Daarul Hadeethis Salafiyyah Liddiraasaati Wal Abhaath Zaria Najeriya.

@cibiyarhadeethinsalafiyyah

Understanding Sunnah According to the Salaf (Pious Predecessors of Islaam).

Daarul Hadeethis Salafiyyah Liddiraasaati Wal Abhaath Zaria Najeriya.

19 Oct, 08:50

Cigaba da Karatun NAZMUL WARAQAAT

Daarul Hadeethis Salafiyyah Liddiraasaati Wal Abhaath Zaria Najeriya.

17 Oct, 14:22

Mai Suna :

Sheikh Bashir Bello Assalafy Zaria

Daarul Hadeethis Salafiyyah Liddiraasaati Wal Abhaath Zaria Najeriya.

17 Oct, 14:22

Zaka iya samun damar Sauraron karatun a saukake Live Broadcast Ta Manhajar Facebook.

Daarul Hadeethis Salafiyyah Liddiraasaati Wal Abhaath Zaria Najeriya.

14 Oct, 22:11

Karatun SHU'ARAA'UL JAAHILIYYAH.

Daarul Hadeethis Salafiyyah Liddiraasaati Wal Abhaath Zaria Najeriya.

14 Oct, 11:00

SAYAR DA KAYA ONLINE

Daarul Hadeethis Salafiyyah Liddiraasaati Wal Abhaath Zaria Najeriya.

13 Oct, 22:45

ALLAAHU AKBAR...!!! 💓

Waɗannan Bayin ALLAAH da kuke ganin Hotonsu a ƙasa. Mutanen Gazza ne a wani yankin Mai suna : "KHAN YUNUS ". A Yanzu ana cikin yaƙi da Yunwa, ga Firgici da Tashin Hankali ; Amma suna ta yin Karatun Sunnah abinsu a Fiqhush Shari'ah. cikin Littafin AL'IMAAMU IBNU QUDAAMAH AL'MAQDISIY. RAHIMAHULLAAH mai Suna "UMDATUL FIQHI"

Madallah da wannan Himmar kuma ALLAAH ya saka Masu da Alkhairi. A irin wannan yanayin ne AL'IMAAMUL BAGAWIY. RAHIMAHULLAAH ya Rubuta Littafinsa Mai Suna "SHARHUS SUNNAH".

Ɗaliban ilimi a dage Sosai wajen Himma a Fagen Neman Ilimi. Babu kasala, babu Nawa, babu Wasa da Harkar ilimi.
Baka da wani Uzuri ko kaɗan da zaka ce Shine dalilin rashin Neman iliminka a yau.
Abubuwan da suke hana Neman ilimi.
01.Facebook
02. What's App
03. Rashin Ikhlaasi wato Tsarƙin Zuciya wajen Neman ilimi.
04. Rashin Manufa Neman ilimi
05. Rashin Malami Na ALLAAH Mai Tarbiyyah da Tarbiyyantarwa.

Idan Mutanen da suke Gazza zasu duƙufa wajen Neman ilimi inaga ni da kai. Baka da wani Uzurin zama da Jahilci Ɗan Uwa.
ALLAAH yasa Mu dace da Alkhairi.

Daarul Hadeethis Salafiyyah Liddiraasaati Wal Abhaath Zaria Najeriya.

10 Oct, 22:35

A wannan halin da al'ummar wannan ƙasa suke ciki dama sauran ƙasashen musulmai ahir ɗinka da kare azzulmai da ƙoƙarin ba su uzuri da mafaka, da ma yi wa wani fata ko murnar samun wani matsayi a cikinsu. Don kuwa duk muguwar addu'ar da ake musu, da kuma zaluncin da suke yi to kana da kaso a ciki.

Abubakr al-Mirwazi ya ce lokacin da aka ɗaure Ahmad bn Hanbal, sai mai gadin kurkukun ya tambayesa : Shin hadisin da aka ruwaito game da azzalumai da masu taimaka musu sahihi ne?" Sai Imam Ahmad ya ce: "Eh." Mai gadin kurkuku ya ce: "To, shin ni ina daga cikin masu taimaka wa azzalumai ?" Sai Imam Ahmad ya ce: "Masu taimaka wa azzalumai su ne masu aske maka gashinka, masu wanke maka kaya, masu dafa maka abinci, masu saye da sayarwa da kai, amma kai kanka kana daga cikin azzalumai."

Iya wannan kaɗai ya isa nuna maka hatsarin azzalumi da taimakonsa.

Allah ya sassauta mana ya kuma yi mana maganin azzalumai a duk inda suke.

Daarul Hadeethis Salafiyyah Liddiraasaati Wal Abhaath Zaria Najeriya.

06 Oct, 11:06

TAMBAYA AKAN RABON GADO

Daarul Hadeethis Salafiyyah Liddiraasaati Wal Abhaath Zaria Najeriya.

06 Oct, 11:04

Audio from Bashir Bello Assalafy

Daarul Hadeethis Salafiyyah Liddiraasaati Wal Abhaath Zaria Najeriya.

06 Oct, 11:04

Audio from Bashir Bello Assalafy