JANABA DA HAILA [ 02 Darasi Na 09]
6, Yahalatta ga mai azumin da janaba tasameshi yayi bacci idan yana tsammanin cewa zai farka cikin dare yayi wanka,
Idan yayi bacci da niyyan zai tashi sai yamaka bai tashiba sai bayan fitowan Alfijir azuminsa ya inganta kuma bakomai akansa.
Amma Inda zaifarka cikin dare saiyaga cewa da sauran lokaci saiya koma bacci karona Biyu saibai farkaba har saida Alfijir yaketo, To wajibine yakame harzuwa shan ruwa, sannan daga baya zai biya wannan Azumin.
7, Wanda Janaba tasameshi Ko macensa haila yadauke mata saidai bazasu iya wankan tsarkiba saboda gudun ruwan zai cutar dasu kokuma babu ruwan, kokuma lokaci yaƙure ta yadda lokacin daya rage bazai isheshi wankaba, wajibine suyi taimama maimakon wanka,
Inkuma Mutum baiyi taimaman ba har Alfijir yaketo to bashida azumin wannan ranan kuma wajibine yakame a wannan ranan, sannan zai biya bashin wannan Azumin Bayan sallah kuma sai yayi Kaffara idan a watan Ramadanne.
8, Idan Mutum yana wankan tsarki da tunanin cewa wankan dayakeyi Ingancec_ce ne,
Saidaga baya tabayyana masa cewa ba daidai bane wankan dayakeyi, Azumin dayayi abaya ya inganta, saboda wanzuwansa da janaba badagangan bane,
Amma sallolinsa dayayi abaya wajibine yabiyasu dukka.
9, Idan Mace tamanta da wankan haila ko wankan nifasi na wani lokaci, sai daga baya ta Tuna, to azumin datayi tsawon wannan lokacin ya inganta, Babanbanci azumin Ramadanne ko wani azumin daban.
10, Idan Mutum yasan cewa idan yakusanci iyalinsa cikin azumi bazai iya wankaba saboda baruwa ko saboda wani uzurin nadaban, ya halatta duk da haka yakusanci iyalinsa sai yayi taimama maimakon wanka,
Amma idan baiyi taimamaba har Alfijir ya keto azumin sa ya lalace kuma dole yakame wanann ranan sannan bayan sallah zai biya wannan Azumin Kuma zaiyi Kaffara.
11, Idan Me azumi dagangan yayi wani abunda yasan cewa zai tayar masa da sha awa har Maniyyi yafita, kamar kallon ko taɓa abunda zai harfar da hakan koma wani abun daban, to azuminsa ya lalace.
12, Idan mai azumi yayi wanin daniyyan ya fidda Maniyyi, to koda Maniyyin bai fitaba zai qarisa wannan ranan kamar sauran masu azumi kuma zai biya wanann azumin bayan sallah bisa ihtiyaɗi na wajibi.
13, Idan mai azumi yafarka lokacin da baniyyi ke fita ajikinsa, bawajibi bane ya hanashi fita.
14, Idan Janaba tasamu mai mazumi ko yayi mafarki da Daddare, yaƙi wanka da gangan har lokacin wanakn yaƙure, Wajinine yayi taimama maimakon wankan, kuma zumunsa ya inganta, amma ya aikata haramun saboda rashin wankan dayayi.
14, Idan haila ko nifasi yabijirowa mace lokacin azumi acikin yini - bayan ketowan Alfijir ko da rana ko da yamma - azuminta ya lalace koda kuwa kafun Magriba ne da ƴan mintoci ne, zata biya wannan Azumin Bayan sallah,
Amma tabbas Allah zai bata ladan wannan azumi da tayi wanda bata samu daman ƙarisashiba.
✍ Abdullahi Dahiru
Shiga nan domin samun audio na karatun 👇
https://t.me/TAMBAYAMABUDINILIMI