*LADUBBAN WALIMA GUDA GOMA SHA BIYAR*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
1:- In an gayyaci Mutum zai je walima to ka niyyaci koyi da sunnah ne, sannan da girmama shi wanda ya gayyaceka.
2:- Kayi Bismillah kafin kafara cin abinci,sannan in ka gama kace Allahamdullih.
3:- Haramunne don ana walima a ci ko a sha da hannun haku.
Saboda fadin Manzon Allah SAW (KADA KU CI DA HANNUN HAGU,DOMIN SHAIDANNE YA KE DA HAGU)
4:- Haramunne cin abinci da zafi,sai dai a ci shi da dumi.
5:- Ba a nunfashi
abin sha.
6:- Ba a son hannuka ya dinga yawo,a cikin kwanon abinci ,abincin iri daya,kuma na cikin jama'a.
7:- Ba a son cin abinci ta tsakiyar kwano,,sai dai ta gefe.
8:- Ba a hura abinci ko busawa.
9:- Ba a cin abinci a kashingide.
10:- Ba a hada dabbino biyu lokaci goda a bakinka,ko duk wani irin abinci mai kwaya, kamar Danwake,doya,dankali,
da daya daya ake ci bada biyu ba sai dai in ka nemi izninsu.
11:- Ba a son adinga sunbatar gurasa,ko borodi,ko kuma ka hulakantatta har ka dinga goge hannunka da ita.
Wannan almubazzaranci
12:- an so in mutum zai ci abinci ci ya ci da yatsu uku.
13:- An so in kana cin abinci sai lomarka ta fadi,ka dauka ka ci,amma in gorin na da tsafta ne.
14:- Mustahabbine in mai walimar yana cin abinci tare da mutane ya fifita wasu akan wasu.
15:- Mustahabbine in ka gama cin abincin walimarka,to ka yiwa shi wanda ya gyaceka addu'a.
*ALBIDAYATUL MUTTAFIQIH* NA _(WAHID BIN ABDUSSALAM BIN BALI)._
_Shifi na 183-185 cikin babin da yake magana akan walima._
Abin da na fada dai dai Allah ya taramu a ladan, ya amfanemu baki daya,wanda nai kuskure Allah ya yafemin da ni naku baki daya .
`
*
📝DALIBARKU,'YARUWARKU A MUSLINCI*
*RUKAYYA AUWAL MUHAMMAD*
02/6/1446
3/12/2024
Domin samun shafinmu na telegram
👇👇👇https://t.me/Ilimantardaalumm