GIDAN DA ALLAH YA DAUKAKA
Maharan da suka kai hari gidan Sayyida Zahara (S.A) suna sane da fadin Allah cikin Qur'ani, in yace :
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَدْخُلُوا بُيُوتًا غَيْرَ بُيُوتِكُمْ حَتَّىٰ تَسْتَأْنِسُوا وَتُسَلِّمُوا عَلَىٰ أَهْلِهَا ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَكُمْ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
Ma'ana:
"Kada ku shiga gidajan da ba gidajan ku ba, sai kun samu izini kunyi sallama ga mutanan gidan, Wannane mafi alkhairi gare ku ko zaku tuna."
Anan mahara ba subi umurnin Allah ba na neman izinin shiga gidan 'diyar Manzon Allah (S.A) ba.
Ta wani bangaran kuma gidan Sayyida Zahara (S.A) na da matsayi da babu wani mutum a doron kasa da ke da ikon shiga ba tare da neman izini ba. Allah ta'ala cikin suratul Ahzab, aya ta 35, yace:
يا أَي هَُّا الَّذينَ آمَنُوا ل تَ دخُلُوا ب يُوتَ النَّبِيِّ إِل أَ ن ي ؤذَنَ لَكُم
Ma'ana:
"Yaa ku wa'danda sukayi Imani! Kada ku shiga gidajan Annabi, sai an baku izini..."
Ba shakka gidan Sayyida Zahara (S.A) na jerin gidajan Annabi da Allah ya hana shigan sa batare da izini ba, wannan kuwa yazo cikin littafan tafsirin Sunnah da Shi'a, karkashin tafsirin ayar da Allah ke cewa:
فِى ب يُوتٍ أَذِنَ اللَّو أَن تُ رفَعَ وَ يُ ذكَرَ فِيهَا ا سمُو يُسَبِّحُ لَو فِيهَا بِال غُدُوِّ وَا لَْصَالِ
Ma'ana:
"A cikin wasu gidaje da Allah yayi umurnin a daukaka kuma a ambaci sunan sa a cikin su, Suna Masa tasbihi a cikin su, safe da maraice."
Malam Suyu'di da wasu Malamai sun ruwaito ruwaya daga Manzon Allah (S.A) cewa, Gidan Imam Ali da Fatima (S.A) yana cikin manya manyan gidajan Manzon Allah (A.S):
Ibn Mardawaih ya ruwaito daga Anas bin Malik da Buraida cewa:
"Manzon Allah (S.A) Ya karanta ayar 'A gidan da Allah ya umurta a daukaka...' sai wani ya tambayi Annabi cewa: Wadanne gidajene wadannan da Allah ya umurta a 'daukaka? Sai Manzon Allah (A.S): 'Gidajan Annabawa.' Sai Khalifa Abubakar ya nuna gidan Ali da Fatima yace: 'Wannan gidan na ciki?' Sai Manzon Allah ya amsa masa yace: 'Ei, Yana cikin Mafi girmansu.'
Madogara:
-Al-Suyuti, cikin littafin Durrul Manthoor, jildi na 6, Shafi na 203.
-Al-Tha’labi An-Nishaburi, cikin Al-Kashif Wal-Bayan, jildi na 7, Shafi na 107
-Al-Tha’alibi, cikin tafsirin sa Tafsirul Jawahirul Hisan, jildi na 7, Shafi na 107.
-Aloosi, cikin Tafsirul Roohul Ma’ani, jildi na 18, Shafi na174.
Wannan shine gidan da Mahara suka kaiwa harin ta'addanci suka kone shi duk da masaniyar su da matsayin gidan koda kuwa mutanan gidan basu da daraja a idanun su. Suna sane da cewa Fatima, Mijin ta da 'Ya'yanta na ciki. Wasu daga cikin maharan sun canza ra'ayi bayan jin maganar Sayyida Zahara (A.S), kamar yadda Malam Dinawari, ya kawo cikin littafin sa Imama Was-Siyasa, jildi na 1, Shafi na 16, cewa:
"Lokacin da Umar bin Khaddab da jama'ar sa suka isa gidan Fatima. Sun kwankwasa kofar gidan, sai sukaji muryar Fatima tana kuka tace: 'Yaa manzon Allah! Wanne irin tsananin cutarwa ne wannan muke fuskanta daga 'dan Khattab (Umar) da 'dan Abu Quhafa (Abubakar) bayan rayuwar ka.' da wasu cikin jama'ar suka ji kukan Fatima, Sai suka canza ra'ayi kwalla na fitowa daga idanun su suka bar wajan cikin damuwa. Amma duk da haka Umar da wasu jama'an suka tsaya."
Yaa Jama'a, Wanne Laifi 'diyar Manzon Allah (S.A) ta yiwa Al'umma bayan rayuwar sa Mai albarka!!
Yaa Ubangiji ka shaida Mun yi Bara'a ga dukkanin wanda ke da hannu wajan kone gidan Sayyida Zahara (S.A).
Yaa Ubangiji Allah, Ka zamanto majibinci, garkuwa, shugaba, mataimaki, mai shiryarwa da kuma nuna hanya ga Waliyinka, Al-Hujjat dan Al-Hasan, tsira da amincinka su tabbata a gare shi da kuma iyayensa, a wannan lokacin da kuma dukkanin lokuta har ka tabbatar da shi doron kasarka yana mai maka biyayya da kuma tabbatar da shi na tsawon lokaci.
#JATJ
#AlfatihaZuwaGaRuhinSheikhAdamuTsoho
https://t.me/JawadAdamuTsoho