"Babu wani Annabin da bai yi nasara ba. Aikin Annabi shi ne isar da saƙo... Kafa Daula Musulma da iko, in wannan shi ne nasaran Annabi, to da yawan Annabawa ba su yi nasara ba, don su ba su kafa daula ba. Har Abul-Anbiya Ibraheem (A.S) bai kafa Daula ba, amma manufarsa kenan kafa daula ɗin ko da bai kafa ba. Haka nan kuma kowane Annabi ko da bai kafa daula ba, manufarsa (da hanƙoronsa) kenan ya kafa daula ya zama al'umma ta ɗauru a kan koyarwar addini. Al'umma ta ɗoru a kan koyarwar addini, wannan wajibi ne."
#SHEIKHIBRAHEEMZAKZAKY(H) | 24th, Rabi'us Sani. 1446 - 27th, Oct. 2024
#Islam #IslamulMuhammady #SidiZakzaky #Nigeria
📱 https://whatsapp.com/channel/0029VaCAJv2EwEjrsx6pUS20