Tarbiyyar Yara
1. Idan kana/kina buƙatar ‘ya’ya na gari, ku zaɓi abokan zama na gari (miji da mata), domin ‘ya’ya photocopy ne na iyayensu. Ka zaɓa wa a ‘ya’yanka uwa, ya fi ka zaɓa wa kanka mata. Kada ka auri fitsararriyar mata, kuma ka ce kana son ‘ya’ya na gari.
2. Ka koyar da ‘ya’yanka karatun addini tun suna ƙanana, domin idan suka girma, ɗawainiyyar rayuwa ba za ta bar su su kai kansu koyo ba. Karatun addini ba ya hana na boko, haka na boko, ba ya hana na addini.
3. Duk makarantar da za ka kai yaronka, sai dai su taya ka ba shi tarbiyya, domin tarbiyya tana ginuwa, tun daga zaɓar iyaye, muhalli, mu’amalar aure, cin halal, haihuwa, rainon yaro zuwa girmansa, wannan kuma duk a hannunka suke.
4. Yaro ya fi kwaikwayon ɗabi’u, mu’amala da salon magana a wajen iyaye, makwabta, abokai da muhallin da ya tsinci kansa fiye da bin umarnin baki (yi kaza, bar kaza). Idan ɗanka yana yawan zagi, ko wata mummunar ɗabi’a, muhalli da ya tashi ne sila.
5. Idan ka ƙi jan yaronka a jiki, zai fi shaƙuwa da abokai a waje fiye da kai, kowanne ɗan Adam yana buƙatar kulawa, nishaɗi da farin ciki. Wannan kuma zai bibiye ka har a tsufa, yaronka za fi ba wa buƙatar abokansa muhimmanci fiye da taka.
6. A wajen bayar da horo, idan kana yawan tadowa da yaronka laifuka ko kuskuren da ya yi a baya, zai koyi ɗabi'ar yawan yi maka karya. ‘Ya’yanka za su zaɓi yi ma ƙarya, saboda gudun faɗa.
7. Idan kana yawan sauƙaƙawa yaronka ƙananan abubuwa (daga shekara 3 zuwa 7), kamar cire masa kaya, ba shi abin ci a baki, yawan ɗaukarsa maimakon a bar shi yana takawa da ƙafarsa, yaron zai tashi da kasala. Yana da kyau a riƙa barin yaro yana yin wasu ƙananan abubuwa da kansa, idan ya yi kuskure, sai a gyara masa.
8. Idan kana yawan yi wa yaro faɗa ko hantara a bainar jama’a, zai daina jin kunyar mutane, koda a cikin gida ne, domin tozarci ne.
9. Idan ana kawo ma ƙorafin yaro kana ƙin karɓa ko kana ba shi kariya, a hankali ɗabi’ar rashin kirkinsa za ta girma, hatta kai ma ba za ka iya hana shi ba.
10. Idan kana yawan ba wa ‘ya’yanka shawara fiye da ƙarfafa masu gwuiwa, hakan zai kashe musu zurfin tunani. Ka riƙa ba su dama suna tunani a karan kansu, ko yin shawara jin me ke cikin ransu, kowa yana da zaɓi.
11. Idan baka bawa yaronka zaɓi, sai dai abin da ka yi niyya, zai koyi ɗabi’ar yawan ɗauke-ɗauke (sata), saboda neman abin da ransa yake so. A wani lokacin, ka riƙa ba wa yaronka zaɓi, Me yake so,? Me zai ci?
12. Idan kana yawan raina wasu mutanen a gaban yaro, shi ma zai tashi da wannan ɗabi’ar, saboda ana ƙasƙantar da wani a gabansa yana gani, ko yana ji. Kar ka nuna masa gidanku ya fi nasu wane, ko kun wuce ajin wasu.
13. Idan kana yawan nuna wa yaro fifikonsa akan wasu, zai tashi da kyashi da hassada, hatta a kan ƙannensa da za a haifa a gaba.
14. Idan baka godewa yaronka ko jinjina masa saboda wata bajinta, zai tashi da saurin fushi, ya yi aikin wahala, ba sakamako.
15. Idan kana son haɗa kan ‘ya’yan tun a yarinta, ka rinƙa haɗa musu abin su ci tare, za ka ga ɗabi’unsu na tausayi, haƙuri, son juna, ko son kai, sai kana daidaita su.
16. Idan yara suka kwace masa abu ya kawo ƙara, kullum kana yawan ba shi haƙuri, zai zama dolo. Ka koya masa jin mulki da mallaka, da jarumta. Idan Ya fita ya jefar da takalmi, ka ce ya je ya nemo, kar ya zama asarari, albozari.
17. Ka riƙa aiken yaro da kyauta zuwa ga ‘yan uwa, ka riƙa zuwa zumunci gidan ‘yan uwa tare da shi, zai tashi da kyautayi da zumunci.
18. Idan ƴarki ta tambaye ki kuɗi, kada kowanne lokaci kina ce wa, je ki wajen babanki, wani lokacin ki rinƙa shiga tsakani.
19. Duk wata ɗabi’a maras kyau, yaro tun yana ƙarami ake hana shi, kar ka ce, AI YARO NE! Idan ya girma da ɗabi’ar, ko kai ba za ka iya hana shi ba.
20. Ka daina yawan furta ‘AI NI ‘YA’YANA BA SU ISA BIJERE MIN BA’ Malam! Tarbiyya na hannun iyaye, amma shiriya ta Allah ce, sai Ubangiji Ya barka da yawonka, da zafin kai, da tsaro, kuma yaro ya bijere. Sai da addu’a!