Ko akan wadannan abubuwan 5 kadai mutum yaje ya kware; indai a Technical Analysis ne to ya kusa gama Secondary School Level a Trading😊.
_______
D'abi'ar farashi a yanayin tafiyarsa shi ake cewa "Price Action" a Crypto da sauran Financial Markets.
Kwararrun Traders suna anfani da ilimin sanin Price Action wajen yin Trading. Kamar kaine idan ka laƙanci d'abi'ar mutum zaka iya hasashen abinda zai iya yi.
💎 In sha Allahu yau zamu tattauna ne a takaice akan wadannan ;
1. Zones/Gurare 5 da idan Price yaje gurin yake juyowa (ya tashi ko ya fadi) a mafi yawan lokuta.
2. Me yasa haka take faruwa a irin wadannan guraren.
3. Yau she ne guraren suke aiki yaushe ne ba sa aiki.
Wadannan abubuwan zasu taimaka mana sosai wajen gane guraren da ya kamata mu shiga ko mu fita daga Trade. Wanda bai san Basics a T.A ba Wannan rubutun ba nasa bane a yanzu gaskiya sai dai a nan gaba.
💎 1. Support and Resistance Level: Mostly Idan Price yazo Support ko Resistance yana juyawa.
- Hakan tana faruwa ne saboda Order Flow da ake samu daga sauran Traders saboda suma duk suna da idear cewa guri ne da Price yake reacting.
- Hakan tana faruwa ne saboda Market Sentiment, buyers suna ganin saukin Price a Support sai hakan ya jawo Demand =(Tashin Farashin) , a Resistance kuma Sellers suna ganin price yayi daraja yanda ya kamata dan haka bari su siyar suyi Taking Profit sai hakan ya jawo Supply =(Faduwar Farashin) .
- S/R suna aiki ne idan ya zama akwai Volume me karfi a gurin, idan kaga an zo level din amma ba'a samu wani Bounce me karfi ba to zai yi wahala level din yayi aiki, hakan yana nufin za'a iya breaking dinsa a wuce cikin sauki.
- S/R sunfi yin aiki idan ya zama cewa Price yayi Testing level din fiye da sau daya IDAN a "Ranging Market" ne, idan akazo jikin Level aka dinga Testing dinsa hakan yana nuna rashin karfinsa ne saɓanin daga zone zuwa zone akayi testing din.
- Ba'a saurin shiga kasuwa a S/R Level har sai an samu Confirmations saboda guri ne da ake yawan samun "FakeOut" saboda Targeting Liquidity da Market Makers suke yi. Nayi bayanin ma'anar Liquidity a Support and Resistance kwanaki.
💎 2. Trendline (Dynamic Support and Resistance) : Trendline yana aiki ne as Dynamic S/R kuma shima ana anfani dashi wajen gane gurin da Price zai juya, duk bayanan da nayi a sama awajen Support and Resistance sune anan, ba sai mun maimaita ba.
- Abunda kawai zan iya karawa anan shine Trendline yafi yin aiki idan mutum yana kula da Primary da kuma Secondary Trend, ma'ana Trend din Higher TimeFrame da kuma na Lower TimeFrame, saboda Correction din Higher TF Clear Trend ne a Lower TF.
💎 3. Supply and Demand Zones/ Order Blocks : Suma gurare ne da Price yake juyawa idan yazo. Sannan gurare ne da idan aka same su a karon farko ma'ana aka samu sabon zone to Price yana komawa yayi Retesting dinsu.
- Hakan tana faruwa ne saboda Large Order Flow da ake samu a gurin daga Market Makers sai Price ya tafi da sauri ba tare da Traders sun gama shigar da kudade ba, ma'ana an bar Orders dayawa ba'a yi executing ba, to idan ya dawo gurin sai a kara sabon lodi na Orders din can da aka bari da farko sai acigaba da tafiya. Anan gurin ma fahimtar "Dominant Pressure" din nan da mukayi last week zai yi anfani sosai da sosai.
- Suna aiki ne idan aka zo testing dinsu a karon farko wato a sanda suke "Unmitigated", saboda a lokacin ne ake kara loda kudade/orders da basu samu shiga ba a tafiyar farko.
- Supply and Demand/Order Block basa yin aiki sosai idan aka riga aka yi testing dinsu suka zama Mitigated sbd babu sauran Volume/Orders a gurin da zai sa su juyar da Price .
Secret🤫 : Indai aka samu "Drop Base Drop" na Supply ko "Rally Base Rally" na Demand to sai kasuwa ta koma baya tayi testing din at least Recent Supply/Demand Zone kafin ta cigaba da tafiya. Pin it!.
💡Idan mukayi nazari akan Supply and Demand Retest da kuma Trendline za muga kusan abu daya ne yake faruwa, kawai Trendline kamar zanen Chain ne na S/D Retest dan saukaka fahimta amma babu wani banbanci.