NASEEHA FOUNDATION

@naseehafoundation


Working assiduously to inculcate good conduct and eradicate immoralities in all facets of the society by way of beautiful approach and continous improvement.

NASEEHA FOUNDATION

22 Oct, 18:10


DAURAR MATA A YANAR GIZO

{A cikin ku lallai a samu wata al'umma waɗanda suke kira zuwa ga alheri, kuma suke kira zuwa ga kyakkyawa kuma suke yin hani daga mummuna.....} [Al'imran:104]

Shin kina son ki zama ƙwararriya a kan aikin umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna da yanda za ki mu'amalanci mutane gurin yin umarni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna? To albishirinki, ga dama ta samu.

Cibiyar An-Nasiha ta shirya DAURA ta kwana biyu a yanar gizo ga ƴan uwa mata mai taken:

مسائل  وقواعد في الاحتساب

MAS'ALOLI DA ƘA'IDOJIN UMURNI DA KYAKKYAWA DA HANI DAGA MUMMUNA.

MASU GABATARWA:
🔸️Malama Fatima Dawud      
🔸️Malama Ruƙayya Badamasi

RANA: Litinin da Talata
28-29/10/2024

LOKACI: 8:00pm zuwa 10:00pm

Wuri: Shafin Naseeha Foundation na mata da ke a Telegram.

Link👇

TELEGRAM
https://t.me/+WqQ8bcAfsJ4yZjVk

NASEEHA FOUNDATION

15 Oct, 19:55


MUSABAƘA TA MUSAMMAN A KAFAR SADARWA, WANDA DUK YA SAMU NASARA A MUSABAƘAR ZA A BA SHI KYAUTAR KATIN KIRAN WAYA NA NAIRA 1500

SHIGA NAN DOMIN YIN MUSHARAKA👇

https://www.facebook.com/100072481787150/posts/pfbid02zUKLAPXCqTeTZnvtQaZF8PAUp4NyB2b6M3JfYwMrTcm7tz1ePHHYEXvXsgMPCsk1l/

NASEEHA FOUNDATION

14 Oct, 20:00


"IDAN NAGARI SUKA YI RIKO DA HANNUN MASU ƁARNA, SAI SU TSIRA BAKI ƊAYA".

Cibiyar Naseeha ɓangaren mata na farin cikin gayyatar ƴan uwa mata halartar lacca da ta saba shirya musu duk wata mai taken:

SAƁAWA IYAYE

Mai gabatarwa: Malama Ruqayya Tijjani

Rana: Alhamis 17th/10/2024

Lokaci: Ƙarfe Takwas da rabi na dare(8:30pm)

Wuri: Shafin Naseeha Foundation na mata da ke a Telegram.

Link👇

TELEGRAM
https://t.me/+WqQ8bcAfsJ4yZjVk

NASEEHA FOUNDATION

09 Oct, 21:49


https://youtu.be/Cxx7fIUkWN4?si=0YOgBXBBNrFJvrBy

NASEEHA FOUNDATION

09 Oct, 21:49


HADISAI GAME DA MATSAYIN AIKIN UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI GA MUMMUNA (HISBAH) DA KUMA KWAƊAITARWA AKAN AIKIN

HADISI NA ASHIRIN DA TARA(29)

Daga Ummu Habiba (R.A) Ta ce: Manzon Allah ﷺ ya ce: “Dukkan maganar da ɗan Adam zai yi nauyin ta na wuyan sa, sai dai idan maganar ta zamo yin Umurni da kyakkyawa, ko yin hani ga Mummuna, ko ambato Allah”.
TIRMIZI

DARUSSAN DA KE CIKIN WANNAN HADISI:

1  –  Duk abin da muke furtawa cikin maganganun mu Allah zai mana hisabi a kansu Alkhairi ko sharri.

2  – Muhimmancin kiyaye harshe tare yin amfani dashi wajan ambaton Allah da umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.

3 – A duk sanda zamu yi magana mu zamo masu faɗar Alkhairi ko muyi shuru.

__


#Ihtisab #hadisai130 #Mugyara

TELEGRAM:
https://t.me/naseehafoundation

WHATSAPP;
https://whatsapp.com/channel/0029VaArvyV0rGiDM3nbrW1e

#Naseehafoundation mu taru mu gyara domin mu gudu tare mu tsira tare.

NASEEHA FOUNDATION

08 Oct, 19:47


RIYAADUL MUHTASIBIIN//33

INKARI A KAN SANYA ZINARI GA MAZA


Daga Ibn Abbas (RA) ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ga zobe na zinari a hannun wani mutum sai ya cire shi ya jefar da shi, sai ya ce: (( Ɗayan ku zai ɗauki rushi na wuta ya sanya a hannun shi?)) sai mutanen da ke wajen suka ce wa mutumin bayan Manzon Allah ﷺ ya tafi: Ka ɗauki zoben ka, ka amfana da shi, sai mutumin ya ce: wallahi ba zan ɗauke shi ba har abada, alhali Manzon Allah ﷺ ya jefar da shi [Muslim]

FA'IDA


1- Halaccin mai iko ya canza munkari da hannu shi, kamar shugaba, ko wanda ke wakiltar sa, ko magidanci a kan matar sa da ƴaƴan sa, ko makamancin haka.

2- Daga cikin salon da Annabi ﷺ ya ke amfani da shi wajen inkarin munkari akwai tsoratarwa mai tsanani a kan makomar mai aikata munkari, wanda ya kamata ga mai umurni da kyakkyawa da hani da mummuna yayi amfani da hakan a innda ya dace.

3- Kausasawa wajen canza munkari ya danganta da irin yanayin munkarin da halin wanda ya aikata munkarin.

4- Ya kamata wanda a ka yi wa inkari ya karɓi gaskiya, ka da jiji da kai ya kama shi ko da an kausasa masa wajen inkarin.

#Riyadulmuhtasibin
#Naseehafoundation

TELEGRAM:
https://t.me/naseehafoundation

WHATSAPP;
https://whatsapp.com/channel/0029VaArvyV0rGiDM3nbrW1e

INSTAGRAM:
https://instagram.com/naseehafoundation?utm_medium=

NASEEHA FOUNDATION

30 Sep, 16:28


HADISAI GAME DA MATSAYIN AIKIN UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI GA MUMMUNA (HISBAH) DA KUMA KWAƊAITARWA AKAN AIKIN

HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS(28
)

Daga Abdullahi Ɗan Mas’ud (R.A) cewa yaji Annabi (S.A.W) yana cewa: “Lallai nan gaba zaku samu nasara a kan abokan gabar ku – Kafirai – kuma zaku ci ribar yaƙi – Ma’ana zaku samu ganima mai yawa, kuma za’a buɗe muku hanyoyin yaɗa Musulunci gari gari, duk wanda yakai wannan lokacin a cikin ku, to yaji tsoron Allah, kuma yayi Umurni da kyawawan ɗabi’u, kuma yayi hani daga Munanan ayyuka”.
TIRMIZI

DARUSSAN DA KE CIKIN WANNAN HADISI:

1 – Albishir daga Annabi (S.A.W) ga Sahabban sa da abinda zai faru dasu na nasara a bayan sa.
2 – Muhimmancin sanya tsoron Allah a rayuwar Musulmi duk inda ya tsinci kansa.
3 – Tunatarwar Annabi (S.A.W) ga Sahabban sa da yin riƙo da aikin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna a cikin rayuwar su.
_____

#Ihtisab #hadisai130 #Mugyara

TELEGRAM:
https://t.me/naseehafoundation

WHATSAPP;
https://whatsapp.com/channel/0029VaArvyV0rGiDM3nbrW1e

#Naseehafoundation mu taru mu gyara domin mu gudu tare mu tsira tare.

NASEEHA FOUNDATION

25 Sep, 13:20


RIYAADUL MUHTASIBIIN//32

INKARI A KAN BAYYANA AL'AURA DA UMURNI DA SUTURCE TA

Daga Miswar Bin Makhramata (RA) ya ce: Na ɗauko wani dutse mai nauyi, ina ɗaure da gyauto mara nauyi, sai gyauto ya kwance alhali ina ɗauke da dutsen, ban iya ajiye shi ba, har sai da na kai shi mazaunin shi, sai Manzon Allah ﷺ ya ce: ((Koma ka ɗauka tufafin ka ( Ma'ana ya ɗaura) kar da ku rinƙa tafiya tsirara)) [ Muslim]

FA'IDA

1- Yin inkari da umurni a kan abin da ya shafi ladubba da kyawawan ɗabi'u na daga cikin abin da mai umurni da kyakkyawa da hani da mummuna ya kamata ya ba muhimmanci.

2- Yana daga cikin hikima mai umurni da kyakkyawa da hani da mummuna ya bayyanawa wanda yake wa gyara cewa abin da ya aikata laifi ne, shi ya aikata ko wani ne ya aikata, a yanzu ko a nan gaba.

3. Haƙurin mai umurni da kyakkyawa da hani da mummuna ga wanda yake yi wa gyara da kuma kula da halin da yake ciki, Manzon Allah ﷺ ya jinkirta wa Miswar (RA) inkarin har sai da ya ajiye dutsen, sannan ya mai gyaran kuskuren da yayi.

#Riyadulmuhtasibin
#Naseehafoundation

TELEGRAM:
https://t.me/naseehafoundation

WHATSAPP;
https://whatsapp.com/channel/0029VaArvyV0rGiDM3nbrW1e

INSTAGRAM:
https://instagram.com/naseehafoundation?utm_medium=