kara, An ɗage Alƙaluman, Takardun sun bushe.” [Tirmizi da Ahmad suka ruwaito shi]

Telegram
https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

BINTUS-SUNNAH

18 Oct, 11:51


Shin kuna yin wasu daga cikin waɗannan kusakuran a ranar Juma'a?!!!

BINTUS-SUNNAH

18 Oct, 08:54


15/RABI'UL THANI/1446
18/OCTOBER/2024

ADDU’AR YAU JUMA'A:
Ya ALLAH ka ƙara salati ga Manzon tsira (ﷺ) da iyalansa da sahabbansa da waɗanda suka yi imani suka kyautata halayensu har izuwa ranar al-ƙiyamah.

HADISIN YAU JUMA'A:
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Haƙiƙa ALLAH Yana da wasu mala'iku masu yawo a bayan ƙasa, suna isar min da saƙon gaisuwar al'mmatah a gare ni.” [Nasa'i Ya ruwaito shi]

TELEGRAM:
https://t.me/BINTUSSUNNAH

FACEBOOK:
http://www.Facebook.com//Bintusunnah/