MAS,ALOLIN DASUKE KARYA AZUMI 04.[ DARASI NA 08 ].
14, baya halatta mutum yahaɗiye kaki ko wani abun dayariga yafito bakinsa, bisa ihtiyaɗi na wajibi.
Idan kuma yahaɗiye ba bisa zaɓinsaba ko bisa Mantuwa azuminsa bai karyeba,
Amma yawun dayake bakinsa bamatsala dan mutum yahaɗiye shi.
15, Anfani da abun fesawa na masu ciwon sarƙewan nunfashi da makamantan sa domin ya buɗa magudanan nunfashi ko sauƙaƙe numfashi ba matsala kuma baya karya azumi.
16, Ɗure da akeyiwa mutum tawajen bayan garinsa ( masu ciwon rashin iya bayan gari ko ciwon ciki .... ) inda abu me ruwa ruwa ne yana karya azumi koda kuwa dole takama ayi hakan.
Amma inda daskarer_rene bamatsala baya karya azumi.
17, Idan Me Azumi yaƙirƙiro amai da gangan azuminsa yakarye,
Kodakuwa dolene tasashi yin aman saboda ciwo ko wani abun daban,
Amma idan yayine bisa Mantuwa kokuma kuskure ba bisa zaɓinsaba azimin sa bai karyeba.
18, bisa ihtiyaɗi na wajibi ; Wajine ma azumi yanisanci Anfani da Allura me ƙara ƙarfin jiki dama wasu abubuwan da,ake sawa ta jijiya hakanan ruwan asibiti ( Drip ) da dukkan nau,o'insa.
Amma Allura Da akeyi bana jijiyaba saboda jinyan rashin lafiya bata karya azumi haka alluran dake kashe zafin wajen da za ayi ɗinki ko aiki itama bata karya azumi.
19, Bamatsala mutun yanaķalto Ruwayoyin dasuzo daga Manzon Allah (s,a,w) ko iyalan gidansa wanda aka rawaitosu a littatafai wanda mutum baida masaniya akan cewa ķarya akayiwa ma,asumi.
Dukda cewa bisa ihtiyaɗi na Mustahabbi mutum yajingina ruwayan zuwaga littafin daya dauko aciki baya jinginawa ma,asumi kai tsayeba.
20, Idan Mutum yanaƙalto magana yajinginawa Allah (s,w,t) ko Manzon Allah (s,a,w) ko wani daga cikin ma,asumai, yanada Qudurin cewa ya inganta, sedaga baya seta bayyana masa cewa bai ingantaba azuminsa bai lalaceba.
21, wajibine mutum mai azumi yanisanci haɗiye ƙura mai kauri, bisa ihtiyaɗi na wajibi,
Kamar ƙuran dake tashi lokacin Shara ko kuma wanda iska ke tayarwa,
Idan Mutum bai nisanci ƙuran ba har yashige maƙogoronsa to azuminsa yakarye bisa ihtiyaɗi na wajibi.
22, Idan Mutum yamanta cewa yana azumi sai bai nisanci ƙuraba har yashige maƙogoron sa Azumin sa bai lalace ba,
Haka hukuncin yake Idan ƙuran yashige batareda zaɓinsaba.
23, Haɗiye Jinin daya fito daga dasashi ( dasori ) Baihalatta,
Wajibine mutum yatofar dashi, yana tofarwa kuma bakinsa ya tsarkaka ba dole saiya kurkureba,
Amma wannan Idan yazama jinin bai ɓace acikin yawuba kenan - ta yadda baza,aganshiba inda za atofar da yawun - amma idan yaɓace acikin yawuto ya tsarkaka ya halatta ahaɗiyeshi kuma Azumin mutum bai ɓaciba.
23, Bamatsala Mutum yatsaftace bakinsa da makilin da buroshin, matuƙar mutum bai haɗiye wani abu da gangan ba.
Jiƙa jiki da ruwa tahanyan shiga cikinsa ko she ƙashi akan mutum ko wanka a ƙarqashin shaya duk basu ɓata azumi.
✍ Abdullahi Dahiru
https://t.me/TAMBAYAMABUDINILIMI
Sheikh Abdullahi Dahiru 📚

Koyon Larabci, Ilimin Sarfu, Nahawu, Balagha Dakoyon Rubutun Larabci, .....
Kasance Da Wannan Shafi Dayardan Zaisamu Abunda Yake Buqata.
کانالهای مشابه



Sheikh Abdullahi Dahiru: Jagoran Ilimi a Fannin Addini da Harshe
Sheikh Abdullahi Dahiru na daya daga cikin manyan malaman addini a Najeriya, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen bayar da ilimi mai inganci ga matasa a fannoni da dama. Tare da tsawon shekaru na koyarwa, Sheikh Abdullahi ya zamo sanannen malami a fannonin Fiqihu da Aqida, wanda ya shahara wajen koyar da ilimin Larabci da sauran zamantakewa tare da hanzarta koyo da kuma koyarwa. A cikin wannan makala, zamu duba irin tasirin da Sheikh Abdullahi ke da shi a cikin al'umma da kuma yadda yake taimaka wa matasa wajen samun ingantaccen ilimi. Hakanan, za mu yi la’akari da wasu daga cikin tambayoyin da mutane ke yi game da iliminsa da hanyoyin koyarwarsa, domin samar da karin haske ga masu sha'awar wannan fanni.
Menene Fiqihu, kuma me ya sa yake da muhimmanci a cikin ilimin addini?
Fiqihu yana nufin ilimin shari'a na Musulunci wanda ke tantance dokokin da suka shafi rayuwar al'umma. Wannan fanni yana da matukar muhimmanci saboda yana ba da damar fahimtar abin da ya dace a yi ko a guje wa a cikin al'amuran yau da kullum, daga ibada har zuwa mu'amala. Malamai kamar Sheikh Abdullahi Dahiru suna taka muhimmiyar rawa wajen bayyana wannan ilimi ga al'umma, ta yadda zasu iya gudanar da rayuwarsu bisa ga koyarwar addini.
Haka kuma, Fiqihu ya na da matukar tasiri wajen karfafa zaman lafiya a cikin al'umma. Lokacin da mutane suka san hakkin su da wajabinsu a cikin shari'a, hakan na taimakawa wajen rage rikice-rikice da tasiri mai kyau a cikin al'umma. Malamai kamar Sheikh Abdullahi suna da rawar da suke takawa wajen ilmantar da mutane, ta hanyar shirya taruka da koyar da dakin karatu.
A wane fanni ne Sheikh Abdullahi Dahiru ke bayar da horo a ilimin Larabci?
Sheikh Abdullahi Dahiru yana bayar da horo a fannin ilimin Larabci wanda ya hada da nahawu, sarfu da balagha. Koyon Larabci yana da matukar muhimmanci ga wadanda suke son samun ingantaccen ilimi game da addinin Musulunci, domin yawancin littattafan ilimin addini, da hadisi, da Qur'ani ana rubuce su ne cikin harshen Larabci. Hakan ya sa Sheikh Abdullahi ke ganin bukatar koyar da wannan fanni ga matasa da kewayen gidajen karatu.
Hakanan, ilimin Larabci yana ba da damar samun fahimta mai zurfi game da koyarwar addini da al'adun Musulunci. Malamai kamar Sheikh Abdullahi suna kira ga matasa da su rungumi ilimin Larabci a matsayin hanya ta cimma zurfafa fahimta a fannonin addini da zamantakewa, wanda hakan zai inganta rayuwarsu.
Ta yaya Sheikh Abdullahi ke taimaka wa matasa wajen samun ingantaccen ilimi?
Sheikh Abdullahi yana nuna himma wajen zayyana shirye-shiryen horo da za su taimaka wa matasa wajen samun ingantaccen ilimi. Ya na shiryawa matasa karatuttuka, inda suke koyon muhimman darussan addini da na zamantakewa. Haka ne ma, yana ba da damammaki ga matasa su shiga cikin dandalin tattaunawa inda zasu iya tambayar duk abin da ke damunsu ko kuma samun karin bayani kan abubuwan da suka koya.
Bugu da kari, Sheikh Abdullahi yana amfani da kafafen sada zumunta wajen yada ilimi da shawarwari ga matasa. Hakan yana sa su iya samun ilimi daga ko ina cikin duniya. Ta wannan hanyar, ana kara fadada yawan matasan da suka shafi karatun addini da ingantaccen ilimi na zamani.
Me yasa koyon Larabci ke da matukar muhimmanci ga muslmi?
Koyon Larabci yana da matukar muhimmanci ga Musulmi saboda harshen Larabci ne aka rubuta Qur'an da Hadisai. Samun ilimin Larabci na ba Musulmi damar karanta da fahimtar ayoyin Qur'ani da Hadisai a asalin harshensu, wato tare da hakikanin ma'anoni. Hakar tana ba da haske da inganci wajen gudanar da ibada da sauran al'amuran rayuwa.
Haka zalika, koyon Larabci yana taimaka wa Musulmi su fahimci al'adun Musulunci da kuma tsarin rayuwar da aka gina bisa ga shari'a. Wannan yana karfafa alakar Musulmi da addininsu da kuma ba su damar gudanar da al'amuransu cikin tsari daidai da koyarwar addini.
Menene Aqida, kuma ta yaya take shafar rayuwar Musulmi?
Aqida na nufin imani a cikin Allah da abubuwan da suka shafi addini. Wannan yana dauke da akidun da suka shafi imani, kamar imanin da ga Allah, mala'iku, littattafai, annabawa da ranar lahira. Aqida tana daga cikin ginshikan addinin Musulunci, kuma tana da matukar tasiri kan yadda Musulmi ke gudanar da rayuwarsu.
Rayuwa ba tare da Aqida ba na iya haifar da rudani da rashin tabbas a cikin al'umma. Malamai kamar Sheikh Abdullahi suna daukar nauyin ilmantar da matasa kan Aqida, don su sami tushen da ya dace na addini wanda zai ƙarfafa musu gwiwa da kuma juriya a dukkan fannonin rayuwarsu.
کانال تلگرام Sheikh Abdullahi Dahiru 📚
Tambayamabudinilimi channel, managed by Sheikh Abdullahi Dahiru 📚, is a treasure trove of knowledge for those interested in learning about various aspects of Islamic studies. From Fiqh and Aqida to Arabic grammar, language, rhetoric, and writing, this channel covers a wide range of topics essential for anyone seeking to deepen their understanding of the Islamic faith and its teachings. Whether you are a beginner looking to start your journey in Islamic education or an advanced student wanting to enhance your knowledge, Tambayamabudinilimi has something for everyone. Join us on this enlightening journey as we explore the depths of Islamic knowledge and learn from the wisdom shared on this platform. Don't miss out on this opportunity to expand your horizons and grow in your faith. Kasance Da Wannan Shafi Dayardan Zaisamu Abunda Yake Buqata!