HADISAI GAME DA MATSAYIN AIKIN UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI GA MUMMUNA (HISBAH) DA KUMA KWAƊAITARWA AKAN AIKIN
HADISI NA TALATIN DA DAYA(31)
Daga Abu Sa’idin (R.A) ya ce: Wata rana Annabi (S.A.W) yayi mana wata Huɗuba bayan Sallar La’asar har zuwa lokacin faɗuwar rana (Bai bar wani abu da zai faru ba sai da ya bamu labari , tun Daga lokacin sa har zuwa tashin Alƙiyama) wasu daga cikin mu sun haddace, wasu kuma basu iya kiyayewa ba, a cikin huɗubar; Ya fara da yin godiya ga Allah, sannan ya yabeshi, sai yace: “Bayan haka: Haƙiƙa duniya yabanya ce me ƙayatar wa, da ke cike da kayan morewa, kuma lallai Allah zai ara muku rayuwa a duniya don ya ga yadda ayyukan ku za su kasance, don haka ku saurara kuji; Ku kiyayi ruɗun duniyar nan, kuma kuji tsoron makircin Mata, ku saurara kuji; haƙiƙa ƴan Adam an halicce su ne kowa da irin matsayin sa, wasun su an halicce su a muminai, kuma zasu rayu suna masu imani, sannan su mutu muminai, wasun su kuwa an halicce su a kafirai, kuma za su rayu a kafirci, sannan su mutu a kafirai, wasun su an halicce su a muminai, kuma zasu rayu suna masu imani, amma sai su mutu a kafirai, wasun su kuwa an halicce su a kafirai, kuma zasu rayu a kafirai, amma sai su mutu a muminai, Ku saurara kuji; shi fushi tamkar wani garwashin wuta ne da ake rurashi a cikin cikin ɗan Adam, shin baku ganin yadda idanun mai fushi ke yin ja da kumburar jijiyoyin wuyan sa? Idan ɗayan ku ya shiga irin wannan yanayi, ya yi sauri ya zauna a ƙasa, ku saurara kuji; haƙiƙa mafi Alherin Mutane shi ne wanda bai da saurin fushi, mai saurin yarda da haƙuri, kuma mafi sharrin Mutane shi ne mai saurin fushi, mai karancin haƙuri da ƙin yarda idan an saɓa masa, Amma idan Mutum ya zama baida saurin fushi kuma baida saurin haƙura ko kuma mai saurin fushi kuma mai saurin haƙ ura, to wannan ba yabo ba fallasa kenan. Haka kuma idan mutum ya zama baya saurin fusata kuma baya saurin haƙura to shi ma ba yabo ba fallasa kenan. Ku saurara kuji; Lallai mafi Alheri a cikin ƴan kasuwa shine mai sauƙin biyan bashi, mai sauƙi wajan bin bashi, kuma mafi sharrin ‘yan kasuwa shine mai taurin biyan bashi, fitinanne in yana bin bashi, amma wanda ya zama mai sauƙin biyan bashi, amma fitinanne in yana bin bashi, ko kuma mai taurin biyan bashi, amma mai sauƙi wajan bin bashi, to waannan ba yabo ba fallasa kenan, Ku saurara kuji; tabbas ko wanne mayaudari maciyin Amana yana da tuta ranar alkiyama, ko wannen su gwargwadon girman yaudarar da yayi gwargwadon girman tutar sa, ku sani; Lallai mafi girman cin amana ita ce cin amanar Shugaba ga Al’ummar sa, ku saurara; kada tsoron Mutane ya hana wanin ku ya faɗi gaskiya in har ya santa, Ku saurara; Lallai mafificin Jihadi shine faɗar gaskiya a gaban azzalumin shugaba...” Can da yamma rana ta kusa fadawa sai yace: “Lallai kwatankwacin abinda ya rage a wannan Duniyar daga abin da ya wuce na shekarun ta, shine kwatankwacin abin da ya rage a wanna ranar ta yau daga yinin ta”.
TIRMIZI
DARUSSAN DA KE CIKIN WANNAN HADISI:
1 – Ƙoƙarin Annabi (S.A.W) wajan koyar da sahabban sa Alkhairi dan su aikata shi da sharri dan su ƙaurace masa.
2 – Fatan yin kyakkyawan ƙarshe a rayuwar duniya domin ba wanda yasan yadda ƙrshen sa zai kasance.
3 – Muhimmancin danne fushi da yin sassauci ga waɗanda kake cinikayya ko rayuwa tare dasu.
4 – Falalar faɗar gaskiya da tabbatar da ita ga shugabanni da Al’umma baki ɗaya – Yin hakan daidai yake da yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.
5 – Tunatarwa game da kusantowar Alƙiyama.
#Ihtisab #hadisai130 #Mugyara
https://youtu.be/vjs3YpK-FIQ?si=QYQfDmcjO5_e-klB
TELEGRAM:
https://t.me/naseehafoundation
WHATSAPP;
https://whatsapp.com/channel/0029VaArvyV0rGiDM3nbrW1e
#Naseehafoundation mu taru mu gyara domin mu gudu tare mu tsira tare.