ZAUREN DALIBAN SUNNAH @zaurandalibansunnah Channel on Telegram

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

@zaurandalibansunnah


📲 ZAUREN DALIBAN SUNNAH.📲
Ibnul Mubarak(RA) ya ce: Babu wata daraja mafi falala da ɗaukaka bayan Annabta kamar yaɗa ilimi mai amfani.
Ku zuba hannayen jarinku ta hanyar yaɗa ilimin Addini
barakallahu feekum💌

ZAUREN DALIBAN SUNNAH (Hausa)

ZAUREN DALIBAN SUNNAH.nnZauran Daliban Sunnah shi ne wani Telegram channel da ya kunshi manyan littafai da kuma bayani game da Sunnah a farkon jami'an tsakanin musulmi. A wannan channel za mu kasance a cikin girman ilimin Addini da ke ciki. An samo wasu bayanai da dama akan Sunnah, takaitaccen addini, da kuma hikayoyi da addini da suka samu tare da cewa sunnah ta shiga al'umma har zuwa lokacin da Annabta (SAW) ke rayuwa.nnZa mu cika wannan channel da littafan fassarar rayuwa da saukin amfani da Sunnah a kan mu, don samun bayanai da kuma fahimtar addini a kanmu. Da wannan hanyar, za mu ba kowa duk abin da ya kamata ya sani game da sunnah da addini, kuma a yi kokarin kawo mana wannan ilimin ga dukkanin musulmi.nnZa mu cigaba da zama a kan wannan channel, don ku ziyarci da kuma zuba hannu. Barakallahu feekum!💌

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

24 Nov, 09:59


Yo in ba bagidaje ba wadda baisan mace da sirrin zama da ita ba......................

Tayaya Allah zai maka ni'imar mace mai son ka da son farantama, ta ma kwalliya, ta buga girki, kana sin abunda takema ko yadda take da yasa har kake jin dadin zama da ita.......

Amma ka gagara yaba mata ko godemata ko nuna farin cikin ka da samunta a matsayin mata, ko ka furtamata kana jin dadin zama da ita ?

Shin in ka faɗa harshen ka ne zai naɗe ko ajin kane zai zube ? Yo in banda naka tayaya zata samu karfin guiwar ci gaba da yin wadannan abubuwa ?

Haba Malam Audu.... gobe sai kace tabar baka kulawa ko ba kai bane a gabanta ? Ko kace mata iya riqe miji ba ?

Shin yanzu mai wanan hali yasan mace da yadda ake zama da ita kuwa ?

Tare da 🖊Coach Fatimah Chikaire

Dalibi mai neman ilimi Graphics Designers.

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

24 Nov, 09:01


Akasarin maza ko da ki na musu abun da suke so ko jin dadin sa ba lallai su faɗa mi ki ba, sai dai su yi ta miki 'yar kora kunya da hauka, basarwa da kame kame kamar abun ba wani abun gila bane a wajen sa, wani kuma boli da watsi zai yi dake da abun kamar bai dame shi ba, wani ba sannu balle nagode....................

Amma wallahi har cikin tsakiyar kokon zuciyar sa dadin abun da kike musun su ke ji, hasalima shi kadai in zai keɓe harda tsalle, tafi da buga kafa zaiyi adole ga shegen ya ramfo zuciya da rayuwar wata, yayi ta jin dadin yanzu shi akema haka, ko yaji shima ashe yana da matsayin da za a na masa haka.

Ɗan baɗo da kuwa zai jiyo tafiya ko muryar ki zuwa inda yake firit zai nitsu ya murtuke fuska ya murza gashin baki ya soma wani basarwa yana kaɗa 'yan kafafuwa da danna waya kamar wani boss.

Alhali ko kallo da tuna abun da kike masa yayi sai yaji dadi a ran sa, duk inda ya samu dama kuwa sai ya yabaki da abunda kike masa amma ba lallai ke ya fada miki ba.

Rabu dashi kar ki damu da sai lallai ya fada miki, ke dai cigaba da abunda kike yin, dan 'yan wannan kunji kunjin abubuwan da kike ganin kamar bai damu dasu ba ko baya jin dadin su, ko baya yabawa ko kike ga kamar baya lura, ina tabbata miki su ne dalilin da yasa yake ɗaga miki kafa yake barin ki ki share a wasu abubuwa da wasu kyautata miki da yakeyi, ba lallai ya fada miki ba, amma kuma abunda yake miki a aikace zai iya tabbatar miki da abunda bai da qarfin furta miki.

In da kuwa zaki daina waddan abubuwa dan tunanin baya magana akai, ina tabbata miki zai rage tallafi ko ya dage tallafin da yake miki kamar yadda kika bar yi kema, haka kuma watarana sai yayi korafi. Haka kuna kar ki damu da abunda yake korafi akai su yana son a gyra sune, kyautatawan da kike masa yake shuru a kai ina tabbata miki yana so kuma yajin dadi da kike masa su.

Shiyasa yake da kyau Ku zama masu lura da duba ayyukan mazajen ku fiye da abunda kuke son su furta ko abunda suke furtawa.

Tare da 🖊Coach Fatimah Chikaire

Dalibi mai neman ilimi Graphics Designers.

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

24 Nov, 08:24


Allah ya bamu dacewa, amin

Allah ya tsare mana imanin mu da mutumcin mu, amin

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

24 Nov, 08:19


DAN UWA MATSO KAJI:

"Kowa kaga ya samu wata dama to tabbas wani fitacce ya sami irin wannan damar yayi zamanin kafin shi".

"Ka sani in kai mai alkairi ne ko mai sharri lokaci zai zo ya shafe ka tare da zamanin ka..Kuma tabbas za'a yi maka tambaya kan ni'imar da aka yi maka".

"Don haka kar kayi wasa da damar da Allah ya baka. Haka nan kada wata ni'ima ta sanya ka zama mai wulaqanci domin komai yana da karshen lokacinsa".

"Kar kaki taimakon addini ko watsi da al'ummar mu kaki kulawa da kowa. Kada kaji dagawa da isa har kana tozarts wani.. komi yayi farko yana da karshe".

"Mu sani tarihi adali ne, kuma tarihi baya tausayi baya tsoro zai ambace ka a wata rana, ya bada labarin yadda kayi a rayuwar ka".

Allah ya bamu dacewa, amin


🖊 Sheikh Aliyu Said Gamawa Hafizahullah.

Dalibi mai neman ilimi

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

23 Nov, 20:41


📚 *Karatun Littafin.*📚
🌯🌯🌯🌯🌯🌯🌯🌯


*AL'LU'ULU WAL'MARJAN.*


*اللؤلؤ والمر جا ن فيما اتفق عليه الشيخان.*


*Darasi na 226*


Tare da :- *Sheikh Lawan Abubakar Shuaibu Triumph (Hafizahullah).*
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*Ranar Asabar*
*21-05-1446 =23-11-2024*

*Daga Masjidil Qur'an Bacirawa Kano.*

*Ayi sauraro lafiya*

Domin Bada Gudunmawar ka/ki
👇🏼
0602936955
Arrisalah Foundation
Gt Bank

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

23 Nov, 20:07


Allah ya bamu dacewa duniya da lahira amin.

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

23 Nov, 19:45


LOKACIN SANYI
-
•┈┈┈┈•﷽•┈┈┈┈•
-
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.
-
Kamar dai yadda kowa ya sani, yanzu muna fuskantar lokacin sanyi ne ko ma nace mun fara shiga cikinsa gadan-gadan. Wato shi sanyi yana da wasu darajoji da muhimman lokuta a cikinsa,saboda haka kada muyi wasa da ibada a cikinsa, kuma kada mu aibanta zuwansa.
-
AIBANTA LOKACIN SANYI:
_______
Zaminin Sanyi Shima Halitta Ne Na Allah Kamar Yadda Kowane Zamani Yake, Yana Daga Cikin Kuskuren Da Mutane Suke Yi A Yau Shine Aibanta Lokacin Sanyi, Za Kaji Sunata Faɗar Munanan Maganganu Akan Sanyi, Amma Basu Farga Da Cewa Shima Umurni Yake Karɓa Daga Gurin Ubangiji Allah Ba, kuma wannan siface ta butulcewa Ni'imar Allah"
-
FALALAR LOKACIN SANYI:
*_______*
"Annabi ﷺ yace Shin bana nuna muku Abinda Allah yake Kankare Zunubai dashi ba, kuma yake daukaka darajar bawa dashi, (sahabbai sukace eh,) sai yace cika alwala a lokacin sanyi (lokacin da mutum yake kyamar taba ruwa) da yawn tattaki zuwa masallaci, da zaman jiran lokacin sallah, wannan shine ribaɗi wannan shine ribaɗi (dako / tsammani)"
(Muslim da Tirmiziy)
-
GARAƁASAR LOKACIN SANYI:
________
Manzon Allah ﷺ, Yace:
"Shin bana nuna muku Abinda allah yake Kankare Zunubai dashi ba, kuma yake kara muku lada, (sai sahabbai sukace eh,) sai yace cika alwala a lokacin da jiki baya so, da yawan tattaki izuwa masallaci, wannan shine ribaɗi wannan shine ribaɗi"
(Muslim)
-
DARAJAR LOKACIN SANYI:
________
Umar Ɗan Kaɗɗabi Yace:
Lokacin Sanyi Wata ganima ta masu bautar Allah, (ma'ana bayi zasu yawaita yin azumi cikin sauƙi, da ƙiyamul-lali cikin dare.
(Al-Hilyatu Abu Nu'aim)
-
Amir Ɗan Ma'sud Yace:
_______
Lokacin Sanyi wata ganima ce wacce tazo a araha.
(Musnad Imamu Ahmad)
-
DALILIN JIN TSANANIN SANYI:-
_______
Manzon Allah ﷺ, Yace:
Wuta Ta Kai kokenta zuwa ga Allah, tace ya ubangiji sashi na yana cinye sashi, sai Allah yayi mata Izni da tayi huci sau biyu a shekara, sai Annabi yace wannan shine dalilin da yasa lokacin sanyi kuke jin tsananin sanyi, lokacin zafi kuma kuke jin tsananin zafi.
(Bukhari Da Muslim)
-
IBADA A LOKACIN SANYI:
______
Hasanul-Basariy Yace:
Lokacin sanyi zamini ne na mumini, yininsa bashida tsawo, sai yayi azumi Acikinsa, darensa kuma dogo ne, sai yaita yin ƙiyamul-lali (sallar dare)
-
KASAFTA DARE A LOKACIN SANYI:
______
ABU HURAIRATA YA KASANCE:
Yakan raba darensa gida uku, kashin (1) farko, yayi ƙiyamul-lali, (Sallar dare) kashi na (2) biyu, yayi bacci, kaso na (3) ukun, sai yayi nazarin hadisan Manzon Allah ﷺ.
-
Allah kasa mudace
____
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

23 Nov, 19:04


📚 *Karatun Littafin*


*KITABUT TAUHID*

*كتاب التوحيد*


*Darasi na 045*


Tare da :- *Sheikh Lawan Abubakar Shuaib Triumph (Hafizahullah).*
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

Ranar Alhamis
*19/05/1446=21/11/2024*


*Daga Masjid Qur'an Bacirawa Kano*


🌴 *Ayi Sauraro Lafia.*

*Dan Bada Gudunmawar ka/ki*
👇🏼
0602936955
Arrisalah Foundation
Gt Bank

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

23 Nov, 15:10


🍃 #TUNATARWA
Kar a manta da zikirorin yammaci kariya ne daga shaidanu da wanin su 🌹

Kana kiyaye zikirorin safiya da yammaci don Karin kusanci ga Allah, da kuma kariya daga dukkan abin ki?

Da Ambaton Allah ne #ZUCIYA take samin nutsuwa. Karka kasance cikin Gafalallu, masu mantawa da barin Ambaton Allah.

Allah Ta'ala ya taimake mu yasa mu wanye lafiya🍃

Allah Ta'ala ya bamu iko.

@ZAURENDALIBANSUNNAH

Dalibi Mai Neman ilimi

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

23 Nov, 12:23


🛑ZUNUBI🛑

Ibnul Qayyim(RA) ya ce: "Kar da ka rudu idan ba ka ga tasirin zunubinka ba a lokacin da ka aikata, za ka iya ganin tasirinsa bayan shekara arba'in.

الداء والدواء 130

Allah Ka gafarta mana zunubanmu Ameen.

#Zaurandalibansunnah
DagaZaurandalibanilimi
TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibansunnah

Dalibi mai neman ilimi

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

23 Nov, 11:10


𝐀𝐋𝐁𝐈𝐒𝐇𝐈𝐍𝐊𝐔 MATA GA SIRRI.....................................

"Ba yadda zaiyu ki zama kullum kina cikin hatsaniya da tayarma miji hankali, ba ya jin dadin zama dake, kullum cikin daga masa hankali kike sanann ku zauna lafiya ko ki samu kan sa yadda kike so".

🌻"Tayaya in kun samu matsala zai damu ko in kinyi fushi ya nemi sauqowar ki alhali baya jin dadin zama dake"?
🌻"Tayaya zai yi kewar ki in bakya kusa dashi alhali in kuna tare banda damuwa ba abunda kike sa masa"?
🌻"Tayaya zai nemeki in ya ji ki shuru alhali kullum cikin korafi kike"?
🌻"Tayaya zai so ganin ki in kika nesance shi alhali baya samun nitsuwa a wajen ki"?
🌻"Tayaya zai so ya kusance ki a shimfida alhali da bacin ranki yake wuni"?
🌻"Tayaya zai so ya dawo kusa dake ko ya zauna hira dake alhali ba wani abun nishadi a tattare dake ban da damuwa"?


"Shi namiji in kina son ya nuna damuwar sa in kuka samu dan saɓani, dole ki samar da hanyoyin da zaki sakarta shi, ki nuna damawar ki akan sa, ki bashi kulawa, ki na sashi nishadi da dariya, ki zama abokiyar hira da gulmar sa".

"Wannan zai sa kina dauke wuta zaiji yanayin gidan duk zai sauya masa, zai kasa samun jin dadi dan ya rasa hankali, lokaci da nishadin da kike bashi, ba kulawar da ya saba samu, kin watsar da shi ji zai yi kamar maraya, duk wani tallafi na kulawa an cire masa, dan jin sa da yake kamar sarki kin dawo dashi kamar wani bafade a gidan sa, damuwar sa duk zai zama tayaya zaku shirya, ya zai yi ya shawo kan ki.."

"Nan zakiga ya dan soma kora kunya da 'yar hauka, ya soma lallashin da ba lallai ya bada hakuri ba, za a na kawo miki hirar faɗi ban tambaya ba, baki abunda baki tambaya ba ko kin tambaya an hanaki, kiran wayar da bata da wata dalili, sauraron ki kiyita ranting, sa kan sa abunda baki sa shi ko tambaye shi ba..."

"Wadannan hanyoyi ne duk da yake nuna miki yana son ku shirya, in kika lura da wannan abubuwa alamune da ke nuna yana son ku shirya, ke kuma kar ki tsanan ta, ki sauko bori ya hau ko da kuwa bai budi baki ya bada hakuri ba alamomin duk sun bayyana abunda yake yi kenan".

"In kuma son koya masa bada hakuri kike son yi, bayan kin sauqo ya fahimci kin sauqo, ki ce masa " na fahimci kana son inyi hakuri ne " wadda tabbas zai iya cewa "eh" cikin 'yar shagwaba da tsumewa ki ce "tunda haka ka ke so shikenan zanyi hakuri amma gaskiya sai ka bani hakuri, in ba haka ba kuwa haka zan ta hawa kamar kokon da yayi tsami" tabbas zai yi dariya kuma zai bada hakurin " in ya bada hakurin sai ki ce masa " toh ko dai fa" sai ki sake 'yar tsumewa cike da shagwaba kice "Allah kar a sake min wannan abu, in aka sake kuwa makota ne za su kawo maka ɗauki"

Shi kenan an wuce wajen, gobe ko ya ya soma cikin wasa kice " walle ko a kiyaye ko in haɗama ɗan mutum guguwa a zuciya " nan take zai sauqo cikin wasa.

Amma ki zama kamar wata 'yar tasha baki san yadda zaki bi da kan ki ba balle ki san yadda zaki bi da namiji balle har ki koya masa abunda kike son yayi cikin siyasa, komi ke zaki amshi 'yancin ki, komi fitina, komi da da masifa da tsaniya ake yinta, ba 'yar siyasa, ba wasa, ba komi, tayaya zaki mori zama da namiji.

Ki sani shifa namiji duk yadda yake akwai wacce zata iya sarrafashi in baki iya ba kawai baki iya bane, amma shi ziciyar sa anyi shi yadda mace zata iya sarrafa zuciyar sa duk yadda yake kuwa.

Tare da 🖊Coach Fatimah Chikaire

"Allah Ta'ala yasa mu gane gaskiya ya bamu ikon binta".

Dalibi mai neman ilimi Graphics Designers.

ZAUREN DALIBAN SUNNAH

23 Nov, 11:09


𝐀𝐋𝐁𝐈𝐒𝐇𝐈𝐍𝐊𝐔 MATA GA SIRRI.....................................